Page 52- Medical Report

110 23 0
                                    

Page 52

Tun da muka tafi muke dariyar wadannan mutane muna maimaita hirarsu. Musamman ma ni da abin da ya faru daga farko. Don da a ce ina da saurin fushi da tun korar farko ba za mu zauna ba za mu tafi. Amma da yake na san makamar aikina, dole mu hadu da fin wannan ma ya sanya dole na hakura, ga shi nan kuwa na ga ribar hakurin.

Cike da farincikin samun abin da muke so muka isa gida. Haidar irin supportive husband din nan ne shi ya sa nake jin dadin aikina. Idan ma bai taimaka min da gangar jikinsa ba to zai taimaka min da shawarwari ko kuma kwarin guiwa. Tun da muka fara case din nan na Hannatu ban taba yin wani abu ba tare da shawararsa ba. Shi ya sa da wani irin nishadi nake yin komai, don ma wani irin zazzabi da yake kwantar da ni a cikin kwanakin nan.

Abin da ya faru kenan yau ma, tun da sassafe na tashi na fara shiri don yau ne zama kotu, sai dai zazzafan zazzabin da ya rufe ni ya sanya hankalina tashi. Na dauki paracetamol na sha amma duk da haka dai jikin babu dadi. Ga shi ba na so Haidar ya gane jikin nawa ya yi tsanani don ma kar ya ce in hakura da zuwa kotun Fa'iz ya yi madadina tunda da ma mataimakina ne.
Dolena na dauki rigar juriya na saka gudun kar ya gane. Amma duk da haka, rashin kuzarina ya sanya shi dole fahimtar ba ni da lafiya.
Ya dube ni hade da kama hannuna ya ce,
"Na lura da zazzabin nan yana neman cin karfinki Buttercup. Gaskiya ana gama zaman kotun nan yau dole ne mu je asibiti a duba lafiyarki, kar a je malaria ce ta tsotse miki jini ba tare da an ankare ba. Ko kuma typhoid da ke lalata kayan ciki."

Na ji dadi tunda dai bai hana zuwa kotun ba. Na dube shi hade da sakin murmushi na ce,
"In shaa Allah."
Shi ma ya yi min murmushin da ke kashe min jiki, sannan ya rungume ni ya ce,
"Ina ji a jikina za mu yi nasara Baby girl. Idan ma sanya su aka yi, idan kuma su suka sanya kansu don kawai jin dadi, da yardar Allah a yau din nan komai zai bayyana. Sai asirinsu ya fallasa a gaban kowa, kuma a daukar musu tsattsauran mataki kamar yadda suka tsaurara wa baiwar Allah ba ta ji ba ba ta gani ba."
Ya sake ni amma bai daina wasa da lips dina ba, sannan ya ce,
"Idan har ana samun lauyoyi ire-irenku Baby girl, sosai za a samu saukin yawaitar fyade a cikin kasar nan. Shi ya sa ake son wanda suka taba shiga irin wannan halin su karanci fannin nan, saboda za su shiga abun ne cike da takaicin shigar martabarsu da aka yi, sai su yi aiki ka'in-da-na'in, su zama masu goyon bayan victims din saboda ciwon su ma sun taba shiga cikin irin wannan halin."

Na kai sumba a saman lebensa, da murmushi na ce,
"Wannan gaskiya ne Baby boy. Da yardar Allah za a wayi gari wata rana an dakushe duk wani yawaitar fyade a Nigeria. Matsalar kawai lauyoyi ire-iren su Barrista Rafiq, masu goya wa Rapist baya kurum saboda kudi; kudin da za su zo su kare a watan-wata rana, amma ciwon raba mace da mutuncinta ba zai taba barin zuciyarta ba duk yadda ta so kuwa. Mutane irin Barrista Ragiq suna amfani ne da baiwar kwarewa, su dakusar da mai gaskiya, su tabbatar wa duniya su din kwararru ne, ba tare da an san mugaye ne ba. Idan har irinsu za su rinjayi irina, to kuwa ba na jin akwai ranar da za a daina fyade a kasar nan."

Ganin lokaci yana neman yi ya sanya na shiga cikin jikinsa, na ce,
"Mu je mu karya mu wuce ko? Time is going."
Ya daga min kai, sannan muka wuce dining muka karya. Tuni ya kai su Ummu makaranta da ma, don haka muna gama karyawa, kayana kawai na dauka da handbag muka wuce.

"Kin san tun ranar da kika fara shari'a da na zo kallo, ban kara ganin kina wata shari'ar ba. Na san yanzu kin gama gogewa."

Ya fadi hannuna na cikin nashi duk da tukin da yake yi.
"Wurin aikinku za mu fara nufa ko kuwa can kotun?"
Ya tambaye ni bayan ya kalle ni.
"Ina ganin mu dai fara zuwa wurin aikin don in tabbatar da mun hada kowacce takarda. Amma dai bari in kira Fa'iz mu ji ko yana can."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now