Page 32- Nusaiba

142 22 1
                                    

Page 32

Sosai Umma ta yi min nasihar da sai da ta shige ni sosai, lokaci guda na ji na gamsu da dole sai hakan ta faru da rayuwata, zan kuma rungumi komai a yadda ya zo min.

Washegari na koma Office. Ko da na je ban ko tinkari office din Oga Ahmad ba. Kai tsaye office dinmu na je, sai dai ina zama ba da jimawa ba aka aiko kira na in ji Oga Ahmad din. Ji na yi kamar kar in je sai dai babu damar hakan. Na dan shafi fuskata sannan na fada wa Aysha zan je in dawo ta kula min da kayana kar iska ya dauke takardun da nake cikin dubawa.

Ina zuwa Office din nashi na yi knocking sannan na shiga. Shi kadai ne zaune a gaban computer yana tabawa, fuskar nan tashi tamkar bai taba dariya ba, idanuwansa dauke da bakin gilashin da ya mamaye dukkan zagayen idonsa.

K'amewa na yi a gabansa, ban ko motsa ba sai da ya ba ni izini sannan na sara masa, hade da gaishe shi na zauna kan daya daga cikin kujerun da suke gaban teburinsa.

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya dauke dubansa daga computer din ya kalle ni, muna hada ido ya sakar min sassanyan murmushin nan nashi mai tafiya da dukkan kuzarina.

"I have no right da zan hana ki sara min tunda dokar aikinmu ce hakan. Yaya kike? Ya Umma da kannena?"
Na sunkuyar da kaina ina amsa masa da lafiya lau.
"Ma shaa Allah. Ina fatan dai ba ki yi kuka ba. Jiya na kira ki kafin in kwanta amma wayarki a kashe. Kin hana ni jin muryarkin nan da ke sanyaya zuciyar dan marayan Allah."

Dariya na yi a hankali jin yana kiran kansa da maraya, garjejen kato da shi.
"Ba da gangan na kashe wayar ba Sir, ba mu da wuta ne sai tsakiyar dare aka kawo mana."
Ya dan langabe kai hade da fadin
"To ya zan yi, na dai yi managing yin bacci amma mara dadi tunda ban ji muryarki ba."

Shiru na yi ina son fada masa zan tafi kar a fara zarginmu ma, sai ji na yi ya ce
"Dalilin da ya sanya ni kiran ki, shi ne; an sanya date din da za a ba ki award ne a kan aikin nan da kika yi na Kanya Village. Award din ma daga can sama aka turo shi bayan na rubuta application din ina son a ba ki saboda namijin kokarin da kika yi, duk da assignment dinki ne na farko. So, you should start the preparation, in the next three days za a yi taron karrama ki a nan, in shaa Allah."

Wani irin dadi ne ya kume ni, ni har ma na manta da zancen bayar da award din da ya yi min tun kafin in tafi hutu.

"You can go. And please kar ki sake yin wani kukan, idanuwanki sun nuna kin sha kuka sosai. Everything is going to be alright. Nusaiba za ta zo gidanku an jima idan an tashi daga aiki."

Dagowa na yi da niyyar tambayar sa shi kuma fa? Ba ya ce zai je su yi magana da Umma ba?
Karaf idanuwansa suka shiga cikin nawa, sai kawai na ji ba ni ma ba kuzarin yi masa wata tambaya. Da kyar na taka na fice daga office din, ina tunanin dalilin da zai sanya Nusaiba zuwa gidanmu duk da Maminsu na kokarin yi mana iyaka da Haidar din.

Ko da na koma ban wani aikata abun kirki ba, zuciyata sai sake-sake kawai take yi min har zuwa lokacin tashi sai ga kiran Haidar. Ko da na dauka cewa kawai ya yi in fito mu tafi. Ba musu na hada komai nawa na yi wa Aysha sallama na same shi can waje motarsa kunne yana jira na.
Da na shiga motar ko kala ba ta hada mu ba har muka hau kan babban titi. Cikin sanyin muryarsa ya ce
"Bai kamata in boye miki komai ba Buttercup, Mami ta dauka da zafi, ta ce ba da yawunta ba zan aure ki..."
Da wani irin karfi na dago fuskata na kalle shi, shi ma din ni yake kallo duk da tukin da yake yi.
"Amma muna kan kokarinmu ne, Salima za ta zo garin gobe, sannan babbar Yayarmu Anti Jamila ma ta ce za ta zo goben. In shaa Allahu za a yi ta ta kare, don dukkansu sun goyi bayan aurena da ke. Ita Nusaiba don ki tabbatar babu komai a ranta ne ma ya sanya ta cewa za ta zo wurinki yau."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now