Page 12- Samu da Rashi

147 22 0
                                    

Page 12

Washegari haka na tashin sukuku babu kuzari. Ita Umma ta yi tsammanin ko ba ni da lafiya ne har da ballo min paracetamol ta yi wai in sha. A ganin ta kamata ya yi in tashi da kuzarin wannan kyakkyawan labari na jiya. Eh tabbas na tashi da nishadi, amma ba nishadi irin wanda take tunani ba, wani nishadi ne da gare ni ne kadai yake nishadi ba gare ta ba. Rashin sanin madafa ne ya sanya ni rashin kuzarin.

Da yamma bayan Anti Maryam ta tashi daga wurin aiki sai ga ta ta zo. Na dai yi kokarin gayyato karfin hali na shimfida annuri a saman fuskata ko don kada ta ga tamkar na yi biris da nata kokarin ne. Sun sha hira ita da Umma kafin ta karbi takarduna cikin envelope muka yi bankwana ta tafi.

Bayan tafiyarta na fuskanci Umma, har ga Allah ban san ta ina ma zan fara ba, sai dai kuma barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa. Dole ne in har ina son cikar burina in yi mata maganar tun ma kafin lokaci ya kure min.
Gani ta yi ina ta murza 'yan yatsuna irin yadda nake yi a duk sadda nake da bukatar wani abu tun ba yanzu ba, tun muna da kananan shekaru.
Ta ajiye barar magin da take yi ta fuskance ni tare da mayar da dukkan hankalinta gare ni ta ce
"UmmulKhairi yaya aka yi? Akwai damuwa ne?"
Na jinjina kaina ina jin rashin kwarin guiwa na dabaibaye ni.
"Ki fadi ko ma mene ne, ni mahaifiyarki ce, idan har ba ki fada min damuwarki ba waye za ki fada wa? Sannan ni mai ba ki maganin dukkan damuwarki ce matukar bai fi karfina ba."

Kalamanta sun dan sanyaya zuciyata, sai dai har ga Allah ta ba ni tausayi don da alama ba ta san kalar maganar da zan yi mata ba shi ya sa har ta iya lallaba ni.
"Umma da ma...da ma..."
Na kasa fadin komai kirjina na bugawa da wani irin karfi.

Ta kama hannuwana ta soka a cikin nata, ta hau kokarin hada idanuwa da ni amma na ki yarda don ma kar in kasa maganata.
A hankali na ji bugun zuciyata yana daidaita, wani irin courage yana zuwar min, sannan cikin sanyin murya na ce
"Umma, na samu aiki."

Cikin rashin fahimta ta dinga bi na da kallo, ganin ba ta fahimci komai din ba ya sanya ni ci gaba da cewa
"Na samu aikin jami'ar tsaro kamar yadda nake so. Jiya suka tura min ta email wai nan da wata daya za mu fara training. Aikin DSS ne."

Shiru ta yi kawai tana watsa min wani irin kallo, irin kallon ba ki da hankali.

"Umma zan iya hakura da admission din can na Cairo, tunda na samu abin da nake ta son in samu, kamar ba sai na je..."

"Ke da Allah can rufe min baki shashashar yarinya! Ni na zaci kin fara hankali Khairi ashe tunanin banza na yi? Idan ma mafarki kike yi tun wuri ki farka, don ni dai ba zan taba barinki ki tafi ki yi aikin jami'ar tsaro ba. To ina ruwan biri da gada? Mene ne hadin danga da garafuni? Ke da kike mace ai aikin jami'ar tsaro ba naki ba ne, aikin maza ne, mazan ma masu iya katabus ba kowanne kashi tusa ba. Ban amince ba, ba kuma zam taba amince miki ba. In dai har da yawuna za ki tafi to ba za ki je ba. Kar kuma in sake jin wannan maganar daga yanzu!"

Na san za a rina tabbas, don shawo kan Umma ba abu ba ne mai sauki. Har gara ma da a ce ban samu wani admission ba watakila za ta amince. Amma a yanzu dai da kusan komai ya kammala, na sani sai an kai ruwa rana kafin ta amince min.

A wannan dare ko baccin kirki ban samu na yi ba. Da safe na tashi na fara aiki kamar yadda na saba, bayan na kammala komai na sake tinkarar Umma da maganar sai dai ina farawa dole na yi shiru saboda ban ma ga fuskar da zan ci gaba ba. Daga nan kuma sai na hau tunanin ta inda zan bullo mata ta amince, don gaskiya ina ji a jikina alkhairina yana tare da zama jami'ar tsaro.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now