Page 55- Confess 1

108 22 3
                                    

Page 55

Sai da Barrista Rafiq ya dube ni, sannan ya saki gajeren murmushi, ya mayar da duban nashi ga mara lafiyar. Ya ce
"Me za ki iya cewa game da zarginsa da ake yi kan haike wa yarinya 'yar shekara goma sha twakwas?"
Sai kuwa mata ta fashe da kuka, a cikin kukan ta ce,
"Hakika na ji babu dadi, ta yadda har sai da ciwona ya tashi, jin zargin da ake yi wa yaron kirki Saminu. Yaron da ko kallon mata ba ya yi, budurwa ma ba ya da ita. Ko da na ce ya samu ya yi aure cewa ya yi ya ba ni ragamar zabar masa matar. To kuwa ta yaya zan yarda da wannan batu?"
Ta karasa maganar da kuka sosai.
Ganin haka ne ya sa alkali ya ba da izinin a fita da ita.

Barrista Rafiq ya juyo ga alkali, ya ce,
"Ya mai girma mai shari'a, ina fatan wannan kotu mai adalci ta gamsu da cewa Saminu ma ba ya gari tun kafin afkuwar wancan mummunan al'amarin da ake zarginsu da aikatawa. Sannan ya mai shari'a, izinin kotu nake nema domin gabatar da shaidata ta biyu."
Alkali ya daga masa kai alaman go ahead.

"Hajiya Zainab Abdulkadir, idan kina kusa please come forward."
Kamar daga sama matar ta shigo cikin kotun, dukkanin idanuwa suka juyo gare ta. Alhaji Abdulkadir, mahaifin Hannatu, mikewa ya yi tsaye, cike da al'ajabi yake nuna ta da yatsa, da alama ya yi mamakin ganin ta, tunda ba ta taba zuwa kotun ba tun da aka fara shari'ar sai yau. Kuma ga sunanta a bakin lauyan da ke kare wadanda ake zargi da haike wa 'yarsa, diyar mijinta kenan.

A cikin witness box ta tsaya, aka sanya ta yi rantsuwa a kan fadar gaskiya, kafin Barrista Rafiq ya fara mata tambaya.
"Ina so ki fada mana alakarki da yaran nan guda uku ; Ahmadu, Ila, da kuma Ibro da ake zargi suna daga cikin wadanda suka haike wa Hannatu Abdulkadir."

Duban ta na yi da kyau, tabbas ita ce; don har yanzu ba ta canza ba, sai dai kyau da cikar zati da ta kara, ga alaman hutu da ya zauna mata. Idanuwan nan nata masu cike da rashin mutunci suna nan ba su canja ba. Tabbas Malama Zainab ce, wannan malamar da ta tsane mu sadda muna Secondary, wadda ta bar aiki ta dalilin dukan kawo wukar da ta yi min.
Na sake murtsuka idanuwana, ita din dai ce, ta yi kiba sosai, don a da 'yar siririya ce, amma yanzu ta zama wata lukuta, sai gajarta kamar inuwar kashi.

Cikin kwanciyar hankali ta fara magana.
"Yaran mijina ne, wadanda ya yarda da su har yake tura su wurin iyalinsa."
"Mece ce alakarki da Hannatu Abdulkadir?"
"Diyata ce, ko in ce diyar mijina ce. Amma dai diya nake yi da ita gaskiya, don ban taba daukar ta a matsayin diyar miji ba."
"Yaya kika tsinci zancen fyaden da aka yi mata? Sannan game da wadanda ake zargi, me za ki iya cewa?"
"Na ji zafi, na ji ciwo, na yi kuka sosai, don ji na yi tamkar diyar cikina ce tsautsayin ya afkawa. Sannan game da su Ahmadu, gaskiya ban taba gasgata su ba ne, saboda yaran kirki ne, tun da suke tare da mijina, ban taba ji ya yi min korafi a kansu ba. Babban abin da ya kawo ni cikin kotun nan shi ne, so nake in wanke su a kan zargin da ake na cewa su suka haike wa Hannatu, a ranar ashirin ga watan tara na wannan shekarar. Tabbas da a ce wata ranar ce ba wannan Litinin din ba, da zan iya yarda. Amma idan har na yi shiru aka ci gaba da zarginsu, na zama azzaluma. Domin kuwa ba su nan ma, shi Ahmadu tare muka tafi Kano ranar, saboda ya roke ni yana son zuwa Kwari duba Yayansa; kuma tuni ya jima yana rokona duk ranar da zan je in tafi da shi don yana son ganin Yayan nashi da ke da shago a kantin Kwarin Kano. Shi kuma Ibro, ganin haka ya sanya shi cewa mu tafi da shi mu sauke shi garinsu can Rimi. Sai Ila ne ma bai bi mu ba, shi kuma na bar shi tsaron shagona da ke kofar gida, wanda har muka je muka dawo yana nan bai tafi ba. To kuwa ta ina za a ce su suka haike wa Hannatu alhali ba sa nan ma?"
Ta karasa maganar cikin rauni.

Gyada kai kawai na yi. Ta yaya mace da girma da shekarunta za ta zauna ta dinga shirga karya irin wannan, kuma wai diyar mijinta ce ake kokarin kwatar wa hakkinta?
A take na tsinci wata murya daga kasan zuciyata ta ce 'Malama Zainab fa ce, wannan muguwar matar marar imani. Ai komai ma za ta iya yi.'
Sai kuma zuciyata ya fara darsa min wani mummunan zargi. Da ma ni da Barrista Fa'iz mun ce akwai wanda ya tsaya musu, ta yiwu wanda ya tsaya musu din nan Malama Zainab ce, ta yiwu ma ita ce ta sanya su yin aika-aikar. Kodayake kisa aka sanya su yi, sai suka canja su kuma suka fara da fyade.

DARE DUBUحيث تعيش القصص. اكتشف الآن