9

177 21 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Chapter 9

Bayan ficewar malam ilu da muƙarraban sa ƴan kallo ɗago Anna nayi daga ɗuƙen da take muka shiga ɗaki da ita maman manu da muke gida ɗaya da ita tashigo har ɗaki ta zauna ta kalli Anna da har lokacin takasa koda ƙwaƙƙwaran motsi sai ajiyar zuciya da take saukewa dama muddin kaga Anna a irin wannan yanayin to lalle ranta yakai ƙololuwar ɓaci dan haka cikin sanyin murya maman manu ta buɗe baki tace"maman Aisha dan girman Allah kiyi hakuri da abunda malam ilu yazo yayi miki karkisaka abun arai ballema yazo ya dameki ya hanaki sukuni a ranki.

Sai kuma taɗanyi shiru ɗan muskutawa nayi nace"amma maman manu tsakani da Allah yanzu duk zaman da mukeyi da mutane a nan anguwar amma arasa wanda ze dakatar da irin cin mutunci da wannan mutumin yakewa Anna magana ashe duk taron yuyuyu taron kuɗaji marasa amfani muke zaune dasu bamu sani?wannan yanuna koda cutar damu za ayi a unguwar nan ba wanda zaiyi magana wallahi maman manu da zaran nasami albashin wannan watan wallahi ɗaukar uwata zanyi mubar nan unguwar da ba wajen zama bane ba.

"Haba ƴar nan katseta nayi raina a mugun ɓace nace"kinga maman manu tashi kawai ki fitar mana a ɗaki dan dukkan ku halinku ɗaya banga wani abun kizo kina mana karamar murya bayan kowa ya watse ba,ai wannan duka gulmace kiji mai zamuce kisami na barbaɗamu.

"Yi hakuri maman manu rabu da Aisha ai kinsan sha'anin yaro ba kowani ɗan halak ne zaiga ana wulakanta masa iyaye yayi shiru ba cewar Anna da har lokacin bata kalli inda maman manun ke zaune ba tayi maganan.

Washe baki maman manu tashiga yi tagyara zama tana cewa wallahi maman aisha ai wannan maƙwabciyartamu mai ɗan wake ita ke kai gulma wajen malam ilu dake shikuma ba hankaline da shi ba shikuma yazo yana ta tada jijiyoyon wuya kawai dan baku biya da kuɗin wannan wata ba,rainane yasake ɓaci jin wai mai ɗanwake ce ta haɗa wannan tarzomar yasani cewa ai wallahi sai namata rashin mutunci.

Saurin dakatar dani maman manu tayi tace"haba keko aisha daga ganin ɗan fawa sai miya tayi zaƙi haba de ai basai kinje ba kinama zaune zata ciyota ta zo tasame ku nan zaune.

Daga haba ba wanda yasake yin magana haka ta karashe zaman ta harta tashi tatafi ƙofarta mude bataji ta bankin mu ba kamqn yanda Anna tajamur burki nima shirun nayi.
Saboda ɓacin randa nake ciki wallahi sai na nemi ƴunwar dakuma gajiyar da na ƙwaso duka narasa.

Dadare muna zaune ina sake kwantarwa da anna hankali sai ga fadila kaman anjehota ta faɗo mana ɗaki tana ta huci ko sallama babu tashiga cewa yanzu dama wannan mara mutunci mutum haka yazo yamiki anna wallahi sai yasan yataɓoki hukumace zata rabamu da shi wallahi.

Murmushi mai ciwo anna tayi tace"yo mai natada jijiyoyin wuya ai idan mukace zamu rama abunda yamana mun zama ɗaya kenan barin shi da Allah kawai zamuyi shine ze bimana hakkin mu dan Allah ba azzalumin bawa bane saide bawa ya zalumci kansa,Allah yana gani tunda nazo nagarin nan bantaɓa yi da kowa ba,to mai zetada mun da hankali dan ɗan kwaya irin malwm ilu yamun tijara kawai de naji ba dadine gani yanda yan anguwa suka zama ƴan kallo akarasa wanda zece da ilu abunda yayi ba daidai bane ba.

Amma duk da haka nagode Allah haihuwa tamun rana tunda yanta tazo ta tsayamun haka yarba gidan cike da kunya harda su masu kallon.

Daga haka taɗauko wata hiran nan muka shigayi sai can fadila takalli ni tace"nikan yau tunda garin Allah ya waye nake ta zaune ina jiran dawowarki naji ya rananki ta farko ta kasance duk da nasan keɗin kwararriyace inde ta fanin ɗinkine banida haufin ko matar shugaban ƙasa zaki iyama dinki amma kuma kedin matsoraciyace lamba ɗaya masamman ma wajen da ba idon sani.

Dariya nayi nace bawanda yasanni sama dake da anna na nashiga faɗamusu yanda na tsorata kafin wani saurayi ya fahinci halin da nake ciki yabani kwarin gwiwa dariya sosai fadila tamun anna kan cewa tayi Allah yakyauta yarabaki da wannan tsoro naki,sai karfe taran dare fadila tamana sallama rakota mukai nida khadija nan take sanar dani ai takusan samun aiki a masana'antar sarrafa magunguna na al hakk natayata murna dakuma yi mata addu'ar samun nasara tunda tace gobe zataje dan ayi musu gwaji.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now