99

221 14 1
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨

    ✨ *G.W.F* ✨

_________________________
GORGEOUS WRITTER'S FORUM WE ARE THE BEST AMONG THE REST.
_________________________

CHAPTER 99

Taro da Ahmad be samu zuwa ba sai khalid ne daya zo ya wakilce shi,Asibiti suka nufa da Alhaji da jikin nashi yasake Mami sai kuka take tana kiran karya mutu yabarta,haka Ahmad da mai gadi suka cicciɓe shi suka sakashi mota,Mami ma tashiga Ahmad ya zasu zuwa Asibiti da gudu nurses suka xo da gadon daukan mara lafiya suka dauke shi suka shiga ciki dashi Likitoci a ƙalla sunkai mutum uku suka rufa musu baya dayake a Emergancy word suke Ahmad sai kai komo yake yakasa tsayuwa gu ɗaya balle ya zauna gani yake kaman shine silan  faɗuwar ta shi ya dauki lefin da nashi ba ya aza shi a kansa itako Mami ba abunda take sai aikin kuka da sammabatu takeyi.

Suna nan a haka kowa da abunda yake  masa kai komo cikin ransa suna nan a haka Sajid da  da Anty Sajida takira shi a waya faɗa mishi abunda ke faruwa da mahaifin nashi afujajan hankali a tashe yafaɗo kaman wanda aka jeho zaune ya tadda  Mami tana rusgan kuka"Mami wai me yasami Daddy ne lafiya lau fa mukayi sallama dashi da safe nafita?yafada kaman zeyi kuka hankali a tashe yake tambayar ta,ita ko Mami ba baki sai ma karama kukan nata ƙaimi da tayi,dafashi Ahmad yayi ganin ya tashi hankalin sa sosai yashiga ce masa"cool down mana Sajid be a man karkayi mamaki da hukuncin Ubangiji mana duk abunda Allah yayima bawansa daidai ne,Allah yana jarrabtar bayinsa ta hanyoyi da dama dan auna imanin su ko numfashi da muke shaƙa da ixinin sa muke shaƙa idan yace wanda muka shaƙan ba zamu fesar ba ko duka duniyar nan gatan mune ba wanda ya isa yasamu fesarwa ba tare da yardan sa ba, ko duka Likitocin duniyar nan suka taru a kanmu ba wanda ya isa jada hukunci Ubangiji hukuncin sa shine daidai dan haka cuta ba mutuwa bace,sau dayawa sai kaga mai lafiya ya mutu majintaci wanda ake kawowa mutuwa kuma yarayu,kaine wanda ya kamata ka ƙarfafawa Mahaifiyarka gwiwa ba wai kakaraya ba,Alhaji addu'armu yake bukata a daidai wannan gaɓan ba koke ko kuka zamuyi masa ba.

Ya gamsuwa da maganan na Ahmad kai yashiga gyaɗa kansa yana cewa"astagfirullah wa'atubu alaika,nagode da tunatarwar ka gareni hakika kayi gaskiya ruɗewa ce tasani harnaso mance Allah shikeyin yanda yaso da bawansa ba wayo ko dabara mun bace ba, amma kasan  komai yana da sanadi menene yajawo faɗuwar tasa lokaci ɗaya?ware hannuwan sa Ahmad  yayi sai kuma ya buɗe baki a hankali yashiga faɗa masa yanda Alhajin yaxo yasame shi dakuma faɗuwartasa ya daura da cewa"saide ka tambayi Mami ko tasan abunda yatashi hankalin sa  amma ni wannan ne kawai abunda nasani,ajiyar zuciya mai karfi Sajid ya sauke yana mai dukar da kansa ƙasa yace"zan bincika a hankali Allah de yabashi lafiya"amin Ahmad din ya amsa masa dashi.

Haka suka zauna suka cigaba da zaman jiran fitowar Likitan dasuke ɗakin,rashin lafiyar Alhaji be hana Fauza yin budurin birthday dinta ba,sun garƙame manya manyan sifiku sai kiɗa ke tashi kaman zasu tada gidan sama,bata damu da rashin lafiyan Mahaifin nata ba ko kaɗan dan haka ba wanda tafaɗa mawa halin da Mahaifin nata keci ko a cikin ƙawayen nata,duk da basuga Alhaji da Mami ko awajen yanka cake ba,sun barwa kansu ko basa garin ne.

Haka akai ta ɗaukan hotuna da ƙawaye ana daurawa a tiktok wasuma live suke dauka haka IG da FB gaba daya hotunan yana yawo yazama shine topic na wannan ranan a media kaman yanda take bukata kenan,sai can d maraice suka tashi a taron inda ta tattara kyaututtuka da tasamu takai daki tana fadawa saman gadon ta mai taushi daya sha shimfidar bedshit mai kyau ta kwanta dan ta huta.

********

Ɓangaren Aisha wannan abun yazame mata sabon abu,duba da yanda tanuna rashin damuwa da halin rashin lafiya da Mahaifinta yake ciki bata damu da sanin ba,dukda akan idon ta aka sakashi Mota aka tafi kaishi Asibiti amma hakan besa jikin ta yin sanyi kona sakon guda ba,wace iriyar rayuwa wannan,da zaka haifi ɗan ɗan ka amma be damu lafiyan ka ba,ga rashin kulawa gareka kai Mahaifi ko Mahaifiya, ya ilahir rahimina wannan wane irin rayuwa ne.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now