96

215 11 1
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTERS FORUM* ✨

     ✨  *G.W.F*✨
_________________________
Gorgeous writters forum we are the best among the rest.
_________,,_______________

CHAPTER 96

Bakinta na rawa kar kar kar yanda laɓɓanta ke rawa kawai zaka kalla kasan cewa tana cikin halin ruɗewa"Annata tana raye kuma kasan inda take zaka sadani da ita da gaske?

Jinjina mata kansa yashiga yi dan tabbar mata da abunda yake faɗi,riƙe masa ƙafanta tayi tashiga rasgar kuka tana mai cewa"dan Allah ka sadani da ita ko kafaɗamun inda take ni zani da kaina dan....katseta yayi yana cewa"kwantar da hankalin ki zaki cigaba da rayuwa tare da ita idan kinaso,saurin amsa masa tayi da"eh inaso dan Allah tana ina faɗamun inda take.

Kwantar da hankali yarinyar zaki ganta ne matukar zakiyi abunda nace kuma bazaki tsaɓa abunda nace miki ba.

"Zaka sameni dayi maka biyayya akan abunda kace matukar zaka sadani da Annata saide zanyi maka koma meyene matukar be tsaɓama Allah da ma'aikinsa ba,idan ko yatsaɓa faɗin Allah Alhaji saide kadauki hakuri dan bazan aikata saɓo ba"koda zaki rasa Mahaifiyarki datayi sanadin zuwanki duniya takuma sha wahala daku duk da ƙazafin da akemu ku  keda ƙannenki?ya tambaya yana mai tsareta da idanun sa mai kaman na mujiya.

Jinjina masa kai tayi cikin nauyin baki data zuciya tace"ƙwarai kuwa ciki harda rasa tawa rayuwar nasan Allah yana tare damu kuma be manta damu ba,ta amsa masa cike da kwarin gwiwa jifanta yayi da wani shu'umin murmushi sannan yace"kwarin gwiwarki ya birgeni saide kafin ki yankewa kanki hukunci kan rashin amincewa da bukatata kalli wannan videon.

Ipad dayake hannun sa ya shiga shawafa sai yamiƙa mata,da fari ƙin amsa tayi saida yamata alama data karɓa sannan ta karɓa hannun ta yana rawa tashiga kallo ai bata iya kaiwa karshe ba,ta zube saman gwiwarta ta haɗe hannunta gu ɗaya alaman roƙo idonta na tsiyayar da kwallah tashiga bashi hakuri.

"Alhaji dan girman Allah kayi hakuri zanyi duk abunda kace amma dan Allah kace su barmun Annata wallahi zanyi yanda kace rayuwarta tafimun komai a duniya zan iya sadaukar da tawa rayuwar dan ita ta rayu cikin salama,da wani irin dariya yafashe mai ban haushi sai kuma yashiga cewa"zaki rayu cikin farin  farin ciki da salama da yardar mu zakiyi albarka.

Duk da zuciyarta a cunƙushe take dan ganin abun da yanuna mata tana kuma jin zafin halin da taga Mahaifiyarta ciki duk da bata ganin fuskan Matar sosai amma taji a zuciyarta zata iyayin komai dan ta ceto rayuwar ta"saide da yardar Allah de bada taku ba"eh komade me zakice kizama cikin shiri nan da kwana biyu zan nemeki dan jin inda mukatsaya a maganan tamu,ganin yana batun fita daga falon yasata tayi saurin katseshi tace"dan Allah kamun wata alfarma mana?''alfarma ta mecece?ya tambayeta yana tsareta da idonsa masu tsoratata ƙasa tayi da kanta tana maijin tsoron yanda ze ɗauki bukatata cikin sanyin murya tana maisake yin ƙasa da kanta tace"ko zaka bani Annata naji muryarta koda sau ɗayane"ba yanzu ba harsai kin cika sharuɗan mun kafin na sadaki da ita yana kare faɗa mata haka yayi ficewar sa daga falon yana mai jin daɗi a ransa ganin nasara tana tunkaro shi.

Yana barin falon Aisha ta fashe dawani irin kuka mai ban tausayi na kewar Annan ta abunso da kaunanta,idan ta tuna halin da ta ganta yanzu ta cikin wayan saita sake fashewa da sabon kuka"me kikayi musu? suwaye sukayi miki haka?waye wannan da rannan yakira sunanki muka gudu da yayi sanadin rabuwarmu?ya rusa mana ɗan farin ciki da muke da ita,waye waye?ya Allah Ya rahman Ya rahim ya quddus Ya salam kabamu salama acikin rayuwar mu ka kawo mana ɗauki ka agaza mana idan wani lefin iyayena suka maka ya Allah kake hukuntasu da wannan yarabbi ina rokonka ka yafeme su kakawo mana dauki ka agaza mana ja karemu daga sharrin masu yinta,sharrin mutune ko na aljanu ko ta dabbobi,haka ta kasance ta dauki lokaci mai tsawo tana addu'a tana zubda hawaye.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now