89

191 17 2
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨

     ✨ *G.W.F* ✨

CHAPTER 89

Watsi yashiga yi da pillows ɗin cikin fitan hayyaci a zabure yamike ya nufi toilet dayake jin ƙaran ruwa yana fatan ace ita dince saide yana tura ƙofan yaga wayam bakowa wajen sai famfo da aka bari a kunne,zuciyar sa yabashi ƙila taga shigowan ka nan dinne ta boye.

Cike da gwarin gwiwa yashiga dubata cikin part ɗin nasu saide ba tanan dama kuma ba wasu ɗakuna bane masu yawa ɗaki ɗayane sai kitchen da store sai toilet ɗaya dake cikin falon,buguzum buguzum haka yafita daga falon cikin fitan hayyaci harya manta da matsayin shi yakuma manta ta yanayin da yake cikin a hakan nashi yanufi bakin get wajen maigadi yama mance da dare ne ba rana bane,yashiga kwalawa masa kiran"Mati Mati da gudu Malam Mato maigadi ya rugo da ƙatuwar Sandar goransa riƙe a hannu yana muzurai jiki na ɓari ganin halin da Uban Gidan nasa yake.

"Bade ɓarayi bane wallahi banga shigan su ba saide idan ta baya suka ɗirƙa ta katanga.duk yaruɗe dan har cikin ransa ya ɗauka ɓarayine suka birkita Alhajin haka.

"Dalla rufawa mutane baki ina masu Gidan nan suke?tsaɓan ya fita a hayyacin sa yama mance da shine maigidan.

"Ƴallaɓai kaine ai Maigidan yabashi amsa.

Zazzago masa idanun sa yayi kaman zasu fito su faɗi ƙasa launinsu ya canza zuwa launin shuɗin idan ba karya idanuna suka gane mun ba kaman hayaƙi nagani yake fitowa ta bakin sa.

Tsoro iya tsoro Malam Mati yashiga dan haka cikin gudu gudu yayi cikin gidan direct part ɗin Sajid yanufa yana xuwa be tsaya sanyin jiki ba,yashiga buga musu ƙofa dakiran Sajid fito yau gida ba lafiya Alhaji yamance kansa,a gigice Sajid suka fito shida Sajida jin abunda Malam Mati yake cewa kuma saiya sake ruɗasu ai kuwa a tare suka isa inda yake a ɗuƙe tsaɓanin ɗazu dayake tsaye,dan yanayin da yatsinci kansa ciki yaba buƙatar yamike iyalan nasa sugan shi,a haka.

Kusan a tare suka isa inda yaken harda Mami da itama ta tashi zatayi fitsari taji bugun ƙofa da Malam Mati yakema Sajid tafito dan tagani shine idonta yasauka kan Alhajin dake ɗuke ƙasa kaman mai naƙuda tayi kansa da mugun sauri tana cewa"yau me zan gani haka Alhaji lafiya?

"Wallahi Hajia dan ma bakiga yanda yazo mun bane yana tambaya wai ina maiGidan?"maigidan kuma Malam Mati kode gamo Alhaji yayine?Mami ta tambaya kaman zatayi kuka"wani irin gamo kuma Mami cewar Sajid fuskan sa da damuwa.
"Yanzu de kamamun shi mushiga ciki ko hayaƙine amasa.

"Haba Mami yazamu shiga da mara lafiya ciki mu ajiye gwara de mutafi dashi Asibiti,suna cikin magana saiga Ahmad shima yafito daga part ɗin su yana isowa yafara tambayan su lafiya?wallahi cewa Malam Mati yashiga labarta masa yanda sukai da Alhajin da yanda yazo yasame shi harma da karin gishiri saida yayi nan Ahmad da Sajid suka kamashi suka saka a mota sai Asibiti.

KANO

CID Office Faisal ne xaune a gaban Ogan sa cikin Office ɗin sa yana duba file din dake gabansa ya dauki a kalla minti goma kafin ya ɗago  yana kallon sa dakiran sunan sa"Faisal yanzu ina kuka tsaya da binceken naku?na karanta report din idan na fahince ka ba Alhaji Badamasi yayi wannan kissan ba,sannan kuma mun kame wasu Mutum biyu da kume kyautata zaton suna da saka hannun wajen aikata muggan lefuka kuma sune manya manyan diloli suna saida miyagun ƙwayoyi suna kuma safaran su daga ƙasar nan zuwa wasu ƙasashen da sunanan magani suna amfani da maxuban maganin capsule dakuma tambari.

"Very good Faisal na yaba da ƙoƙarin ka wallahi bakaji yanda nakeji ba gami da wannan case ɗin tunda aka kawo wannan case din hannun na wallahi banji abunda ya faran ta mun rai kaman wannan ba,saide inaso kamun wani abu"ta mefa Sir?Faisal ya tambaya yana gyara zaman sa.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now