54

155 15 1
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 54

  "Ai dama tunda naga wancan fitsararriyar ƙanwa taki taxo nasan dawata a kasa ashe keke sashin yimun rashin kunya,to wallahi bazan lamunta ba"wai Alhaji fisabilillahi ace mutum da ɗansa baze iya zama kona minti ɗayane ya fuskanci matsalansa ba kai kullum da kun haɗu kaman musa da fir'auna ai ba haka akeyi ba.

"Saiki faɗamun yanda akeyi yafaɗa a fusace kaman zekai mata bugu"Allah yabaka hakuri ya huci zuciyarka bana nufin ɓata maka nafaɗi hakan ba kuma Ahmad dakake magana kansa tun safe daya fita anan bansake sakashi a idanuna ba,sai yanzu daya kira yake cewa tafiyar ujulace ta kamashi jin faɗanka yasa shi kashe wayan sa.

"Karya yake yana nan ɓuyewa kawai yayi daga gareni ungo anshi wayan ki kiramun shi dan nasan inkece kikayi kiransa yanzun nan ze ɗaga niko danake maƙiyinsa bagashi yayi blocking wayana ba.

Ba yanda ta iya haka tasaka hannu ta karɓi wayan tashiga kiran sa saide kaman abun tsafi duka layinsa a kashe,ajiyar zuciya ta sauke tana maida waya ta ajiye bakin gado sannan tawuce tafita falo ta barshi a tsaye a ɗakin ƙerere kaman dogari,saida yayi tsayuwar kusan minti uku bayan barinta ɗakin sannan ya fito cike da fushi dan shi kadai yasan abunda yashirya ma Ahmad ɗin yana zuwa falo ya isketa zaune tana kallin tv labarun cikin gida kwafa yayi harya gifta ze wuce sai kuma yaja ya tsaya jin wani kanun labarin da yadauki hankulansu daga shi har Ammi.

Miƙewa tsaye Ammi tayi tana nuna tvn da yatsa"Alhaji mai nake gani haka?

Shima tsura mata ido yayi tana girgiza mata kansa kaman bashine yanzu ya gama tijare ta ba,kana nufin cemun bakasan abunda yake faruwa a company ba kenan?

Nan ma ɗaga mata kansa yayi dan shi kansa yashiga cikin matsanancin ruɗani"ana zargin cibiyar magunguna ta AL HAKK da fitar da gurɓatattun magunguna ba bisa ka'ida ba,dan haka hukumar nafdac ta ƙasa ta bada umurnin rufe wajen harsa tagama bincikenta.

Gumine yashiga karyo masa shide yasan basa sarrafa ko wani irin magani ba bisa ƙa'ida ba to meke shirin faruwa dashi?tambaya dayama kansa kenan kira yafara samu daga ƴan uwa da abokan arziki wasu jajanta masa sukeyi wasuko gulmace kawai yasasu kiransa haka ita kanta Ammi duk wanda yagani a labarai sai yakirata ita damuwarta ɗaya Ahmad ina yashiga gashi wayansa a kashe baya shiga,Anty hajiace takira itama jajen tawa yayar tata tayi sannan tadaura da cewa zatama faisal magana insha Allah daya shigo zata turashi can gidan naku yagana da Alhajin dan sanmu matsaya guda kafin sunan company sa yaɓaci godiya Ammi tayi ta zauna ta rabka tagumi,shi kansa Alhaji badamasi yama rasa mai zeyi dan kwata kwata jiyake ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cak.

Alhaji sunusi yakira yana ɗauka yace"wai mai nake gani yanzu a labarai ne?
"Kaman yanda kake gani nima yanzu haka abunda nagani kenan narasa wake shirin ɓatamun suna company wallahi,na raini company na tun yana jariri harzuwa girmansa ban taɓa samun tangarɗa ba,nasha wahala kafin nakai wannan matsayi amma rana tsaka wasu da bansa kosu waye ba suke neman ɓatamun suna bani da maƙiyi kowani dana taɓa sa'insa dashi,ya kare maganan sa cike da rauni ƙwantar masa da hankali Alh sunusi yafara dan yasan koma waye yayi musu wannan abun to tabbas yasan sirrin abunda akeyi a wajen to amma waye shine de besani ba amma zeci gaba da baza yaransa dan su binciko masa gasu goga yanzu basama a ƙasa ko wace uwa duniya suka tafi oho tunda sanda yamusu rashin mutunci akan ɓacewar Ishak  suka samu saɓani suka watse sukabar masa daban sa.

Haka yayi ta magana aransa amma a zahiri cewa yayi"ko zamu haɗu anjima da dare kaman yanda muka saba haɗuwane dan zuwa wajen shugaba ya taimaka mana koda wani abun.

Juyawa yayi yakai dubansa ga Ammi da take zaune shiru be ɗauke idonsa daga kanta ba yace"gaskiya sunusi bazan iya zuwa ba dan iyalina tafara zargina gami da fitan dare da nake.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now