98

294 18 4
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITER'S FORUM* ✨

  ✨ *G.W.F* ✨

_________________________
GORGEOUS WRITTER'S FORUM WE ARE THE BEST AMONG THE REST.
_____,,,,,,,,_______,,,,,,,,______

CHAPTER 98

Komawa ciki yayi a inda yafito ya barta anan ya sameta kwance saman tayis ta ƙudundune ta haɗe kai da gwiwa sai riskar kuka take,yaji ba daɗi saboda marinta da yayi amma idan ya tuna da furucin ta sai yaji haushin ta.

Da kyar ya bude bakin sa cike da jin haushin ta yace"wallahi idan baki dena wannan kukan naki ba yanzun nan sai kisa naje wajensa na datse masa harshen da ya furta wannan ƙazamin furuci gareki,cike tsoro tawaro manyan idon ta ma sha Allah suna ta tsiyayar da ruwan ƙwallah ta kalle sa dasu,tana mai rufe bakin ta da hannun ta tana ɗaura ɗaya hannun saman ɗayan ta shiga girgiza masa kanta,dan ba taji wasa a muryar sa ko a idon sa data kalla ba.

Wayan sane yashiga tsuwa da neman agaji kaman baze ɗauka ba,sai kuma ya ɗaga yana cewa"ina jinka da muryar sa dake cike da fushi.

"Luck Broo kabita a hankali ba lalle ta yarda da kai kai tsaye daga yi mata bayani ba,kai ko irin  kalam soyayyar nan da ƴar tarairaya baka iya ba,ka kasa saye jaririyar zuciya irin ta Aisha zuciyar da ba abunda tasani sai abunda ka koya mata abune mai sauki,zuciyar da ba tarayu da wanin ka ba mallakan sa,amma kai sai muzurai..."ka gama?

Ahmad ɗin yakatse shi da tambayan sa hakan  cike da ƙosawa da surutun na Faisal,murmushi Faisal yasaki daga ɗaya ɓangaren har Ahmad din na iya jiyo sautin sa yace"ban gama ba,karka manta tarko muka ɗanawa waƴan nan mutanen kuma duk wani motsinka yana kan idanun su,duk wani shige da fice naka da zaran wani abun yafaru kaine mutum na farko da zasu fara zargi dan haka ka iya takunka,mun samu labarin gobe manyan kayayyakin da sukai order ze isa Lagos kuma sun zuba manyan kuɗaɗe cikin wannan harƙallah idan muka kame waƴan nan kayan gaskiya mun durƙushe su duka.

Kamai da hankalin ka ka kula sosai karkayi gigin barin Aisha ita kaɗai dan wayan nan mutanen ba imanine dasu ba zasuyi komai dan ganin sun kare kansu kar asirin yatonu idan zaka fita,karinƙa fita da ita,sannan mustapha yace gobe za'ayi bikin birth day na ɗiyar Alhaji Na Allah wannan dama ce a gare mu,kaga zamu bigi tsuntsu biyu da duwatse ɗaya ku ku kame mana nan mu dasu Mansur mu kame can kafin mu samu zama mu tattauna yanda zamu gama da ƙunyarta tasu baki ɗaya.

" hmmm ajiyar zuciya Ahmad ɗin ya sauke kaɗan ya juya yana kallon Aisha datayi shiru amma hawaye basu dena zubo mata daga idanun ta ba,yace naji amma saide na haɗaka da ita dan ni bazan iya tsayawa ina wani lallashin ta ba.

Dariya sosai Faisal ɗin yashiga yi masa yana cewa kaide kasani magulmaci ya kashe wayan,duk maganan da sukeyi tana sauraron su dan a hands free wayan take,yana kashe wayan yamiƙe yashiga ɗaki ya barta nan zaune a falo,wani tunani ne ya faɗo mata maganan Anty Hajara na ranan inda take cewa idan kinaso kijawo hankalin mijinki da farko kina bukatar nitsuwa ki kasan me yakeso dakuma me bayaso,sannan wace iriyar shigace take daukan hankalin sa shigar ƙananun kaya ko shigar dogayen riguna kode shigarmu ta hausawa danginsu atamfa leshi da shadda kode yafison ya ganki da kayan bacci koda inners a sa'inda Anty hajara take mata wannan maganan har kunya take bata sai yanzu abun yafaɗo mata arai tace bari ta gwada ta gani ko zata iya miƙewa tayi tsaye ta shiga toilet din da yake cikin falo a ranta tana cewa"yau zanyi maganin girman kanka,bani kake kira da yarinya ba yau zakaga yanda ƙaramar yarinya zata wujijjigaka sai kazo kabani hakuri da bakin.

Wanka ta tsala dayake akwai komai na bukata aciki ta wanke gashin kanta sosai da shampoo tafito kanta yana ɗingan ruwa ɗaure take da towel iya gwiwa tanufi ɗaki daidai sanda shi kuma yabude kofan ɗakin ze fito bakin ƙofa sukaci karo da juna ƙirjinta masu tudu suka bige masa ƙirji sa da wani irin slow motion ta ɗago kanta gashin kanta masu tsawo da tsantsi suka shafi gefen fuskan sa take hancinsa suka shaƙo masa kamshin sabulun da tayi wanka dashi dana shampon da tayi amfani wajen wanke gashi dashi ai besan sanda ya lumshe idanun sa ba take wani abu mai kama da mashi yasoki zuciyan sa.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now