76

184 17 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 76

   Gudu yake shararawa shide fatan sa ya'isa dawuri kafin wannan hoda data shaƙa yasake ta,sai daf da sallan isha'i suka isa  suna shiga garin ya sauke ajiyar zuciya direct wani katafaren gida yanufa yanayin horn mai gadi leƙo yana ganin sa yabude masa yashiga da motan sa yayi parkin kai tsaye bakin tap din dake tsakiyan wasu furanni yanufa alwala yayi yafita zuwa masallaci sai da yayi sallah sannan yazo.

Har sannan bata farka ba,saida ya geshi ya bude ƙofan wani falo sannan yazo bakin motan yabuɗe bayan mota ya dauko ta kaman wanda yadauki ƴar tsana  ya shiga da ita hadaɗedden falon da bakajin komai sai sai sanyi ac da wani dadɗan kamshi daya cika falon kwantar ta saman kugera 3sitter harya miƙe tsaye ze tafi yaji ta riƙe masa hannun komawa yayi yazuba  idanun saman kyakkyawan fuskarta kallon ta yake ko kiftawa babu beta sanin yarinyar haka take da sassanyar kyau ba sai yau ya shagala da kallon ta jin zuciyan sa na motsawa yasashi saurin kai ɗaya hannun sa ya zare daya hannun sa cikin nata ya mike yashiga toilet dan  watsa ruwa.

Alhaji sunusi yashiga mummunan tashin hankali ko yanzun duka sun halarta a guest house dinda suka saba haɗuwa duka sun halarta idan kacire Alh badamasi .

Alhaji surajo ne yamiƙe rai a ɓace yake magana inda yake cewa"sunusi nasan kafi kowa sannin manene ƙa'idan ƙungiyar mu kasan wace irin tafiya muke amma koda yaushe anfi samun matsala ta ɓangaren ka"amma ranka yadaɗe oga kasan ba lefina bane ko?nima badason raina hakan ke faruwa ba.

"Dallah rufa mana baki Alh bashir yace rai a ɓace ya daura da cewan kuma kasan ɓatan Ishaq yana daga cikin mummunan kaddara mu barin sa  wajen mu kasan barin sa yana rayuwar ƴanci babban barazana ce garemu dama dukiyar mu baki ɗaya"kuma saida akace dakai mukaishi matsafa ko dawanau mubarshj can arinka masa alluran mahaukata amma kaƙi tunda kace bakason yanzu a kashe shi,alh shehu ne yake wannan maganan.

Miƙewa Alh sunusi yayi tsaye yana cewa"ina ganin dr da muka bawa contrack ɗin alluran nan yaci amanar mu,ni sai yanzu ma nake tunawa da sharadin shugaba yazama mun dole in nemo Ishaq ko wani dake da alaƙa dashi.

"Ya batun saka hannun da alh badamasi ze wa wannan takardun kasan fa idan basaka hannunsa muka samu da farko ba komai namu baze tafi daidai ba"kaman de yanda ishaq yayi maka tsawon lokaci da muka dauka muna ƙillace dashi sai daga baya muka gane takardun duka kaddarorin sa dukka sunan matar sa dakuma babbar ƴarsace har yanzu munkasa sani ina suke aina suke rayuwa kai ko kamanin ita yarinya ba wanda yasani cikin mu balle musaka anemo mana ita.

"Sannan ita ma matar damuke ta murnan munsameta sakacin ka da rashin kulawanka yasa munrasata rana tsaka,kuma duk da hakan baka tunanin komai kai auren  ƴarka kasa gaba,tom bari kaji yanzu haka alh badamasi an aiko masa da sammaci daga babban kotu"kotu ya ambata a kiɗime"eh kotu yasake amsa masa kuma baka da labarin wannan ɗin ko?

Saida ya sharce gumi daya tsastsafo masa a goshi ya haɗiye wani ƴawu mai kauri tukun ya gyaɗa ma ogan nasu kai.

Wata uwar harara Alh surajo yamasa yace"dama tun farko saida mukace baza muyi wannan tafiya da kai ba kanace kace zaka iya gashi baje ko ina ba asirin mu naneman tonuwa.

Yakare maganan yana huci cike da bacin rai idan yatuna cikin ƴan watanni sunyi asaran million of naira sai yaji mugu mugun haushin sa gashi duk abunda ƙungiya ta ginɗiya masa ba wanda yacika cikin sharuɗan ta.

"wai kai surajo me matsalan ka danin ne alh sunusi yace yana miƙewa rai a ɓace dama tun shigowata ƙungiyar nan nasan basona kake ba,take faɗa ya kaure tsakanin su kaman zasu bawa hammata iska saida shugaban su ya tsawatar sannan suka nutsu suka zazzauna bayan ya umurcesu da haka.

Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya sannan yace" hukumar NAPTIP tasakomu gaba kan wannan harƙalla tamu duk da ba wanda yasan  mune muke aikata abubuwa da suke zargi amma ina jiye mana tsoron faɗi wannan karon dukda tunda muke bamu taɓa faɗiwar ba,kuma bazamu yarda mufaɗin ba gaban maƙiya suma dariya.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now