50

156 16 0
                                    

💕 *AURE WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 50

    Jan hannunta laila tayi itako sai wani turjewa take cike da jarumtar da tanemo ta yafawa kanta amma ƙasan ranta fal tsorone dakuma fargaba dan cikin ta hautsina mata yake kaman zata saki zawo sabida tsorata da tayi da kalman wannan Alhajin na rashin imani.

Suna kaiwa bayan wasu motoci tasaki wani irin mahaukacin ajiyar zuciya tana dafe da setin ƙirjinta dake mata wani irin lugude sai numfashin wahala da take saukewa, akai akai saida ta seta nutsuwarta sannan ta ɗago da dubanta ga laila tace"kinceceni wallahi dakyar nasha.

Dariya laila ta fashe dashi saida tayi harda riƙe cikita tana mai nuna fuskar Aisha tace"kalli fuskarki gaki da tsoro amma bakin ki baya mutuwa nide abunda kawai zance dake ki kula ba ko ina zakina sake baki kina magana ba,irinsu Alh sunusi basu da imani wallahi zasu iya iyin komai saboda farin cikin su data iyalansu.

Ahmad dan sussunar da kansa yayi cike da ladabi yace"dan Allah daddy kai hakuri akwai yarinta tattare da ita be dace kaida kake babba kabiye mata ba,dan biyematan da kaine yabata daman sakin maganganu haka batare da ta tauna abunda zata faɗi ko kula da kaiɗin babba bane ba,daddy kasan sha'anin ƙuruciya"kai dallah rufama mutane baki anfaɗa maka ƙuruciya haukace toh nabi ƙuruciya dagudu ba wando nace nabi ƙuruciya dagudu ba wando tuntuni yariya tana ta zuba iya shegenta bakai magana ba sai yanzu zaka wani kashe murya kaman karuwa taso damfara kana wanu cewa sha'anin kuruciya.

To wallahi muddin bata farantawa shalelena rai ba kuwa itama bazata taɓa samun kwanciyar hankali ba,kwanciyar hankalin ta ɗayane kawai takawo kayan sannan tazo ta bani hakuri yanzun nan,ya kare magana yana huci kaman wani zaki.

"eh wallahi daddy sai takawo kayan nan kuma ta gogemun takalmi da hijabin ta sannan ta duƙa har kasa tabani hakuri basmace ke wannan magana shiko daddyn nata sai wani washe baki yake kaman gonan auduga,karshe Ahmad tafiya yayi ya barsu tsaye a wajen dan kansa har sara masa yake dan kwata kwata ya tsani tashin hankali da hayaniya arayuwar sa,ko meetin sukeyi da ma'aikata ko abokan kasuwancin sa yawanci khalid ke wakiltansa shike gudanar da komai.

Taku yasoma yi dan barin wajen cike da izza da ƙasaita kai kace jinin sarautane shiɗin"kai Ahmad Ahmad ina zaka baka kirata tazo ba,da karfi Alh sunusi yake kiran sunan sa yana masa magana dan ganin kaman yanufi parkin lot,bema nuna yaji shi yayi tafiyarsa yana isa wajen yabude motarsa ze shiga sai ya hangota duƙe dafe da kirjinta fasa bude motan yayi yanufi inda suke yana zuwa be tsaya yimata magana ba kawai ya damƙi hannunta yanufi bakin motarsa yabude yatura ta ciki da karfi sannan shima ya zagaya yashiga mazaunin driver key yama motan sannan ya figeta da wani irin karfi ya bar wajen wani irin tsorone yasake kama Aisha ji take kaman ta saki futsari awando tawani waro ido cikin in ina tasoma cewa"da Al lah kamun rai karage  gudun nan dani wannan gudun wallahi banshirya mutuwa ba,akwai buruka da yawa da nakeson cikawa kafin mutuwa ta.

Banza yamata saima kara gudun motar daya sake duk inda motar su ta gilma sai mutane sun bisa da kallo masu abun hawa kan saide sune suke kauce masa hanya.

Ganin hakan da Aisha tayi sai yasake tsoratata dan Aisha duk jarumtarta da rashin bari takwanan ta amma akwi tsoro dan ko adaidaita ta hau idan taga driver na gudu sai tayi masa magana tayi yanda yaraje gudun dan ita anata ɗan ƙaramin tunanin duk wani hatsari dake faruwa gani take gangancin driver ke jawowa da suna kula da yin tuƙi cikin nutsuwa da hakan bazata yawaita faruwa.

HAJ MARIYA
tunda jiya dasukayi maganan nan da ƙawarta Haj balkisu hankalinta ba akwance yake ba,dan haka yau koda Alh sunusi yafita daga gidan ita ma shiryawa tayi ta nufi gidan kawartata dan tun daga bakin ƙofan shiga falon take ta ƙwaɗa sallama mai aikin gidan ne ta amsa mata tana mai bata hanya ta wuce a wulakance take kallon matar"hajiya fa?Tayi tambaya kaman wacce akace dole sai tawa matar magana.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now