86

242 22 3
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTERS FORUM* ✨

          ✨ *G.W.F* ✨

CHAPTER 86

  Shiru tamasa ta basar dashi fuskanta yana nuna kaman bataji daɗin zuwan nasa ba amma cikin zuciyar ji take kaman taje ta rungumesa dan murna.

Tunda Alhaji mai gidan nan ɗazu da yazo yabita da wani kallo da shu'umin murmushi ta rasa nutsuwarta idan ta tuna yace idan bezo yau ba ze iya kaiwa gobe ko jibi sai taji jinin jikinta yana tsinƙewa gashi dare na karayi.

"Kode ba'ayi farin ciki da zuwan nawa bane na koma inda nafito?saurin ɗagowa tayi tana kallon sa da jin tambaya daya mata kaman tace masa a'a karka tafi ka barni ta riƙe hannun sa tasakar masa kuka ko zeji tausayin ta yafasa tafiya amma saboda jan aji irin ta ɗiya mace mai kamun kai da sanin darajan kanta ta dauke kanta tayi daga barin kallon nasa tana sake tsuke fuska kaman bata ji mai yake cewa ba.

Takowa yayi yashigo cikin takun sa dake nuni shiɗin jarumin namiji ne ya iso gareta bata ankara ba saijin ƙamshin turaren sa daya cika mata hanci tayi kusa gareta ɗagowan da zatayi saura ƙiris yarage ƙirjin su ya haɗu dana juna,ja baya tasoyi cikin zafin nama ya damƙo ƙugunta da duka hannun sa biyu yana dawo da ita kusa dashi yana haɗe ƙirjinsu waje ɗaya.

A fusge ta furta"a'auzu billahi"karki sake mun uziyya yafaɗa cikin yin ƙasa da murya yana ɗalle mata baki da yatsa"auchh ta furta cikin rawar murya idonta na cikowa da hawaye.

"Shiiii yace da ita yana daura yatsan sa saman bakin sa banson kukan gulma idan kukan kike sha'awa yanzu saina sakiyi mai dalili.

"Hajiya nifa ban yarda da yaron nan ba cewar Alhaji bayan fitan Ahmad daga falon"wane yaro kuma Alhaji?Mami ta tamvaya tana gyara zaman ta.

"Ahmad mana bayan shi akwai wani yaron ne"me yasa kace haka?ko yayi ma wani abunne?"beyi ba saide ina tunanin yana shirin yi idan ko hasashena yazama gaskiya wallahi kinde ji narantsa miki zan ajiye duk wata sanayya dake tsakanina da Uban sa in masa rashin mutunci ne.

Ni yaron nan yake neman yaudara  yakomawa aikin sa amma yake yin abu kaman wanda bamusan abunda yakeyi ba,ai duk wani motsin sa akan idon mu yake ko yaɗauka shi kaɗaine wanda ya iya taku,yakare maganan sa yana ta kumfar baki.

"Nifa Alhaji bangane akan me kake wannan kumfar bakin ba ko zakamun dalla dalla ta yanda zan gane ka ganar dani,ta kare fadin hakan cike da zakuwa dan son jin meya fusata shi har haka.

Ruwa mai sanyi ta daukata mika masa ya amsa yasha cikin glass cup sannan ya dire cup din saman center table dake gaban su ya shiga sauke ta gwayen ajiyar zuci yajin jina bayan sa da kushun dayake zaune akai yace wato Hajia ina tunanin yaron nan Ahmad yakoma aikin sa na yaƙi da fasa ƙauri idan ko bincike na ya cimmasa saide Uwar sa ta haifi wani wannan karon bazan bari ya tarwatsa ni kaman yanda yayi galaba akan mu shekarun baya.

"Amma Alhaji kasan Fauza tanason sa kana ganin zaka iya hafa rayuwar ƴarka cikin halin ƙunci kawai dan wani dalili naka ko burina ka?

Da dariya ya fashe kaman ta bosawa saida ya tsagaita da dariyan sannan ya kalli Mami yana cewa"kuɗi maganin wulakanci kuɗi maida tsohu yaro kuɗi masu gidan rana kuɗi mai maida yaro babba idan basu rayuwa sai tagayyara"saboda kuɗi kenan zaka iya rusa farin cikin ƴarka?ta katse shi da tambaya"eh mana to mai aciki shima yabata amsa kansa tsaye.

Ya daura dacewa ko kinsan yanzu haka mahaifin sa yana hannu ana zarginsa da kissa bayan fyaɗe"na shiga uku tafaɗa tana dafe da kirginta yanzu abunda yake faruwa kenan amma baka faɗamun ba tuntuni,takare maganarta tana ta salallami.

Shiko Alhaji na Allah yasamu abunda yake so dan haka ya cigaba daurata yana cewa"hatta da lasisin sa an sauke dan naji kaman anacewa yana amfani da ilimin sa yana safarar hodan iblis"na shiga uku cocaine fa kenan?me yasa badamasi zeyi haka dan Allah"sabida kuɗi mana ya amsa mata a ba abunda mutum ba zeyi ba saboda yasa kuɗi dan shine burin kowani mahaluƙi yatara yabarwa ƴaƴa da jikoki.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now