36

143 18 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Chapter 36

Kafin tasauke hannun ta nima nakai mata maruka dama da hauni ba ita ba hatta Ahmad abun yaba shi mamaki dan betaɓa tsamanin zata iya rama wannan marin ba duba da yanayin tazaran shekaru dake tsakaninta dasu dakuma wayewa uwa uba ƴaƴan manya.

Zafin marin be gama sakin salaha ba ta tsinkayo muryata nama basma magana cikin ladabi kaman ba itace tayi wannan abun ba yanzu"anty basma kifayi hakuri kinsan ni bana barin bashi komai ƙankantar sa,bare kuma ga taɓamun lafiyata tunda nake ko uwar da ta haifeni ma bata taɓa saka hannun ta ajikina ba bare kuma wata,ɗan dafe gishinta tayi kaman wacce tayi mantuwa sai kuma ta ɗan kalli salaha tace sorry fa kawar Anty.

Wani irin malolon abune ya takare makoshin ta harma ta kasa cewa uffan.

Juyowa tayi ga Ahmad dayake hakimce saman kugera duk wannan abu kaman baya gun,saboda ya maida hankalin sa kacokan saman systerm ɗin sa,

Azahiri kenan amma a baɗini duk abun nan da ake yana ganin su"gani tace dashi ba tare da tako kalli inda yake ɗin ba,banza yamata kaman ma besan da wata halitta mai suna Aisha a wajen ba.

"Ok basma kuna iya tafiya dan ina da aiyuma masu tarin yawa"kuttt yanzu My saboda wannan kucakar ƙasƙantacciya ƴar wanki shegiya wacce...."ya'isa taji an katseta a tsawace yanda tsawan yashigeta har saida taɗan zabura abunka da wanda yataso ba gwaɓa.

"Ya'isa ya'isa tasake maimaita hakan cike da ɓacin rai dakuma baƙin cikin yanda wasu masu kuɗi basu ɗauki talaka bakin kamai ba,mai zan so ga wannan saurayi naki ƙwala ƙwalan idon ko kuma farin fatan,Allah ya sauwake mun keda kike ga abun burgewa a gun kyayi,amma bar wani haɗani da wannan abun ko kusa.

baya daga cikin gerin miji da nakeso in kina abunki yatsaya tsaka ninku amma kibar sakani cikin tsabgarku,duk talauci da ƙaskancina Alhamdullahi bantaɓa zuwa gidan masu kuɗi danyin bara ba,gumina nakeci kuma ko wanki da kike goranta tamun bafa sata nake ba balle naji kunya sai na wanke miki ɗan kamfe harma da ƙunzugu sabida rashin sanin dajara a hakanma sai na tsaya tsayin kada kafin abani hakkina ko da saura bayan wannan?

Wani irin zabura rahaina tayi cike da borin kunya kunyata kawartasu da wannan yarinyar tayi dakatar da ita nayi da cewa"haba raihana ke kuwa mai naki na zabura haka kode neman suna kike?
Da kin tsaya matsayinki da baki ɓata lokacinki wajen daukar jakar mace ƴar uwarki ba wallahi kuke saka ana raina mu ƴaƴan talakawa saboda ƙwaɗayi da rashin sanin ciwon kai.

Daga haka ta juya da nufin barmusu office ɗin harta kama handle din kofan zata buɗe taji ance"waya baki izinin fita?

Sake handle ɗin tayi a hankali ta juya ta kalle shi shima ita ɗin yake kallo hartayi ƙasa da kanta jin idanunsa masu kaifi a kanta saide tunawa da tayi da abunda yamata ɗazu hakan yasata banka masa harara ta juya da sauri tafita waje tana rufe masu ƙofa da karfi daya ba sautin garammm.

Rintse idonsa yayi shi kaɗai yasan abunda yakeji akanta,amma ƙwarin gwiwarta da rashin tsoron ta yana burgeshi besan sanda murmushi ya suɓuce masa ba.

Ganin murmushi saman fuskansa abunda tunda take dashi take mararin ganin sa dashi amma bata taɓa gani ba sai yanzu,hakan yasake tunzurata ta fashe masa da wani sabon kuka tana cewa"wato abunda wannan ƴar sharan tamana ma be ko dameka ba,sai ma murmushi dakake binta dashi tunda nake dakai bantaɓa ganin ka dashi ba,kullum kazo guna fuska cunƙushe kaman wanda aka faɗawa sakon mutuwa.

Wallahi daddy zankira in faɗa masa beyi yunƙurin hanata kiran ba dan yana ganin alama tanan tafi kauri kai ƙara abu kaɗan daddy be gama tunanin da yakeyi ba ta miƙomasa wayan tana ƙananun kuka.

Karɓan wayan yayi a hannunta ya kara kunne sa,sallama yafara masa madadin amsa masa da sallama da yayi sai tsinkayo muryar Alh sunusi yana masa faɗa da tada jijiyoyin wuya beyi kunkurin katse shi ko bashi hakuri ba,saida yakai aya a maganar tasa sannan cikin ladabi Ahmad din yace"sorry Alhaji ban hanata party ba inma duniya zata gayyata sani yarage nata nine de bazan samu daman halarta ba saboda wani aiki mai mahimmanci danake dashi a wannan lokacin.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now