94

263 18 5
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUR WRITER'S FORUM*
        ✨G.W.F✨

CHAPTER 94

Wani irin sauri Alkali Sada yake kaman ze kife ƙasa saboda tsaɓan ruɗewar da yayi yabi ta wata ƴar ƙofa datake ta cikin kotun ta bayan inda Alkali yake zama tanan yabi zuwa ainihin inda  Ofishin Alkalai suke ajejjere,shiga ɗaya daga cikin ƙofofin da suke jere awajen yayi kasa zama yayi sai kai komo yake yama rasa wani irin tunani zeyi.

Duk ya ruɗe ya ɗimauce take wani irin zufa ya karyo masa,yana cikin wanan halin Barrista Tafida ya shigo yana cewa"haba yallaɓe ya zakayi mana haka kuma?ina ganin nasara ta tunkaroni ina kallon kaina matsayin miloniya tsanina da nasarata be wuce taku biyu zuwa uku ba kasaka ƙafarka kayi fatali da ita why why why yallaɓa why?saboda idon sa yariga da yarufe be kula da halin ko ince yanayin da yasami Alkali Sada ba,shi dan gani yake kaman da gangan Alkalin ya ɗaga karan,ya kare maganan sa kaman zeyi kuka mission impossible sunan wani film,sassauta ɗaurin neck tide dinsa yayi yana daukan ruwan gora daya gani saman table din dake Office ya ɓalla murfi yakafa baki yasoma ƙwanƙwaɗa.

Duk wannan hargowar na Barrista Tafida hakan besaka Alkali Sada yi magantu ba,shima din ruwan yake da bukata dan jika maƙushin sa,saida yasha ruwa mai sanyi sosai ji yayi kaman wani abu dayake tokare a maƙoshin ya wuce,saida yakai zaune sannan yace" ina Tafida yake?"gani ranka yadaɗe ya amsa cike da girmamawa,numfasawa yayi naya cewa"inaga kai baka ga abunda ni nagani bane shisa kazo ka cikani da surutu.

"Me ka gani Ranka yadaɗe?wakilai ne sukazo don saka ido kan wannan shari'a wace hukunci zan yanke"what?Barrista Tafida ya faɗa yana ɗan zare ido"kwarai kuwa dan haka inaga idan katashi daga nan kawoce Gidana kai tsaye kudin nan daka kawo mun su jiya ko sisi ban taɓaba dan haka kadauka ka kamaida musu da abun su kuma kace CIKI DA GASKIYA WUKA BAYA HUDA SHI.

Gaskiyar suce kaɗai abunda ze kwacesu"amma Ranka yadaɗe...ɗaga masa hannu Alkali Sada yayi yana cewa kaga Tafida akan su bazan ɓata,aikina dama sunana baki ɗaya ba,shekara ɗaya da rabi yarage mun barin aiki gwara nabar aiki ana mai darajani ba Allah wadai dani ba,ni tunda nake ban ma taɓayin shari'ar rashin gaskiya da zalla son zuciya irin ta yau ba nasan dawaya cikin ƴan kallo sunyi ta Allah wadai dani saboda rashin adalci kiri kiri dana nanu awajen inaga dalili kenan da aka turo ƴan ganin kai daga ƙungiyar kare hakkin dan Adam wato human right.

"Haba Ranka yadade kai wani abu mana yanzu ina ji ina gani zan rasa million goma harfa da sabuwar mota za bani,haka barrista Tafida yake ta sambatu shide Alkali Sada tunda ya faɗamasa yaje Gida ya dauki kudin yamai dama  masu shi abun su besake yin magana sai addu'a dayake tayi na Allah yadaura shi a saman su kawai yake kai karshema cewa yayi da Barrista Tafida dan Allah ya fita masa daga Office yana bukatar kebewa bayason yawan surutu da yake masa haka barrista Tafida yafita daga Office din jiki a mace dan shi yagama lissafin abunda zeyi da kudin.

******
Da ɗan gudu Ammi ta nufi inda Ahmad yake tsaye bayan mutane ƴan ɗauka rahuto sun fiffito abun be musa daɗi ba can na hango Mom Islam hannunta rike da biro da takarda sai cizon  biron take da alama ba haka taso ba,taso tasamu na rubutawa amma Alkalin kotu ya gudu saboda tsaro ba tsoro ba,ni kaina ba hakan naso ba amma ya na iya da samarin kakata haka de na hakura nafito na raɓa ta can gefen inda Ahmad yake tsaye na rakuɓe na tsaya ina jiran suje gida nima in bisu inje dan sake ganin wata wainar za'a toya kuma a can.

Yaude Ammi ta kauda kunya ta rungumi ɗanta ɗaya tilo ɗa mafi soyuwa a ranta,a bayyanar jama'a  tasaki kuka tana cewa"ka gade ga abunda Mahaifinka ya zaɓarma kansa yafi son yamai daku marayun karfi da yaji ni kuma ya maidani bazawara da girmana,mutum da mutuncin sa yazaɓi yin shiru koda mutuncin sa ze zube shi bedamu da hakan ba,ba ruwan shi da ya makomarmu zata kasance bayan babu shi"Ammi kiyi shiru kidena magana kinga mutane suna kallon mu mu tafi gida idan yaso sai muyi magana,yafaɗa mata hakan ne san ganin hankalin wasu daga cikin masu wucewa ya fara yowa kansu.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now