88

251 27 7
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨
     ✨ *G.W.F* ✨

CHAPTER 88

Duk yarikice yama rasa abunyi janyuta yayi yasakaya jikin sa ya rungumeta da karfi kaman wanda akace za kwace masa ita,a gefe ɗaya kuma ba abunda zuciyar sa keyi masa sai kai komo,idan har abunda yaji suna magana akai ba gaskiya bane wani shirin sune fa?

Tabbas idan wani abu yasami ta baze yafe musa ba haka zalika baze yafema kansa ba.

Da wannan tunanin yasoma jijjigata yana dan marin kumatun ta a hankali da kiran sunan ta amma ina bata motsa ba ,batama da alaman motsi kaman wanda aka mitsina yamiƙe da sauri yana gyara mata kwanciya ya sauka daga saman gadon yasaka jallabi kitchen ya tafi yaɗauko ruwan gora mai sanyi yazo dashi ɗakin saida ya zauna saman gadon ya shiga yayyafa mata saman fuskanta cike da tsoron saida yazuba mata kusan rabin goran saman fuskan ta tukun ta jawata nannauyan ajiyar zuciya ta soma kiran sunan sa dayi masa magiya duk ta firgita tafita hayyacinta riƙota yakeson yi yasata jikin sa ko zeji sanyi cikin zuciyar sa amma ina sai yin bayake taki yarda ya matso koda kusa da ita duk ta kwuƙwikuye abun rufuwar tana bashi hakuri ganin yanda take a firgice yasan ba zata bari ya taimaka mata tasaka kaya ya kaita asibiti a duba masa ita ba.

Waya ya dauka yakira Dr Hajara bayan sun gaisa nan take tsokanan sa tana cewa"lalle kace yau dole nayi sadaka tunda harka tuna damu har kakira waya Allah de yasa lafiya ba wani lefin mukai ba?tafaɗa cike da zolaya matar Abokin sace Abdullatif tare sukai karatu da shi,hmmm kawai yace jin yanayin da ya sauke ajiyar zuciya be iya yace da ita komai ba,yasata tambaye shi da lafiya kuwa A-B dan haka suke kiransa yawanci tunda Basma ta nace masa take kiran sa da hakan,shiko yana amsa matane ganin A mafarin sunan sane B kuma sunan baban sa"lafiya Haraja amma gaskiya ba lau ba Allah de yasa kina cikin Abuja bakiyi tafiya ba?

Jin muryan sa kaɗai ya isa ta fahinci yana cikin damuwa"ina gari yanzu hakama ina Asibiti dan yau night nake amma lafiya naji kace ba lau ba?Nan yace mata wallahi Madam ɗina ce ba lafiya kuma taƙi bari na taimaka mata balle nakawo ta Asibiti shine nace ko zaki taimaka nazo na dauke kizo ki dubamun ita,ya kare maganan kaman zeyi kuka.

"Subuhanallahi garin yaa?saida ta tambaya ne kuma taji kunyar tambayar tata tayi saurin cewa turamun address ɗin inda kake gani nan zuwa yanzu ba sai kai kazo ba ai bazaka bar mara lafiya ita kadai ba.

Tana kashe wayan nata ta fito dauke da wata ƴa karamar box data zuba kayan aiki tace da Abokiyar aikin ta"dan Allah Joy zan ɗan fita duba Matar wani Abokin mijina koda zazo nemana"Ok koda Oganki ne yazo Joy tafaɗa cikin zolaya tana ƴar dariya dan tasan Hajara a kan Mijin ta bata da sauki.

Ƙaramar dariya ita ma tasaki tana cewa"lalle wato kema Joy yanzu kin zama ƴar sa ido kin yarda da sharrin su Latifa ko?"amma bakiji nace komai ba dan nasanki ina buɗe baki abunda zakice kenan Latifa da yanzu ƙarasowa ta kenan tayi maganan tana kaiwa zauna.

"Kunga nide saina dawo dan nasan inna tsaya na biyewa surutun ki ba tafiya zan ba,tafaɗa tana daukan box din tafita,adawo lafiya sukai mata.

Saida takira Mijin nata ta faɗa masa zataje duba Matar Ahmad ɗin kafin ta shiga Motar ta tafita daga Asibitin,inda tabar Abdullatif da mamakin yaushe Ahmad din yayi wani Auren dan yana da Labarin ɗage auren su da akai da Basma.

Address ɗin ta bi tazo kofan gidan ta parka motar ta tafito dama ya faɗama maigadi akwai wacce zatazo ya shigo da ita ta karamin kofa kuma yakiyaye bayaso yayi wani abu da ze bada  wata ƙara da zagane anbude wani yashigo ko yafita"inde wannan ne baka da matsala Ranka yadade daga haka yakoma ciki.

Kai tsaye ɗakin yakoma tana nan kwance inda ya batarta tana kuka jin kukan nata kaman ana watsa masa tafashasshen ruwan zafi a cikin zuciyar sa matsowa yayi gefen ta yanayin ƙasa da kansa cikin tsigan rarrashi yace"Eashow kiyi hakuri ki daure na taimaka miki koda kayane ki saka kafin Likitan da zata dubaki ta ƙaraso.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now