97

262 17 4
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITE'S FORUM* ✨

       ✨ *G.W.F* ✨
______________________
GORGEOUS WRITER'S FORUM WE ARE THE BEST AMONG THE REST.
_______________________

CHAPTER 97

"Meya fusata Ishaq?naga yanayinka ya canza lokaci ɗaya kake kuma  neman daukar fansa a kansu?"hmmm Badamasi tabon da Sunusi yamun yafi naka,Sunusi yamun tabon da bazan taɓa mancewa da shi ba.

Yasa nakoma tamkar jemage cikin tsuntsaye ban iya nafita ko nan da can da rana ba,saide ko da dadare,ya maisheni matacce a idon duniya dama ahalina baki ɗaya,ya rabani da kowa nawa ya rabani da dangina da kowa nawa yasaka iyalina shiga duniya ba tare da wani nawa yasan inda suke rayuwa ba.

Ya mai dani tamkar wani dabba cikin keji harna tsawon shekar takwas kafin nasamu wasu bayin Allah suka kuɓutar dani,Badamasi nasan Sunusi beyi maka koda kwatan abunda yamun ba,daga taimakon sa ya zama Yarona wanda nafi aminta dashi nabashi dukkan yardata yaci amanata ya wulakanta mun rayuwata taya zan manta dashi mutumin daya saka rayuwata cikin garari wani irin hukunci kake tunin idan yashiga hannuna zan masa hmmm yasauke ajiyar zuciya,zuciyar sa tana masa ƙuna tamkar wuta naci a cikin sa,idanun sa sun canza launi a yanda suke sun koma jaajir dasu a take yanayin sa ya canza zuwa na zallah ɓacin rai tamkar wani ɓakin ƙumurci haka yake huci,dukan su dasuke zaune a falon sun tsorata da yanda yanayin sa ya canza lokaci ɗaya ya cigaba da magana cikon wata murya mai amoo yace ba kashe shi zanyi farat ɗaya ba,idan na kashe shi farat ɗaya ko na damƙashi ga hukuma wannan baze saka na huce taƙaicina ba,zanfi so da kauna kafin ya mutun sai nayi wasa kura da rayuwar sa sai ya rasa komai daya tara sai duniya ta juya masa baya sannan ne hankalina ze kwanta bayan nasa ankaishi gidan ɗan kande dan ya girbi abunda ya shuka.

"Ina bayanka zan kuma tsaya dakai harsai wannan burin naka yacika sai munga bayan su,Ahmad ya faɗa shima Faisal miƙewa tsayen yayi yana cewa"ina bayanku harsai munga bayan waƴan nan azzaluman.

"Sai mun ruguza wannan azzalumar ƙungiyar da yarda Allah ina tare daku ɗari bisa ɗari inji Baristar Anwar dake zaune,murmushi Janar ɗan Musa yayi irin tasu ta manya yana mai cewa"nima ɗin baxa'a barni a baya ba ina tare daku harsai munga karshen su,gyaran murya Alhaji badamasi yayi hankulan su suka maida kansa musƙutawa yayi ya gyara zaman sa ya fuskance su yana cewa"kafin ku tunkari waƴan nan mutanen kuna bukatan runduna.

"Ba runduna muke bukata ba"basira da iya taku Ahmad ɗin ya bama Mahaifin nashi amsa"kamar ya fa?Alhaji badama yasake tambayar ɗan nashi dan neman karin bayani.

Gyara tsayuwa Ahmad ɗin yayi ya fuskanci Mahaifin nashi da kyau yace"Plan shiri muke da bukatan yi ba yaƙin fito na fito zamuyi dasu ba,zamu tsara yanda zamu lalata musu komai nasu ba tare da sunsan mu ne ba,koda kuwa zasu san mune sai mungama dasu komai ya ƙare musu sannan zamu bayyana kanmu da kanmu gare su,kafin sannan kai kana bukatan kaje ka huta.

"Wani irin hutu kuma zanyi Ahmad bayan kana ganin abunda yake shirin tunƙarata,karfa ka ɗauka dan anyi zaman kotun farko ka dauka komai ya wuce a wajen su,idan baka manta ba ai yanzu ɗan jarida yagama fada maka shirin su a kaina shin kana tsammanin zasuyi baccine su manta dani bayan burinsu be cika a kaina ba.

Murmushi Faisal yayi yana cewa"eh to nima de haka nagani amma idan munkai ka Asibiti ka kwanta a can zaka huta,zamu aje jami'an tsaro na fararen kaya,waƴan da zasu baka tsaro dakuma saka ido akan duk wasu masu shige da fice,ka kwanta a can ka huta kasha vitamin C,koda sun zo gunka idan abu yasoma kwaɓe musu kanuna haryanzu kana tare da su,ka kuma cigaba da nuna tsoron nan da kake da shi akan abunda ya shafe su.

"Lalle Yarana sun girma sunyi hankali sun kuma san takan tsiyar maganin xomon zamani sai karen zamani Allah yadafa muku yashige muku gaba yamuku jagora"Amin Ammin mu suka amsa baki ɗayan su sannan ta kalli Ishaq tace"inason maka albishir"fuska a sake ya amsa mata da"ina sauraronki Hajia Ma'arufa Abdul-jabbar da mamaki duka suke kallon sa barin ma su Ahmad ya 'akai wannan mutumin yasan complete sunan Ammin sa haka shiko Faisal beyi mamakin jin sunan Ammin abakin sa ba,dan Anty hajia ta taɓa ce masa kakannin su ƴaƴan maxa suke duk da bata faɗaɗa masa ba.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now