END

224 23 4
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨

      ✨ *G.W.F* ✨

_________,,______,,,,_______
GORGEOUS WRITTER'S FORUM WE ARE THE BEST AMONG THE REST.
_____,,,,,,,_______,,,,,,,_______

END OF BOOK 1

"Oga wannan yarinyar ba zata magantu ba sai mun bata jikin ta,ai da sauri na maida kallo na kan mai maganan wato abani jikina a dakeni yake nufi kenan tabdi jam hummm nace batare da na bari sun fahinci tsorona ba.

Bafa zata tayi magana ba,Oga da alama irin yaran nan ne masu shegen tauri kan nan kaman ta kafiran farko"ka dauko mun ita yafaɗa cikin bada umurni dan ita ɗin ƙadara tace,banaso ayi kuskure wajen taɓa mata lafiyan ta,dan wannan da kake gani ƙila itace mabuɗin cikan burina dan haka ɗauko ta kawai a canza mata waje,shi kuwa wannan basamuden dama kaman jiran umurni Ogan nasa yake ya tunkaroni da karfin sa dan takun sa ɗaya sai yabada wani irin ƙara ƙura dayama wajen ƙawanya kuma sai kaga ya tashi,buɗe baki tayi da nufin dakatar da Ogan nasu duk da ba kallon sa take ba kuran da wannan basamude yatayar ya badeta tashiga tari ba ƙaƙƙautawa,Alhaji Bala dayaga halin da take ciki shi ya dakatar da wannan ƙaton daga barin tabata,daidai kuma sanda suka juya ma wajen bayane yace akira masa Ahmad ɗin nan kuwa Ahmad din yayi masu tass,murmushin mugunta kwance saman fuskan sa yashiga cewa"Ahmad Amadu Amadi Madi yakira shi da mabambanta sunaye ya daura da cewa ni gareni wannan yarinya jarice a wajena dan da ita zanyi kasuwanci har in samu riba ninkin ba ninki,sannan inaso kasani ni ba lusarin namiji bane kaman yanda kakira ni dashi lusari yana can ƙwance gadon Asibiti kaman yanda kabani Awa ɗaya nima na kara maka wata Awan idan kanason tsiratar da rayuwar wacce kakira da sunan mata,idan yawuce wannan lokaci karkayi tunanin samun ta,kasaka a ranka karasata ne har ƙashen rayuwarka kaje kanemi wata ga nan ƴan mata burjik daidai ajinka...."shut up yafaɗa a mugun tsawace shima  kansa besan yayi ba tsaban ɓacin rai har jikin sa rawa yakeyi ya cigaba da fadin wallahi wallahi ko ƙwarzanewa tayi sai kunyi nadama balle ta kaika aikata abunda kace din duk da bansan waye kai ba amma ina kyautata zaton zan samoka samoka ba abune mai wuya ba aguna koda karkashin ƙasa kashiga kai da muƙarraban ka saina nemoku nayi ɗaidai da rayuwarku.

"ƙwarin gwiwarka yana burgeni Ahmad badamasi ko Mahaifinka bashida wannan kwarin gwiwan a ina kai kasamo shi?kafin Ahmad din yabashi amsa sako yashiga wayan Alhaji bala sauri kunna data yayi yashiga Whatapp abunda yagani saida yakusan sakin zawo saboda rudewa da yayi"Inna Inna Inna yashiga maimaitawa yanata kiran Inna amma yakasa ƙarasawa cewa Innalillahi dayake dama bakin be saba da ambaton Allah ba.

Shikenan nashiga uku Sunisu yakira sunan da wani irin yanayi ya daura da cewa yau ba zan ma ce Alhajin ba,kasani a uku na banu na lalace duk ya rude ya ɗimauce yama rasa inda ze saka ransa yaji daɗi"wai kai me haka Bala kanada hankali kuwa?kawai kawani rude meyake faruwa da kainene eh?ya tambaya cike da jin haushin abokin nasa.

Wayan da yake rike da ita a hannun sa yamiƙa masa dan shi bashima da bakin magana,zufa kawai yake sharcewa cikin sa sai ƙugi yake yana bada wani irin sautin ƙululuuuu kai kace zawon ze sake.

Me ina tambayan ka sai faman wani miƙomun waya kake,dungura masa wayan yayi dayasa dole ya karɓa shima da yake shima ya zaƙu ya kalli meya zautar masa da aboki haka lokaci ɗaya.

Ai kuwa sai ga Alhaji Sunusi dafe da baki yashiga zarya yana cewa"garin ya hakan tafaru?ya akai sukasan Minal ɗiyar kace?har sukai nasaran suka yaudareta suka ɗuramata miyagun ƙwayoyi haka?ya Allah wai meke shirin faruwa ne damu?

"Da nide Sunusi ai kai haryanzu ba wanda ya taɓaka tun tuni saida nace maka kar kayi kuskuren sawa aɗauko wannan yarinyar kaƙiji dan kai idanun ka yariga da ya kulle ƙwaƙwalwanka ya toshe basirarka ta ɗoɗe baka gani da hangen komai sai biyan bukatun kanka,da cikan burin ka shine kan gaba da komai a rayuwarka,idan kai kana da basirar ɗauko yarinya da cikan burinka shikuma Ahmad da yake yaro mai basira sanin mukaman aikin sa zama zeyi yazuba ido yana kallon mu,ko barin sa Gida yanxu bana tantama cikin dayan biyu yayi hakane dan raba mana hankula,bawi dan yaguji mahaifinsa yayi hakan ba,bawani ɗan halak da za'a taɓa masa iyaye ya zauna ya zuba ido yana kallo ba,kuma wallahi Sunusi kasani matukar sunan ƴata ya ɓaci kaima sai naka sunan ya ɓacin daga haka ya kaɗa masa babban riga ya fizge wayan sa daga hannun sa yayi gaba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 05 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now