30

176 20 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Chapter 30

  Duk yanda Anna taso danne zuciyarta kasawa tayi saboda yanda Aishsn ke wasu irin maganganu kaman mai aljanu,sai kira take innallahi Anna shikenan mama rabi ta mutu anmata kisan gillah Anna kalli nan kigani na shiga uku sun kasheta suna taran jinin cikin wata ƙatuwar ƙwarya lahaula ya ilalil alamina Anna harda fadila cikin wannan aika aikan kalli kukama take saboda munafinci.
  Rufemata bakin Anna tayi dan bazata iya sauraron wannan kayan taƙaicin ba cike da tausayin ƴartata tasoma cewa"ya'isa Aisha kiyi shiru ki nutsu bude idonki ki kalleni nan sai kuma tashiga dan marin ƙuncinta a hankali ta yanda bazataji zafin marin ba tanayi tana kiran sunan ta.

Duk yanda Anna taso Aisha tayi shiru batayi ba sai wajejen asubah bacci mai nauyi yayi awun gaba da ita.

Washe gari muka tashi da mummanan labarin mama rabi ta amsa kiran Allah,sakamakon amai da gudawa cikin dare kafin akai ga zuwa asibiti rai yayi halin sa.

Anna tasha kuka sosai da ta tuna da maganganun Aisha na daren juya sai ta ɓarke da kuka karshede sai zazzaɓine mai zafi yarufeta ta lulluɓa da abun rufuwa sai rawan sanyi take kar kar kar.

Kwanan basma uku a asibiti zuwa wannan lokacin jikin ta yayi  kyau an kuma tsaida lokacin biki sati biyu zo kaga murna da rawan kai wajen basma yayinda ita ma hajia mariya ta ɗaga dubai ranan da aka sallame su a asibiti da dare domin sayayyan kayan gado da kuma kitchen na gani na faɗa acewar ta bikin ƴar gata za'ayi.

Ammi zaune take tayi jigum saboda tunani neman mafita wa ɗanta damasu baki ɗaya dan ita harga Allah bata yarda da wannan haɗin ba gani take kaman da wani abun a ƙasa.

  Kasa hakura tayi saida ta kira ƴar uwarta hajia ikilima ta waya dan su sami zama,
  Bayan sunyi waya kaman da minti ashirin sai gata dama a hanyarta da zuwa gidan takira ta.

Bayan gaishe gaishe Ammi ta gabatar mata da ruwa da lemu da ɗan abun motsa baki sannan suka zauna zaman tattaunawa.

Nan ta fayyacewa ƴar uwatata komai"yanzu ikilima ina mafita cikin wannan lamarin nifa gani nake kaman da akwai wata a ƙasa sannan narasa gane kan Alhaji inde magana tashafi Alh sunusi wallahi hankalin sa baki ɗaya bacewa yake bashi da ra'ayin kansa saita wannan bawan Allah wallahi ikilima bana tantama wannan mutumin ze iya kashe rai dan biyan bukatar sa.

Nisawa haj ikilima tayi ta kalli ƴar uwartata tace"yaya ni a tunanina mafita shine munewa Ahmad wata ƴar wacce zata kula dashi ya aura.

"Anƴa kina ganin Ahmad ze yarda da wannan?
Ko wannan da za'ayi yanzu fa saida yarinyar tanemi ta kashe kanta shine fa ya yarda amma tun tuni Alh yana maganan auren yayi biris.

guntun murmushi haj ikilima tayi tace"AUREN WUCIN GADI zamu masa kuma na tabbata kafin wa'adin yacika ze sota ya kaunace ta saboda kyawawan ɗabi'un ta sannan wannan yarinya zata maxa kariya gareshi haka shima ze zame mata kariya.

"Taya ƴar uwa?

Kawo kunnen ki nan tama Ammi wasu maganganu cikin kunneta sai ga Ammi tana sakin murmushi dacewa"inde wannan ce na yarda nabaki wuka na baki nama sai yanda kimayi.

"Wuka da nama kika damƙawa ikilima anƴa baza'ayi abun arziki awajen.

Dukkansu a tare suka juya dan ganin mai maganan alh badamasi ne da yasako kai falon yake tambaya dan jin maganan Ammi.

"Au ashe kana kusa dama maganar lefe naxo muyi dariyar jin daɗi yayi yace"a'a lalle yau anyi abun kirki ashede kin fara hankaltuwa,yakare maganar cike da zolaya.

"Au da me kaɗaukeni?
  Fuska a washe ya amsa mata da cewa"ai ke dince maciji sari ka noke.

"Lalle Alh ai kaikan ka kasani idan nayi sarata bana nokewa dan nasan a gaɓanda nakeyi.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now