48

163 16 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 48

   "K kinsan waye ubana da zaki tsaya gabana ina faɗi kina faɗi?
Kallon kasa da sama tamata sannan ta danyi wani juyi da ɗan miƙa kamande da gayya tayi haka illa kuwa sakon ya isa gawanda takeson isarwa dan kusan mutuwar zaune yayi dukda ƙokarin sa nason basarwa dayake dan yamai da hankalin sane kacokan kan systerm din dake ajiye a gaban sa idan baka sani ba sai kaɗauka wani aiki yake mai mahimmanci saide a baɗininsa hankalin sa gaba ɗaya yana kansu dan kallon kasan ido yake binsu dashi"na sani mana ta amsa mata a ƙaikaice mutum ne shi mai hannu biyu kafa biyu ido da baki da hanci sunan sa SUNUSI takare faɗi da tafa hannu sai me?
  Dawani irin mugun sauri ya daugo kansa yana kare mata kallo anya yarinyar nan tasan waye mahaifin Basma da harta iya kiran sunan sa tsirara haka,maganan da yakeyi a ransa kenan yayin da Salaha dake laɓa bakin ƙofan shiga office tayi saurin dafa bakinta da hannu tana jan kafarta takoma da baya dan baxata so suyi ido biyu da ƙawatata ba,dan ita tasan waye uban nata a rashin imani.

Ita karan kanta anata ɓangaren mutuwar tsaye tayi dan wannan shine zata iya cewa karon farko datayi kuri da mahaifinta wani mahaluƙi ya kira sunan sa tsirara haka bawani ɗan kara wai wannan yarinyar da haifuwar kaji ma zata iya cewa ta haifi irin take tsaye gabanta ido cikin ido ta kira mata sunan mahaifi haka.

"Waye ubanki anan garin?

Waya ɗaure miki gindi dahar kika samu gwarin gwiwan kiran sunan mahaifina a tsirara haka?

Yanda tayi maganan kawai ze tabbatar maka da ranta na ɓace sosai da hakan.

Itako Aisha ko ajikinta saima cewa da tayi"koba haka sunan sa yake ba?

Nagade sunan da akai masa yanka da ita kenan yo mai nawani nuna damuwa dan ankira mutum da sunan sa,taɓe baki tayi ta cigaba da cewa ni banga abun damuwa anan ba.

Idan dama saboda wannan kika kirani to kinga ninayi nan,takare dafita daga office dinma baki ɗaya,a fusace ta juya kan Ahmad dayayi kaman ma baya wajen cikin muryar kuka take magana"yanzu MY rashin darajata har yakai kana waje ana gayan magana bazaka iya tsawatarwa ba,kanajin fa yanda wannan ƴar mitsitsiyar yarinyar nake takira suna daddy haka gatsar bawani kara ko girmamawa,kawai sai tasaka masa kuka datake ta dannewa tuntuni.

Numfashi ya sauke yana mai ture systerm ɗin gefe yacire eyeglass dayasama idon sa danson kare masu kallon ya ije gefe sannan ya harɗe hannun sa guɗa yana kallon yanda ta dage tana risgar kuka"wai kukan duka na me?
  Ya tambaya kaman ma besan meyafaru tsakaninta da Aishan ba,sake sautin kukanta takara batare da tama kula shiba ganin bata da niyar amsa masa yaɗaga kafadan sa yana cewa"anyway tunda bazakiyi shiru ba shike nan inada meetin jirana ake yanzu haka zsn iya tafiya idan kin kuma gida kimiƙa sakon gasuwata ga hajia.
  Saurin shangaban sa tayi ganin dagaske fitan zeyi bata tsaya wata wata ba ta rungumesa cikin kuka take cewa"wato baka damu da damuwata shine bazaka kirata ka tsawatar mata yanxu taci bulus kenan duk rashin kunyar da tamun,ni akullum sai sake linƙaya nake a kogin soyayyarka amma kai ko oho saima kakkaucemun dakake wai mazanyi kasoni koda ƙwatancin yanda nake sonka ne.
"Hmmm Bass matsala yafaɗa can kasan maƙoshi yana zameta daga jikinsa kamo hannun ta yayi ya zaunar da ita saman kugera data tashi goran ruwa mai sanyi ya ɗauko yamiƙa mata bamusu ta karɓa tasha dan ita kanta tanada bukatar ruwan,ajiyar zuciya ta sauke tana kafesa da ido,kaman bazece komai ba sai can kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali yace"abunda nakeso kikasani mu ƴan kasuwane bawai ƙarƙashin wani muke ba balle ya mulkemu.
   Sannan a harka ta kasuwanci ba nuna ma mutum iko akan abunsa,bakibi hanya daya dace ki mallaki wannan kaya ba,da farko kin nuna kinaso kuma dole a mallakamiki wannan dole ya tsaɓa ka'idan mu ƴan kasuwa,sannan kinnemi mai abun kina bukatar abu awajenta amma kina nuna ita bakomai bace face wata ƙaskantacciya.
  Yama za'ayi ta saurareki,da ace sari zakiyi ko pieces dubu kikace kina bukata kunyi ƙudi kinbiya wannan kina da ikon abunda zakiyi dasu koda kingani a jikin wata kafin yaxo gareki hakkinkine kibi diddigi.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now