37

151 16 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Chapter 37

    Yanda suhail yake zayyano mata da sirrin zuciyar sa da kalamai masu sanya farin ciki karshe har bacci ya dauke ta suna kan waya saida yaji saukan numfashita sannan ya sumbashi wayan shima yakwanta.

Hajia mariya suna tattauna yanda tsarin komai ze kasance musu a bikin ita da kawarta hajia bilkisu  dan bikin ƴar gata za'ayi acewar ita hajia mariyan"dole ƙawata ƴar gwallin gwalin ai dole a gwada mata gata saide kawata wani hanzari ba gudu ba.

"Uhmmm ina jinki hajia mariya ta faɗa tana maida hankalinta ga ƙawartata dan tasan da magana a bakin ta.

"Yauwa dama batun tarewar angon a nan gidan naku duk da banso saka bakina acikin lamarin ba amma gani nayi mai ze hana tunda yaron shima naga kaman  da rufin asirin sa kiyi magana da Alhaji ya bari ayi mata jere a ɗakin ta kinsan bakin mutum mugun abu kuma ko dan saboda ƙawayen mu da ƴan gulma da ƴan bani na iya dole sai kanayi kana canza taku kinsan haka kawai wasu gulma da tsugu didi ke kawusu zuwa gidan biki kinga idan ko yarinya bata tare ɗakin miji ba yo mai amfanin zuwa dubai sayomata kayan gado kinga ai asara ne tunda basu fita cikin gidan naku ba.

Nisawa hajia mariya tayi ta kalli kawartata tace"kumafa balki magananki tana kan hanya,amma kibari kawai zanyi magana dashi Alhaji idan yaƙi zan haɗa da babba yayansu tunda yana jin maganan sa.

********
Aisha ta dauki wanka tana zaune tsakiyar gado suna video call da suhail sai zuzuta kyanda tamasa yake"Aisha wai menene sirrin wannan kyawun naki?

Fari tayi da ido ta dan tura baki cike da yanga tace"kaine sirrin ƴar dariya yayi cike da jin dadi yana shafa kansa da hannu nockin kafar ɗakinta akai tana daga kanta sukai ido hudu da Malik dayayi kicin kicin da fuska yace"dallah malama kifuto mu tafi kin tsaya kina batan lokacin saboda rainin wayo kin barni ina jira kaman wani drive kinzo kin zauna kina ta zuba a waya.

Langwaɓe kanta tayi cikin siririyar murya tace"sorry gani nan zuwa yanzu,dalla mata harara yayi ya juya yana banƙo mata ƙofa dayin ƙwafa.

Ajiyar zuciya ta sauke"lafiya?Suhail ya tambayeta ta daya bangaren dan ganin mood ɗinta ya canza lokaci ɗaya"aiki zani shi kansa sai yanzu ya tuna suna da meetin da wasu baƙi gashi kuma tun ɗazu yana ganin kira daga P-A ɗinsa daga ɗaya daga cikin wayoyin sa amma ya gagara ɗaga kiran"yanzu sai yaushe kuma?

Nasan idan kin tafi aiki ba lalle nasame ki a waya ba,kuma gaskiya baxan iya yini ba tare da nasake jin muryarki ba.

"Mayi waya data yaya khalid amma fa banda vid call saboda kasan yanayin aikin mu"ok yanzu de zaɓamun kayan da zansa nafita,waro manya idanunta tayi tace"ta ya?

Clothes set ɗinsa yanufa yafara ɗaga kayan gasunan burjik kaman zaka buɗe kanti saboda yawansu,can ya ɗago wani blue suit sunyi mata kyau a ido tace wannan sai kuma waje net tie shima ta zaɓa masa sai agogo sai kuma takalmi saida ya kewaya yasaka kayan ya feshe jikin sa da turaruka yafito fes dashi sai zuba murmushi yake haka kawai yatsinci kansa cikin nishaɗi gani habibty sa tazaɓa masa kayan gani yake kaman tunda yake be taɓa shiga data amshi shi irin ta yau ba.

Anty malika ce ta leƙo tana cewa"to tsuntsuwar soyayya ai sai kizo ki wuce kin dasamun ɗan uwa ke kina zaune nan hankali kwance kuna shan soyayya cike da kunyarta tamiƙa mata wayan ta dauki jakarta tayi waje a guje duk kiran da Anty malika take na ta tsaya ta karɓi wayanta ƙi tayi,gaisheta da Suhail yayi shiya an karar da ita ashe bata ma kashe wayan ba,amsa masa tayi cike da kunya tace"yi hakuri na kora maka ita ko?

Labas dama shirin sallama muke kika shigo ki gaidamun da su ummi zasuji ta amsa ta kashe wayan a ranta tana yaba kyaun Suhail ko ina Aisha ta tsinci diamond haka.

Ahmad ya gama ciki yana batsewa ganin yanda lokaci ya ƙure Aisha bata zo ba,gashi yana son yau tayi masa wasu ɗinkin dan ita kaɗai ya yarda duk cikin ma aikatan nasa dan yasan ita bata saka wasa a aikinta komai yinsa take tsakanin ta da Allah bata saka ganda ko son jiki komai wuyan ɗinki idan yabiyo ta hannun ta yinsa take ba tare da ƙorafi ko cusgune fuska ba.

Tana sauka a motar tana sake marairaice murya tana bama malik hakuri ganin yanda yake fushi tace"haba yaya malik a haka zan baka lil sisi ta kana irin wannan cinmun magani haka aikuma na baka hakuri ko.

Besan sanda murmushi ya kubce masa ba yace"kin ganki ko?

Ki kiyayeni Aisha wallahi kiyayi ranan da zan damƙoki ko wannan mai jan kunnen naki be......"sai kifito ai duk makara da kikayi kuma still kin tsaya kina.....Ahmad ne yake magana tsaye yake bakin kafar motar"barka da safiya yah Ahmad shima malik ya katse masa faɗan daya zo da ita.

Miƙa masa hannu yayi sukai musabaha"lefin kane ko?ya tambaya yana tsare malik din da ido.

"No ya amsa masa yana kallon Aisha data marairaice fuska alaman ban hakuri.

Maida idon sa yayi kan Ahmad daya tsare shi danson jin mai zaice"hajia sai kifito tunda mun ƙaraso jiki ba ƙuzari ta fito daga motar ta raɓa gefen Ahmad zata wuce ƙamshin turaren data shafa mai sanyin ya daki hancin sa,lumshe idon sa yayi kafin yabuɗe su harta ɓace masa shama malik yashiga motar sa yana kokarin ta dawa a ranshi cewa yake wazai iya da wannan muzuran naka.

Tana shirin shiga hall din ya katseta da cewa"biyoni office.

Wani irin abu ta hadiya mukut dan ita batason wani ƙeɓewarsu dan taga alama iskanci yakeson koya nata.

Shiga hall din tayi kaman bataji shi ba,tanufi saman keken ta tana gaisawa da abokan aikin nata"kee Aisha aka kirata daga bakin kofan yanda taji murya sa ba wasa ciki hakan yasa ta miƙewa ta tako cikin takun ta ta nufosa ganin tana zuwa yasa shi yin gaba,binsa tayi a baya har cikin office ɗin sa tun kafin yayi magana ita tafara bashi hakuri.

"Dan Allah oga Ahmad kayi hakuri wallahi bazan sake makara ba.

Shagala yayi da kallon ƙaramin bakin ta dake motsawa gwanin sha'awa kai Ahmad kai controlin kanka karkabada kanka ga ƙaramar yarinya ta rainaka.

Wata zuciya ta gwaɓe sa,murtu fuska yayi kaman wanda aka aikowa da tsakon mutuwa yace"menene hukuncin wanda ya tsaɓa yarjejeniya?

Da mamaki take kallon sa dan ita iya sanin ta batasan da wani yarjejeniya dake tsakanin su ba.

"Ni bamuyi wata yarjejeniya da kai ba.

"Ni kike turawa baki Eshow yanda yakira sunan saida gaban ta yafaɗi.

Bata ankara ba taji ya canko bakinta ya haɗa da nata yana tsotsa kaman wanda yasami lollipop hawaye zallah ta ƙaicin abunda yake mata takeyi dakyar tasamu ta tureshi gefe tana mammashe leɓen ta saboda zafi da yake mata.

Allah ya'isana nide kalle ka kaman mutumin karki a ido amma cikin ka fal iskanci ba abunda ka iya saison koyamun kawai saboda ka lalatamun rayuwata kacuce ni narasa wanda ze aureni.

Shi maganarta na karshe har dariya taso bashi.

"To ba gani ba tunda nine nayi barnan sai na aureki idan kin rasa mai auren,yafaɗi haka cikin halin ko in kula.

"Allah ya sauwake wallahi ta faɗa tana fita da gudu dafe goshin sa yayi yana furta"ya salam wai meke shirin faruwa dani ne?

Akan wannan ƴar yarinyar bana iya controllin kaina akanta kuma bana jin haka ga kowace mace sai ita Allahumma ajirni..



ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now