68

165 13 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 68

     Shiru Ammi tayi badan tasoba ta zubawa ƙanwarta dake kwance saman gado ido duk ta rame ta zube lokaci guda kaman wacce ta kwanta jinyar kwanaki,sauke ajiyar zuciya tayi sai kuma ta kalli Ahmad dayayi zuru da faisal dake gyawa mahaifiyar sa kwanciya tace"yanxu ya'ake ciki?
  "Eh Ammi yanzu haka nayi report tun tuni harma an baza jami'an tsaro dukkan nin madakatai tashan mota harma da airport jami'an mu na nan dakuma dukkan nin checkin point faisal ya amsa mata da faɗi haka.

"Allah ya bayyanar da ita yasa asame mata cikin aminci da salama"amin suka amsa"su kuma waƴan da suka ɗauke ta Allah yatoni asirin hegu"hmmm ƙwafa Alh badamasi yayi haryasa kai ze fita sai kuma yatsaya jin Ammi na tambayan Ahmad"kai meyakai ka tafiya da ita wajen shagalin su,bayan kasan uban yariyar nan yayake yanzu a wani hali ma ƴar mutane keciki?"shin tana hannu nagari kokuwa?Ahmad ina jin tsoro gaskiya bazan ɓoye maka ba ina jiyewa ƴar nan tsoron wa annan azzaluman sai kuma ta ɗaga hannun ta sama tana tacewa ya Allah ga baiwarka nan Aisha hannun ɓata gari ya Allah karka bawa duk wanda yakeson ya cutar da ita dama,karka basu daman da zasuyi galaba a kanta.

"Wai ke ma'arufa mekike nufi da Alh sunusi ne?nasan duk wannan abun washi kikewa,shin wani abu yataɓa haɗaki dashine?kinfa saka bawan Allan  nan gaba haba haba ko dan suru....ɗaga masa hannu tayi bata bari yaƙare maganan sa ba tace"yanzu me nace Alhaji fisabilillahi kokaji na ambaci sunan wani anan sai kuma ta juya ta kalli Ahmad tace mundin ba'asami ƴar mutane ba wallahi kadeji na rantse maka ko ƴar sarkin makka ce jibi baza'a ɗaura wannan auren ba.

Dasauri Alh badamasi ya juya yana kallon ta baki buɗe shide Ahmad be'iya cewa komai ba saima ƙasa daya sakeyi da kansa dan shi kadai yasan abunda yakeji acikin zuciyar sa.

Basma saida tayi kukanta taƙushi sannan ne salaha da tunɗazu ke bata baki tasamu daman ta kulata tace"yanzu me wancan kucakan take da wanda ni bani dashi,eh salaha kiga yanda mine ya tozartani a bayyanan nasi?ai wannan ma tozarci ne ke kinsan irin yanda nariƙa cika baki a cikin ƙawayen mu amma abunda zemun kenan irin sakayya da ze mun kenan dan yaga inason shi nasan tunda yace bazezo ya halarci partyn mu ko ɗaya ba matsawa danayi akan sai yazo na haɗa da daddyna yama daddynsa magana yazo shisa yamun haka ba komai taƙare magana. tana share guntun ƙwallan idon ta"amma ke yanzu bade kina nufin daga shi har itan sunci bulus ba?kallon salaha tayi tace"ban gane mekikeson kice ba?"ina nufin yanxu tashi zamuyi idan akwai kuɗi a hannun ki muje wajen wani malami da zeyi mana aiki akan sa dama ta ita yarinyar ta yanda koda akwai wani alaqa tsakanin su a raba adasa  musu tsanar junan su a zukatan su sannan a dasa soyayyarki a zuciyar sa ta yanda zeji duk duniya ba wanda yakeso da kauna sama dake koda uwar da ta haifesa sai abunda kikace zeyi mata.

Hmm tasauke ajiyar zuciya basma tayi cike da jin daɗi abunda salaha tace saide zuciyata taso rabuwa kashi biyu ɗaya zuciyar tata na hani gareta yayin da ɗayan ke ingizata ga tabi shawaran salahan da nuna mata ta hakane kaɗai zata rama abunda sukai mata wajen maida Aisha ƴar aikin ta shikuma Ahmad sai yanda tayi dashi dan ko wanka idan taƙi sai tace ya ɗauketa yaje yamata tana wannan tinanin kawai ta ssaki murmushi tamiƙe a hankali tayi taku ɗaya biyu tayi wani juyi tace"hmmm waya ganni ina juya mine yanda nakeso,ƴar dariya salaha tayi sannan tayi ƙasa da murya tace idan kinaso yin haka zakiyi kede kawai shirya muje gobe dawuri dan musamu zuwa da wuri saboda nisan waje kinga yanzu dare yayi amma gobe karfe shidan safe zamu fita dan musamu isowa dawuri"amma daddyna fa tafaɗa da alaman tsoro agareta"sai kisan karyar da zaki musu,abu mai sauki ma ce musu zakiyi zamu je raba iv kinga bazasu tuhumeki ba,ajiyar zuciya ta sauke tana cewa"amma gaskiya salaha kin iya law sosai dama ace law kika kiranta,dariyar jin daɗi salaha tayi itako basma  toilet  ta shiga cike da ƙwarin gwiwa ta wanko fuskarta tafito tazo gaba tangamemen madubi ta dake jera kayan shafe shafe dakuma turaruka masu sanyin kamshi dakuma tsada ta gyara fuskanta sannan tafito zuwa falo wajen ƙawayen ta dasuke zazzaune ana hiran yaushe gamo fitowarta yasasu yin shewa da dariya itama biye musu tayi tsaɓanin ɗazu dasukai mata irin haka tasaka musu kukan haushi yanzu ko samun  waje tayi ta zauna a kacigaba da hiran da ita.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now