95

208 14 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨GORGEOUR WRITEF✨
        ✨G.W.F✨

ƳAN UWANA INA MAI NEMAN AFUWAR KU NA JINA SHIRU DA KUKAYI,TSAWON WANNAN LOKACI IN SHA ALLAH HAKAN BAZE SAKE FARUWA BA.

CHAPTER 95

Kallon sa yake cike da mamakin ya'akai yasan Abokan nasa kusan ruɗewa yasoyi amma saboda bayason yabada kansa gaban yaran sai yayi kokarin daidaita kansa yana kallon su kaman yanda suma shiɗin suka zubawa ido danson ƙarin bayani kan abunda wannan baƙon yake cewa ganin yaƙi cewa komai yasa Ammi cewa da su Fadwa su tashi sushiga ciki.

Bayan barin yaran wajen Ammi ta kalle sa tace"Alhaji ka bude baki kiyi magana ko za sami bakin zaren nasani kasani Alhaji sunusi shine ummul haba isin komai dake faruwa shi kama alkawarin bazaka bude bakinka ka ambaci sunan ko ɗaya daga cikin su ba"Ma'arufa yakira sunanta da karfi cikin ɓacin rai yakuma daura da cewa zaki rufamun bakin ki yanzu anan ko sai na ɓata miki rai.

"Ai raina yadade da ɓaci Alhaji me kake gudu me kake tsoron faruwa wanda be faru  ba,inaso kasan wani abu guda wallahi koda farshen ɗaya daga cikin ƴaƴana ne ya karye ta sanadin ka bazan yafe maka ba,sai ta fashe da matsanancin  kuka.

Rarrafawa Ahmad yayi ya rungumi Ammin nasa yana rarrashin ta"Ahmad nayi shiru tsawon shekaru naxama makauniya akan abunda nake ganin yana faruwa nazama kurma narufe bakina tsawun shekaru ba tare da na furta komai ga kowa ba,ina tsoron kar wani abu yasami ɗaya daga cikin ku,amma duk da haka Mahaifinka be gani ba,dubeshi so yake ya salwantar da rayuwarsa alhalin yasan su waƴanda yarufe bakinsa dan su ba barin mu zasuyi ba.

"Rayuwace muke yinta cike da makanta zuciya sonkai  cin amana yaudara,kowa kansa kawai da iyalinsa yasani ba ruwan kowa da rayuwar ɗan uwansa ya mutu ko yayi rai,rayuwa cike take da ƙalubale kaddara wata abace da Allah ya kaddara faruwan sa tun ran gini tun ran zane wasu kaddaran kuwa muke rubutawa kanmu da hannuwan mu.

"Ma'arufa yakira sunan ta da karfi"ka gafarceni Alhaji Ammina tana da gaskiya koni kaina sai yanzu wasu abubuwa suke zuwamun wanda daa can ban kawowa kaina ba,nasan zakayi mamaki idan nace na taba ganin cocaine a cikin motan ka cikin maxubin capsule harma na dauki guda ɗaya na ajiye saboda rana irin wannan.

Magana nagaba da zan iya faɗa maka a nan shine Alhaji nasan ba sonmu kake ba,kawai de mun fito duniya ka haifemu ne badan kanaso ba kuma ba yanda zakayi da mu"shut up Ahmad Mahaifin kane fa kake faɗawa irin wannan magana inji Faisal da tun shigowan sa Falon beyi magana ba sai yanzu.

"Dont shut me up Broo shima Ahmad ɗin ya juya yana maidawa da Faisal din martani cike da ɓacin rai a muryar sa,karya nayi masane daya na son mu ba ze zaɓi farin cikin wasu da namu ba,lokacin da mu muke kukan rashin sa su kuma suna zaune cikin iyalan su suna dariya.

Lokacin da muke cikin ɓakin cikin abunda yafaru damu mun haɗa kai muna masu jajantama junan mu suko suna can cikin walwala tare da iyalansu.

Lokacin da mu muke ganin duniya ta juya mana,su kuma a lokacinne suke ganin duniyarsu ta dawo musu sabuwa saboda suna ganin burukan su yacika,a lokacin da muka kasa shiga mutane muna masu jin kunya da ƙasƙan da kawunan mu,suko alokacin zasu fito suna masu ɗaga ƙawunan su sama suna masu alfari da kawunsu,lokacin da ƴan ƙannena suka kasa zuwa makaranta suyi karatu su a lokacinne ƴaƴan su kan ƙetare hazo zuwa wasu ƙasar dan yin karatu,gidan mu yakoma tamkar gidan mutuwa zama ake a cikinta tamkar zaman maƙoƙi,an samu gawa a ma'aikarsa cikin Office ɗinsa kasani yasani bashi da masaniya akan abunda ake zarginsa a kai amma ya tsuke bakin sa yayi shiru yaki cewa komai a Kotu saboda wasu can yakeson saka rayuwarmu a garari kaxo kana shuttin ɗin Up a kan me?

Bayan kana ganin yana neman saka rayuwarmu a duhu yakake sone nayi?

Baya ganin halin da matarsa Ammina tashiga ciki a ƴan kwanakin nan,kalleta kalli fa yanda Ammina ta dawo tamkar wacce mijinta ya mutu yabarta da tarin basussuka,ta koma tamkar wata mai takaba da bata da masu kula da ita,baya tunanin ya rayuwarmu zata kasance bayan bashi tare damu.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now