82

178 21 1
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTERS FORUM* ✨

       ✨G.W.F✨

CHAPTER 82

Suna fita daga cikin falon ta kwace hannun ta daga rikon da yamata tayi gaba ta barshi nan tsaye agun yabi bayan ta da kallon yana lumshe ido wani abu na tsargar masa tundaga tsakar kansa zuwa babban yatsan kafan sa.

  Takawa yayi a hankali yanufi motar sa yabude ya dauko ledojin da ajiye a bayan motan da ɗauko yanufi cikin dasu hannunsa duka biyu yana riƙe dasu drinks ne dakuma take away daya musu yashiga dasu,a falo yasame ta zaune tayi kicin kicin da fuska tana kallon sa ta dauke kanta tayi kaman batasan da tsuwar sa a gun ba,ajiye kayan hannun nasa yayi yana cewa.

"Ki dauki waƴan nan drinks din ki kai..."kasan fa bamuyi dakai Aure aike da aiki ba,kuma ni kadena son taɓani ko hannuna ne banason kana tabawa inso samune ma kawai ka maidani gida zanfi samun nutsuwar zuciya data ruhi.

Tunda tasoma maganan ta ƙurawa lips ɗinta dake motsawa ido yanda take motsasu da sauri da sauri dayake tanada saurin baki sannan magana baya mata wuya gata da tsiwa"sadakina nataɓa idan ma na taɓan to me amfanin ki kusa dani da ko hannunki bazan rike ba?

Ina auren ki kuma zamana kike taɓaki kuma da kike wani cewa indena mai kike dashi da ze ɗauki hankalina anan mace kaman an ɗaurawa  muciya zani  jibeki fa.

Karkiyi tsammanin daɗin taɓaki nake dan ma kisani taimaka miki nake dan... bata bari yaƙarasa  maganan nasa ba ta shiga bubbuga ƙafa irin abu nan da yara keyi idan suna jin rigima tashiga yin kuka bilhakki da gaskiya idan ta tatuna sunan da yakira ta dashi na kaman anɗaura wa muciya zani,wanj irin tuƙuƙin bakin ciki ne yasake turnuke ta take taji tsanan sa a ranta ji take kaman ta jawoshi tayi ta shaƙe masa wuya haka takeji.

bedroom ɗinsa yawuce ya barta nan zaune tana kuka wanka yashiga yayi ya fito ya shirya cikin ƙananun kaya kayan sunyi matukar yimasa dayau tafi sai baza ƙamshi yake ƙamshin sa shi ya sanar da ita fitowan sa.

"Cike da tsokala yace wai haryanzu kukan kikeyi?

wani irin haushin sane yasake ƙumeta ta miƙe tsaye ta kama hanyan fita daga falon yace"haba ƴar amanar Anty hajia ina zaki kuma?

Yayi hakane saboda kawai ya tsokale ta so yake yaga wannan tsiwar tata,ai kuwa cike da fushi ta juya suna haɗa ido ta harare sa tare haɗe da murguda masa baki ta juya ta fita.

Tana fita ta samu waje ta zauna bakin baranda saman matakalan shiga falon ta kuwa lula tunani,idan ba karya idon ta yayi mata ba,kaman Alh sunusi da Alh shehu dama mutumin da ta gansu rancan tare a gidan su Basma ta gani a hoton bikin su Sajidan da ɗazu suke kallo ta gani shin wace iriyar alaqa ce tsakanin waƴan nan mutanen da mai Gidan nan dole akwai wani alaqa tsakanin su,ina da bukatar mai da hankali da kyau dakuma saka ido dan sanin mai haɗisu da Alh sunusi.

"Aisha tun ɗazu ina miki magana bakiji ba wani irin tunani kike haka?ajiyar zuciya ta sauke kafin tace"Sajida wallahi banji ba ina can ina tunanin gida ne.

"Gida kuma?
"Eh wallahi gida Sajida tasake faɗa tana ɗan yamutse fuska,da mamaki Sajida ke kallon ta bakin ta fal magana saide ganin Ahmad yana nan tasa yin shiru tana cewa zo muje ki ɗaukar muku abinci mana.

"Ayyah Sajida da kin barshi naga yashigo da abinci tasake faɗa tana miƙewa dan komawa ciki.

Biyota abaya Sajida tayi da sallama suka shigo falon yana nan zaune saman kugera ya bage wasu takardu ga kuma systerm saman cinyar sa yana aiki tuƙuru,sallama da sukai yasa shi dan tsagaitawa da abunda yake yana amsa sallamar da Sajida yamasa samun waje tayi ta zauna tana masa sannun da zuwa dakuma tambayarsa ya aiki.

"Alhamdullahi ya amsa mata yana ɗauke kansa daga kallon ta"ganin tayi shiru sai mutsu mutsu da take yasashi maida hankalin sa kanta yace"koda wani abun ne Sajida?

Sauri amsawa tayi"eh dama nace ko akawo maka abinci ne nan?"na hutash sheki ba saikin wahalan da kanki ba"haba dai Yah Ahmad wani irin wahala kuma baƙonka Annabinka.

Murmushi kawai yayi yasake cewa"yaude ki barshi kawai nariga da nayi mana take away saide ko gobe,shiru Sajida tayi dan ba haka taso ba,taso ya amsa amma ba komai idan be ci yau ba akwai gobe daga haka ta miƙe tana musu sallama harta kusa kaiwa ƙofan fita daga falon sai kuma ta ja  tatsaya tana kallon wani takarda cikin takardun da suke baje ganin ta tsaya taƙurawa takardan dake sama ido yayi sauri ɗauka ya kife,sosa kanta tayi cike da kunyar abunda taso yi tafita da ido yaraka ta.

Bayan ta yabi da kallo harta fita girgiza kansa yayi yana sauke ajiyar zuciya,biro da yake riƙe da shi yasa a baki yana sake nazari akan abunda yake typing yayi shiru yana lumshe idon sa,idan lissafin sa na tafiya yanda yakamata gobe yana da bukatar zuwa Lagos da wuri sannan ance gobe GAGARA BADAU ze sauka Garin Abuja da dare yana bukatar ya'isa da wuri kafin Madaukan nan su bar garin kafin a tsallake dasu boda.

Mami sai zagaye falo take bayan barin Sajida tana ta lissafi saita lissafa kaman lissafin ta yayi daidai kuma sai taga lissafin nata ya ƙwance,burin tane Ahmad ya auri Fauza haka kuma burin Fauzan ce auren Ahmad ɗin sannan burin mijinta ne wannan haɗin amma taya zata cika musu wannan burikan nasu saide kaman wannan yarinya mai siffar zabin na neman rusa wannan lissaafin nasu da hana musu cikan burukan su na shekara da shekaru.

Kasa hakura tayi ta miƙe ta nufi shashin su Ahmad din duk da zuciyar ta na gwaɓanta,kan kartaje ɗin amma a haka taje duk da batasan abunda zuwan nata ze haifar ba,kaman yanda xuciyar ta take bugawa haka ƙafarta yake rawa,hannun ta na rawa takai hannunta ta ɗaura saman handle ɗin ƙofan tana tura ƙofan batare da tayi sallama ba kawai ganin ta yayi ta faɗo musu kai tsaye saide abunda idanun ta suka gane mata saida ya kusa sumar da ita....


ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now