85

162 20 3
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨

     ✨ *G.W.F* ✨

CHAPTER 85

"Ke jahilar inace ke,wato baki da tarbiya ko?

Daddayn zakiwa rashin kunya harkina ke marubuciyace waye ubanki a garin nan?"Fauza Sajid yakira sunan ta a kausahe,kallon sa tayi ta watsar tana yin gaba tashigo falon tana mai jin haushin Aishan da dauka alwashin sai ta settar mata zama.

Murmushi Alhaji na Allah yayi yana faɗaɗa fuskar sa shikaɗai yasan ma'anar murmushin nasa,raɓasu yayi yawuce Mami na biye dashi a baya tana aikawa Aisha da mugun kallo.

Suna shigewa Sajida ta matso kusa da Aisha ta dafata tace"Aisha dan Allah ki koyi shanye abu idan aka miki kiyi ƙoƙarin koyan yaren shiru,saboda shi maiyin shiru idan abu yafaru nadaman kaɗanne tsaɓanin ta maiyin magana na roƙeƙi Aisha,yanda take rokontan yasata cewa"haba Anty Sajida me kike roƙona haka kina nufin koda shirun ze zamana da cutar wa kenan?

"Bama ze zama na cutarwa ba,in sha Allah tana kare ce mata haka ta itama tabisu ta shiga cikin falon Aisha ma juyawa tayi ta koma part ɗinsu,wanka ta shiga tayi tafito ta shirya cikin kaya marasa nauyi ta feshe jikinta da turare tayi sallah tana nan zaune tana azkar dinta amma fuskar wannan mutumin yakasa barin idon ta murmushin da yake dauke saman fuskan sa sanda ze shiga falo abun ya tsaya mata a rai.

Shin me wannan murmushin nasa yake nufi?

Kode kaman yanda Anty sajida tace din ta wuce gona da irine,kwarai kin wuce Aisha wani ɓari na zuciyar ta amsa mata,kema ina ruwanki da shi daga tambaya saiki wuce iyaka,ke bakin ki be iyayin shiru ba ko.

Ya'ilahir alamina,yanzu ina mafita ta fada tana mikewa tsaye ta shiga zaga falon,Ya Allah ka dawomun da Ahmad lafiya koma me ze sameni ya sameni yana kusa dani haka kawai taji  tana bukatar sa yau kusa da ita karo na farko a rayuwa da taji babu daɗin maida martani ga mutum shima ai yacika shishshigi ne ta faɗa tana kaiwa zaune daga bakin ƙofan shigowa falon nasu.

Alhaji na Allah suma shiga falon be tsaya nan ba yawuce ɗakin sa dan yin wanka kaman yanda
Mami ta bukata,yana sako kansa falon nasa yashaƙi daddaɗan kamshi turaren wuta daya kauraye da sanyin Ac kasa hakura yayi saida yace"lalle Mamin yara kice yau tarɓa na musamman akamun.

Murmushi tayi tana cewa"yanzu de shiga kayi wanka bara na ciro maka kayan da zaka saka sai kafito falo muna jiranka cin abinci idan baka manta ba nace maka zamuyi lifayan cin abinci na duka ahali ko?"ina sane ban manta ba ai hakan ma yafi cin abinci a tare da iyali yana kara dankon kauna"nide shiga kayi wanka kafito tace tana fita daga ɗakin.

Tana fita ya ɗauki wayan sa yakira wani tana fara ringin aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren"yauwa aci mugu inaso ka bin diddigin Office hukuman yaƙi da kasa ƙauri ka binciko mun shin Ahmad yayi Join aikinsa ne bayan barin sa.

"Alhajin Allah bade Ahmad Badamasi kake nufu ba?
wanda yakira da aci mugu ya tambaye shi.

"Shi fa ya amsa gumi na tsastsafo masa saman goshin sa.

Aci mugu yace"inde Ahmad yayi join aikin nan gaskiya akwai matsala dan shi mutum ne wanda baya taɓa juya abaya akan duk abunda yasa gaba.

Amma Alhajin Allah wayace maka Ahmad ɗin na garin nan kuma ya join aiki dan yau mako guda ina bibiyar duk wani motsin ma'aikarnan kaman yanda Idon mikiya yafaɗamun amma ni banga wani canji ba daga office din nasu amma de bari nasake bincika naji zan kira ka"ok sai najika amma fa kar adauki lokaci ba tare da samun wani feed back daga wajen ka ba,dan magana danake dakai yanzu haka Ahmad din yana gidana da wata yarinya mara kunya yau kwanan su uku a gidan inji mai ɗakina amma koda naxo an shedamun ya fita da safen nan be dawo ba.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now