78

206 24 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITERS FORUM*✨
    
      ✨  G.W.F✨

*HOME OF GORGEOUS,INTERLLIGENT,AND EXPERT WRITERS, WE THE BEST AMONG THE REST*

CHAPTER 78

   Saida tayi kukan ta ta ƙoshi sannan taja jikin ta takoma inda tayi sallan ta kwanta,a ƙudundune tana rufe jikin ta da hijabin ta.

Wai meke damuna ne?me saya bana iya riƙe kaina muddin ina tare da ita ne,anƴa zan iya cika alkawarin da na daukawar kaina kuwa?
    Cigaba da hakan bayana nufin sayawa kaina raini daga ƙaramar yarinya ne?haka yayi ta sakawa yana warware wa harde daga ƙarshe yasamu waje ya zauna.

  Knocking kofa da a kai yasa shi tara hankalin sa gu ɗaya yana bada izinin shigowa,a hankali ƙofar ta bude ya kafe ƙofar da ido dan son gani wa ze shigo sallama dauke a bakinsa ya sako kai falon fuskar sa ƙawace da murmushi,amsa sallaman yayi yana miƙewa tsaye ya nufe sa shi ɗin ma fuskar sa a sake ƙawace da murmushi kwance saman fuskokin su.

   Rungume juna sukai ko wannen su yana mai farin ciki haɗuwa da ɗan uwan sa,zama sukai a tare suna sake gaisawa da tambayan juna ya bayan rabuwa,nan fa hiran yaushe gamo ya ɓarle tsakanin su ko wannen na yana bawa ɗan uwan sa labarin bayan rabuwar su.

Nan sajid ya dubi Ahmad yace"hala aikin ka kakoma?

"Nap ban koma ba tukun na de gaskiya har yanzu ya faɗa yana ya mutse fuskan.

"Oh ai naji labarin wai akwai wanda a ka turo zeyi resume a office gobe a can ma'aikatar  kasan wana kawo a raina kuwa?
  Ya faɗa yana kafe Ahmad da ido.
Girgiza kansa yayi,faɗaɗa murmushin sa yayi yana nuna ahmad da hannu yace"wallahi kai nakawo a raina"hmmm saboda?be karasa ba yayi shiru()"eh sabida ma'aikatar ku yana da bukatar jajir tattu irin ka masu tsayawa kan gaskiya.
   "Sannan anfi kashe ire iren mu ba ya tari numfashi sa da fadin hakan,saboda ana ganin kaman muna katsalan dan cikin rayuwar wasu,kana ganin shekarun baya yanda ake farautan rayuwata ba, dan de Allah ya tsare ne da yanzu saide tashin zance,saboda kawai mun kame wasu gurɓa tattun da miyagun ƙwayoyi masu illa dakuma miyagun makamai da muka kama shekaran me ya biyo baya?sai da aka kashe mana jajir tattun yaran mu mutum uku sai daga baya dana bincika ashe ma'aikatar mu ita ke saida bayanan ta na sirri ga waƴan nan yan ta 'addan,ba kuma ko wace uwace zata zauna tana gani ta rasa ɗan ta ba.

Uwa ita ke daukan ciki tsawon wata tara da kwanaki sannan tasha  azaban naƙuda haifuwa dakuma shayarwa ta kuma bashi tarbiya amma ace rana tsaka wani ya kashe mata ɗan nan nata wani irin raɗaɗi ganin wannan uwa zata ji?

Wani irin hali wannan uwa zata shiga?Ammina tana ɗaya daga cikin iyayen da basa son su rasa yaran su yasa ta hanani aikin kwata kwata,kuma na hanu.
  Yanzun ma wani aiki ya kawoni garin nan,ai kwanaki na faɗa maka irin sana'a da nake ko? yayi hakane dan son ɓangarar da wancan zance.

"Eh kafada mun to munyi da wasu costomer's shine nazo haɗuwa da su kuma inason ganin wajen su don musa mu bunƙasa sana'ar tamu.

Dariya sajid yayi har yana bubbuga ƙafa yace"kasan Allah Ahmad a shekarun baya idan a kace dani zaka iya sana'ar nan zan musa koma wayene saboda jarumtarka,murmushi gefen baki yayi yana cewa"ai maza sun faɗi kaide yanda nakeji da wannan sana'ar tawa kana ganin zan komawa aikina ne?ai ina koda NAPTIP zasu rinƙa bani linki abunda nake samu na riba bazan ba,zande cigaba da lallaɓa rayuwata,hakade sukai ta hira basu suka ta shi ba saida suka kai sha biyun dare suna hira.

"Ke wai me haka zaki shigowa mutane kina kuka wani abune ya faru tsakanin ku?

Cikin rawar murya tace"ai da sai nafi kowa farin cikin haka,kasake mami tayi tana kallon ƴar tata cikin rashin fahinta sai kuma ta bude baki da kyar tace"ba bangane me kike son ce wa ba?

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now