63

184 21 3
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 63

    Can waje tafita inda bayawan hayaniya taje ta zauna haka kawai takejin tsanar basma har karkashin zuciyarta,tsana da da batajin tana mata irinsa wani irin baƙin ciki takeji aranta yanda ta ƙanainaye Ahmad dashima yake biya mata ko kunya babu da sunan rawa tsuka tayi tasakeyin ƙwafa taja tsaki yafi aƙirga duk yanda taso cire abun aranta kasawa tayi sai kawai tamiƙe tasake shiga can baya inda batajin motsi tana nan zaune tunani duk yayi mata bake bake acikin zuciya to wai ma mai hadinta dasu data zataringa damun kaita a kansu,wata zuciya tace kode kishi kike.

"Ina ina Allah ya sauwake nayi kishi a kan ma wani dalili zanyi kishinsa? saboda yana auren ki wata zuciyar ta bata amsa kinga kuwa dolene kiyi kishinsa hakade ta ringa surutai kaman wata zautacciya ita kanta batasan adadin lokacin da taɗauka nan zaune a wajen ba,ƙusƙus datake ji a bayan wasu motoci shi yaɗauki hankalin ta miƙa tanufi in takejin kaman magana na tashi daga inda take tsaye tana iya ganin mutane biyu duk da bata ganin fuskokin su suna tattauna wani abu abunda taji suna magana akai baƙaramin tada mata da hankali yayi ba,take hanjin cikinta hautsina taji wani jiri naneman ɗibanta kaman zata faɗi da sauri takoma baya dan karsu ganta bigewa tayi jikin madubin wani mota hakan yajayo hankalin su wajen daya daga cikin mutanen biyu yashiga cewa"waye waye a wajen?

Dube dube suka shigayi ita kuma tana ja da baya jin ɗaya yana cewa daya"karmu bari koma wayene ya kufce mana sai mun kamosa dan tabbas maishi yaji abunda muke tattaunawa,a ɗan rikice ɗayan yake magana yana cewa"dama saida nace maka muhadu a wani wajen kaƙi to gashinan yanzu asirin mu yana gabda to nuwa"kai shiru nace kai shiru ya dakawa ɗayan tsawa ganin yanda ya diririce duk ya firgice kai ba namiji bane abu kadan sai kanuna tsoronka a fili sai kace wata mace wallahi ko mace ba zatayi hakan ba,amma dubeka dan Allah abu ɗan ƙanƙanni sai kabi duk katada hankalinka sai kace kaine ɗaya mai rai ran nan fa guda ɗayace kuma kowama ɗayan gareshi.

Jin yanda ɗayan yakema ɗan uwan nasa faɗan yanutsu yabata daman rarrafawa dan neman wa kanta maɓoya tasan muddin tabari suka ganta to kashinta yabushe idan tace komawa zatayi inda tafito dole su ganta kuma su kamata idan suka kamata batasan abunda zasuyi mata ba,sannan yanda take ganin idon waƴan nan kashetama za su iyayi kuma sukashe banza ba abunda ba zasuyi ba dan  kar asirin yatonu.

Neman maɓoya tashiga yi yayinda suma suke dube dube ido rufe dan ɗayan yana sake tabbarwa ɗan uwan nasa karka sake murasa koma wa

Rarrafawa tasomayi tana  jada baya suma kuwa gadan gadan cike da tashin hankali suke nemanta bayan wanj mota tasamu taɓoya tana mai ajiyar zuciya can kuwa ta tsinkayo muryansu suna waya suna sanar wasunsu ansamu matsala akawo musu ɗauki dan basason koma waye ya kufce musu,ai kuwa tuni cikin Aisha ya ɗauri ruwa gashi bata da waya a hannu balle tayi tace akawo mata ɗauki,cikin abunda befi minti goma ba saiga zugan wasu ƴan daba da makamai rirriƙe a hannun su sai kafa wuƙaƙe suke suna kiran yau zasu sha jini,ji tai inama bata fito ba tayi zamanta ai ba lalle sai ta kalli inda suke rawan ba.

"Inason ku bincika mun nan sosai kar maishi yatsare mutum ne kai koma addabane sai kun gurfanar mun dashi nan dan barin maishi haƙiƙa hatsarine garemu,oya rufe bakin sa keda wuya waƴan nan matasan samarin su takwas suka shiga neman ta harƙarkashin mota sai sun leƙa mota kuwa kona uban waye sai sun buɗeta sun duba in kaga basu duba mota ba ka tabbatar a kulle motan take,kaman yanda suke kusantota haka ita ma takeyin baya tare da canza inda take zuwa wani wajen duk ta tsure suna cikin wasan ɓoyan nan kawai ɗaya daga cikin su ya hangota ta madubin wani mota buɗe wagegen bakinsa yayi yana cewa"oga gatanan naganta dago kannan da Aisha zatayi sukai ido huɗu da wanda ya gantan miƙewa tayi takwasa a guje suna biye da ita a baya.

Ahmad da tun fitan ta yake hankalce da ita saide Basma ta kanainaiye shi taki barisa balle yasamu daman binta a baya,malika dake masa liƙi yama magana tabita abaya saide koda malikan tafita bataga inda tayi ba,harma parkin lot ta tafi amma bataga koda mai kama da Aishan ba,harma ta ƙarasa bakin get din hotel ɗin ta tambayi mai gadi koya ganta amsa mata yayi da gaskiya shi bega yarinya mai irin wannan kaman nin da ta ambata ba,tade sake dubawa ta aciki.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now