25

165 20 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Chapter 25

   "Idan yana da farare bugun abuja shi besan dacewa a rayuwar sa bane?
  Jibe shi fa tsofe tsofe dashi yawani biyo yarinya karama yana furta wani banzan kalma wai so mtsss yaja tsuka abun ko daɗin sauraro babu wallahi.

Dariya khalid ya fashe dashi harda riƙe ciki ganin da gaske abokin nasa kishi ke cin sa dan yana gani cikin kwayar idon sa,sai da ya tsagaita da dariyan sannan ya kalle sa yace"a iya sanina sai da so ake kishi...katse kalid yayi dacewa"bawani kishinta da nake kawai de banason wannan mutumin ya lalata mata rayuwane ko banza karkashina take aiki hakkin kare mata mutunci ya rataya ne a wuyana.
  Ba tare da khalid yasake bi takansa ba yace"ni kaga bara nage na turo maka da ita...saurin katse khalid yayi yana cewa"excuse me watsa masa wani kallo yayi"ni dan Allah kadena yimun irin wannan kallon naka zuwa zatayi ta gyara nan kafin bakin mu su karaso kasan tun dazu na aiki dauda dauda wato shine mai shara da goge gogen office ɗin Ahmad.
Aisha tunda na shiga hall ɗin da muke ɗinki kasa taɓuka komai nayi ba komai ya jamun wannan mutuwar jikin ba illa kuwa kalaman wannan mutumin saboda rashin hankali wai yana sona kuma aurena zeyi,
Shin fadila bata faɗa masa alaƙar dake tsakanina da ita bane?
Idan ko hakane akwai gagarumin yaƙi a gaba dan mama rabi bazata taɓa barin mu muyi rayuwar salama da mahaifiya ta ba,saboda bala'i zata yi,ko ita kanta fadilan sai inda karfinta yakare akan wannan mutumin da suke gani shine ginshiƙin rayuwar su ya fidda da su daga kanjin talauci.
Maganan khalid yadawo dani daga duniyar tunani dana lula idan de ba kunne nane baji da kyau ba kaman naje na share office ɗin oga Ahmad yace"ni kuma ya khalid na tambaye shi cikin rawan murya ina dafe kirjina da hannu dan jin yanda zuciyata ke bugawa kaman ze faso ƙirjina ta fito,innalillahi shine kawai kalla dake fitowa daga bakina.

   "Aisha ki tashi muna da baƙin da zamuyi suna tafe yi abu da jikin ki,miƙewa nayi tsaye na nufi kofan kamar kazar da kwai na aciki na fita daga hall ɗin tsinkayo muryar laila dake cewa haba"Aisha kaman wacce akace za yankaki irin wannan tsoro haka wallahi da nice nasami shiga haka da gudu zani dan bazan tsaya sanyin jiki ba.
  ban tanƙa kata ba nayi wuce wata kayan shara na fara ɗauka sannan na shiga office ɗin bakina dauke da sallama jin shiru ba amsa naji sanyi a raina dan na tabbata ogan muzurai baya ciki har nagama abunda zanyi be shigo ba,tattara kayan da ya watsar na fara a raina ina mamakin garin ya ya hargitsa office ɗin haka shi ba karamin yaro ba aiko yarone karami ba zaiyi irin wannan abun ba.
  Saida nagama na adana komai a muhallin da yadace duk da bansan tsarin komai na office ɗin ba amma made nayi bakin ƙoƙarina dan ganin komai na ajiyeshi bisa tsari sannan na shiga tsince glass cup dana gani tarwatse a ƙasa saida nagama tsicewa tass ba tare da na kula ba nakai hannu na ɗauki tsinsiya ashe akwai glass ajiki ban kula ba na damƙi tsinsiyar da karfi wani irin zafin raɗaɗi ne ya ziyarci hannun na harma da kwakwalwata jifa nayi da tsintsiyar nashiga yarfa hannun na,ganin glass ɗin cikin fatan hannun nawa yasake rikitani da kuma jini dana gani ai kawai sai na fashe da kuka nama kasa nutsuwa na zare glass ɗin sai yarfa hannun nake ina hawaye da dan shasshaka kaɗan kaɗan.

   Bazato naji hannun mutum saman nawa da nake yarfawa,waro idona nayi ina kallon sa yanda yariƙe nin sai ya haifarmun da wani irin tsoro da fargaba jikina sai kirma yake a hankali yakai ɗaya hannun sa daya da nufin cire glass din dake maƙale cikin hannun nawa wani irin zabura nayi zan miƙe damƙoni yayi yanda bazan iya kwace kaina ba yacire glass din sai hawaye nake yashiga huramun iska ta bakin sa luf nayi sai sauke ajiyar zuciya nake tissue ya ciro ya goge mun wajen sai da ya tabbata ba wani raguwar jini sannan ya sakemun hannun sauri mikewa nayi tsaye da nufin karasa abunda nazo yi"ki barshi kawai naji muryansa kaman wanda akasa dole sai yayi magana"zan iya na amsa mishi batare da na kalli inda yake ɗin ba,saida nagama nazo na goge saman babban table din dake tsakiyar office ɗin naji yana magana cikin kakkausan murya"maza kije ki kuri wancan sokon tsohun ya janye gwangwanin motar sa nan ba wajen wasan yara bane ko dandalin masoya ba kice masa nan ɗin wajen aikine kuma kar yasake zuwa nan ya parka mun mota idan ba haka ba....hannun sa ya matsa yabada wasu irin ƙasa ƙara rass tunda yafara magana jikina sai yasake ɗaukar wani irin rawa kaman mazari kwasa nayi zan fita da gudu ya dakatar dani ta hanyan cewa"wa ze kwashe miki kayan sharan komawa nayi zan ɗauka yariƙo dantsen hannuna da karfi zafin da naji a ƙashin hannun nawa har saida na furta ouuuch kalleni nan yace ƙin kallon sa nayi sai jin sa nayi yace wallahi koda wasa nasake ganinki da wannan tsohun ko naji labari kin gama yawo.
  Tsaban tsorata danayi da abunda yace na karshe wallahi da kayan sharan a hannuna na shiga hall ɗin da muke dinki sai safa da marwa nake nama rasa abunda yake mun daɗi ashe duka waƴan da suke zaune kowa ido yaxuba mun yana kallona dayawa waƴanda muke hall ɗin tare idan ka cire laila da shamsu bada kowa naje mu'amala ba iya kata da kowa gaisuwa amma ganina cikin wannan hali dayawa suna mamaki to mai yasameni firgici na fita hayyacina lokaci ɗaya.

"Wacece Aisha?
ana kiranta a waje muryan wani security dake bakin get yayi magana daga baki ƙofan shiga hall ɗin muke.
  Saurin bin bayansa nayi da kayan hannuna saida nakai bakin get sannan na tuna na ajiye a wajen masu gadi na nufi inda yake tsaye jinjine da jikin motar sa jallabiyace a jikin sa tunna ɗaxu da safe da alama ko gida be tafi ba kenan tundazu.

  Yana hangoni yafito da saurin sa a cikin motan sa niko nasake tamƙe fuskata nayi ban bari yayi magana ba nashiga cewa"haba dan Allah bawan Allah menaka na shigowa rayuwata dan Allah karabu dani anriga da anmun miji kuma ko da ace babu bazan taɓa son abunda aminiyata keso ba,idan ma ni nafara son abu tace tanaso wallahi ni mai iya sadaukarwane gareta dan haka na haɗa hannuna guɗaya alaman roƙo nace kabarni nafuta,awannin ƙalilan da shigowarka rayuwata kasani nafara fita hayyacina inaga idan kuma muka ƙulla inaga hankalina gaba ɗaya zan rasa daga haka na juya koma ciki ina ta sauke ta gwayen ajiyar zuci kaman wacce tasha kuka shiko anashi ɓagaren Alhaji shehu sake baki da hanci kawai yayi yabita da kallo dan koda wasa betaɓa tsammani yarinyar nan tana magana haka ba.

ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now