41

142 14 3
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 41

    Ɓacewa kuma Anty hajia?"eh Aisha tunda yayi wani yunƙuri akan safaran yara mata da akeyi hukuma tashiga cikin abun kaman fa da gaske daga baya shiru kikeji shikenan aka rufe babinn sa.

"Amma Anty hajjia su jami'a da muke dasu a ƙasar me amfanin su?

"Kina kallon movies?ta tabayita madadin ta amsa mata da tambaya da tayi"eh ina kallon ya amsa fuskarta dauke da mamakin ƙin amsa mata tambayarta da batayi ba.

Wata zuciyar tace yo ya zata baki amsa bayan mijinta da ɗanta duka suna cikin hukuman kuma ana damawa dasu.

Katse mata tunanin tayi da fadi"kaman de yanda kike gani a movies haka abun yake,hmmm ta sauke ajiyar zuciya tare da miƙewa tsaye tana cewa"zanje na kwanta sai da safen ku.

"Da wuri haka karfa kisa abun a ranki ya hanaki sukuni abubuwa dasuke faruwa a wannan ƙasa tamu sai du'ai"in sha Allah shine kaɗai amsa data iya bata tayi wuce warta ɗaki.

Ahmad tunda ya baro sashin Ammin sa ya dawo part ɗinsa yasamo zarya cikin falon yama rasa meke masa daɗi,wani irin tunani zaiyi shifa ba yaro bane da zamasa auren haɗi wai ace amasa aure har biyu ciki ba zaɓin sa ko ɗaya aciki.

Harma gwara Basma tunda yasanta kuma tana sonsa shine de kawai sai a hankali,to ita wanda Ammin sa ta zaɓa masa fa?

Idan yarinyar ta kasance nakasasshiya ko bata daga tsarin macen da yake so fa,kai ina yayi saurin ture wannan tunanin.

ƴanya ze iya hakura ya amsheta a duk yanayi da ze ganta kuwa,kode zuwa ze yasamu ya lallaɓa Ammin sa a ware wannan auren tunda ba wanda yasan dashi.

Amma fa kai gaulane yama za'ayi kaman ka yaro ɗan kwalisa da kuɗinka da ajikan kana da kyau sannan ka haɗa duk komai wanda ko wace ƴa mace zata soka amma ace ka kare a auren haɗi gaskiya beyi ba.

Ire iren abubuwan zuciyar sa ke injiza shi dakyar ya iya shiga  toile ya sakarwa kansa shawer ya jima tsaye a haka ruwan nabin jikin sa kafin ya kashe tap ɗin ya fito ɗaure da towel a ƙugun sa yana kuma tsane ruwan kansa da karami towel din ji yayi kaman yayi tuntuɓe da abu yasa shi janye towel yana binta da wani irin kallo wanda yasa jikinta yin sanyi cikin yauƙi da duniyanci ta miƙe tsaye tana cewa"haba my saura kwana nawane ashafa"sai kibari ashafa tukunna.

Rungumar sa take sonyi yayi saurin dakatar da ita ta hanyan daga mata hannu cike da ɓacin rai yake magana"sau nawa zance miki banason wannan ɗabi'ar yahudancin  na rungume rungumen nan.

Please fita kikoma falo zan shirya kaina"haba my to mai aciki dan ka shirya a gabana ai yanzu munriga da mun zama ɗaya kazama ni nazama kai aiko nida nake ƴa mace ba wani abu bane dan nashirya kana kallo na.

Tunda tasoma magana yakafe ta da lulu idon sa kaman na maijin bacci saida takai karshe da magana da take kuma ba alaman zata fitan haka ya nufi clothes set ɗinsa ya dauki kayan sa yakoma toilet yasaka sannan ya zo.

Gaban tangamemen mirrown dayake jere da mayuka masu tsada da turaruka masu  kala kala jere suke rurus kai kace kashiga kanti saida su,saida ya tsaya ya zaɓa sannan yafeshe jikinsa da turare kala uku duk ƙwakwafinka baka isa kace ga ainihin kamshin turare da yake ba.

A falo yasameta"me zaki sha akawo miki?

Shine tambayan da yamata sanda yake kaiwa zaune.

"Nothing ta amsa masa a taƙaice kafaɗan sa yaɗaga cikin ko in kula.

Ganin bazai tambayi dalilin zuwan nata ba yasata tasowa inda take zaune tazo da zauna kusa dashi ta ɗaura kanta saman kafaɗan sa tace"wai me yasa baka sona?

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now