55

168 15 1
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHSPTER 55

Dariya suka kwashe dashi gaba ɗayansua tare kaman wasu bosawa saida sukayi mai isarsu suka buɗe kwalban barasa shamfe suka shiga kwankwaɗa nan Alh sunusi yake sanar dasu ƙudurinsa"saka hannun wannan mai taurin kan ɗan nasa nake bukata fiyot a wuce wajen.

"To ita kuma ɗiyar taka ya zakayi da ita kasan yaran zamani da shegen hange hangen su wai SO kartaƙi yimana yanda muke so saboda soyayya kasan soyayya ba abunda baya sawa mutum yaƙiyi soyayya maida maƙiyi masoyi.

"Nabi soyayya da gudu ai bazan bari soyayyar ɗan miƙiyina ya tasirantu a zuciyar ɗiyata ba dole itama ta fifita buƙatana sama da komai na duniya dan wallahi ko ɗan yatsan hannuna ne naga ze shiga tsakanina da nasarata da muradina to wallahi guntule shi zanyi kagako ba abu mai wahala bane kawar da duk wanda ze nemi kawo mun cikas ko yun ƙurin cin amanata daga doron duniyar nan,mukut su biyun suka haɗiyi wani ƴawu mai kauri dan Alh sunusi idan ya furta abu ba makawa to kuwa zeyine kamande yande ya samu nasaran kawar da abokan kasuwancin su da dama ace warsa maciya amana ne.

BAYAN KWANA BIYU
Yau aka sallamo Aisha daga asibiti da tarin magunguna Aisha dake zaune bakin gado ta zubawa guɗaya ido da alama tunani take yayinda Anty malika kuma tashiga harhaɗa masu kayansu dan tayi waya da Anty hajia ma tace tayi zamanta yanzu suma za suzo tunda an sallame su,dr sufyan nagani zaune a office ɗinsa sai rubutu yake a wata doguwar paper yana rubutawa yana sakin murmushi dr irfan daya shigo ya'iskesa yayi murmushi yana girgiza kansa dacewa"lalle iska yana wahal da mekayan kara.

Ɗagowa yayi ya banka masa harara sannan yasake maida kansa ya cigaba da rubutun da yake,zama dr irfan yayi kan kugera dake fuskantar abokin nasa yace akan wannan zaman rubutu da kake mai ze hana kaje ka tunkareta gaba da gaba da bukatarka kasan fa yau shine last chace ɗin dan yanzu haka na barota sai haɗa kayansu take kaga kuwa tafiya zatayi sunan ta kawai kasani ba address ba ba ba ba...yakare da zolayarsa zunbur dr sufyan yamiƙe yana kallon dr irfan da shima shidin yake kallo yace"karkace mun haka"to shike nan tsaya kallon ruwa ƙwado yama ƙafa.

Be ma sake bin takan dr irfan dake faman yimasa tsiya ba yayi waje da mugun sauri shiko dr irfan mai zeyi inba dariya ba yana cewa hmm su so manya daa idan ance akwai so kaine kan gaba wajen musawa mutum babu so yanzu ko wace ƙaniyarce kuma wannan yana kare faɗin shiɗin ma fita daga office din yayi yaja masa ƙofa dan dama zuwa yayi ya faɗamasa mutuniyar tasa fa sai faman haɗa kaya take.

Hajia mariya nagani zaune sai zabga murmushi take wato bukata tabiya kenan ta dauki waya takira aminiyarta Hajia balki a waya kira ɗaya ta daga kaman dama jira take"kawata kice tasamu kenan kira a wannan lokaci haka?

Dariya hajia mariya ta kwashe dashi tana cewa"oshe ita hajia balkin dariya tayi daga nata ɓangaren tana gyara zamanta saman gado tace ban nasha da dumi dumin sa.

"Ƙawata komai yayi daidai wato wannan magani da kika bani bala'ine wallahi musibace bakiga yanda Alhaji ya susuce akaina ba wallahi,ai bayan komai ya lafa ina kawo masa buƙatata be wani ja zancen ba sai cewa yayi ai dama can gani yayi kaman nice banida sha'awa yin kasuwanci take ya cakemun 10m inja jari ke in faɗa miki harda babban shago dakuma store ajiye kaya.

"Wayyo daɗi kice duniya sabuwa ƙawata yanzune zaki faso gari,yanzu yaushe kike ganin yadace muje mufara miki sari kinsa ance da zafi zafi ake dukan karfe.

Ɗan jim tayi kaman mai tunani sai can kuma tace"ca nayi mubari harsai an gama bikin basma tukunna kinsan wannan satin ne kuma inajin kaman gobene zasu fara wasu event din.

"Shike nan hakanma yayi amma kisamu kizo mukoma wajen bokan nan ta yanda zaki samu kan Alhajin sosai duk da shima tsaye yake amma bazaki zauna ki zuba masa ido ba.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now