91

284 17 3
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S  FORUM* ✨
       ✨G.W.F✨
_______________________
GORGEOUR INTELLIGENT AND EXPERT WRITTER'S WE ARE THE BEST AMONG THE REST.
_________________

CHAPTER 91

Saide wani abu Ahmad kasan dole wannan aikin yana bukatar plan dolene kayi wani abu dazaka kawar da hankalin su a kanka kafin mufara aiki,dan fa kasan wayan nan mutanen ba imanine dasu ba kawar da duk wanda suke ganin ze zame musu matsala ba wani abu bane agunsu koda mutum yana cikin sune balle kuma wanda baya cikin su.

Kaman de kai yanzu tunda mafi yawansu sun san Aikin ka to kuwa dole za suna kula da duk wani motsinaka,dolene musamu wani abu da zakayi wanda ze dauke hankalin su akanka kafin mu san abunyi.

Shiru sukai dukkan su su biyun kafin kuma Abdullatif ɗin yace me plan ɗinka kafin kashigo garin nan?dan nasanka farin farin sani ba haka kawai kabar Case ɗin Mahaifinka kazo nan Gari ba dole dawani abu.

Murmushin gefen baki yayi sannan yafurta" GAGARA BADAU wayeshi?aina yake da zama ban sani ba amma wannan shine first target ɗina shine kuma abunda yasani shigowa garin nan.

"Tabb Babban magana wai ɗan sanda yaga gawan Soja,maida hankali Ahmad yayi kansa yace"Abdul yanaga duk yanayin ka ya canza daga jin sunan GAGARA BADAU dakaji na ambata.

"Ba dole kaga yanayina ya canza ba Ahmad,tunkaran wannan mutumin fa kaman ace ka tunkari Aljani ne,bawani wanda yasanshi ba wanda yataɓa ganin sa kai ko muryar sa ba wanda yasani intakai ta maka zance suma kansu manya dilolin wayancin su idan muka kamesu ca suke suma basusan waye wannan GAGARA BADAU ɗin ba,yana zaman meetin dasune a duk sanda ya bukata kuma vid call suke yana rufe fuskan sa sannan ana sarrafa muryar sa da na'ura mai tace murya kaji suma dake aiki a ƙarƙashin sa i naga irin mu,masu neman hanyan kamesa da lefi.

_ASIBITI_

Kwance yake kaman gawa samɓal saman Gado bambancin sa da gawa numfashin sa dake sauka a hankali ɗaya hannun sa da ƙarin Ruwa Mami na zaune ta rabka tagumi hannu bibiyu Sajid da Ahmad sunkoma gida Mamice zata kwana wajen sa,to fitan da sukaine Ahmad yasamu yaje Gidan Abdullatif ɗin dan ganin ya Aisha take da jikinta.

Karfe 1:30 yabude idon sa ya kalli inda yake take kuwa komai daya faru yasoma zuwar masa kaman yanzu akai,rintse idon sa tayi da karfi a ransa yana tsinewa Alhaj Sammani da gurguwar shawaran sa.

Washe gari aka sallame shi suka dawo Gida tunda suka dawo yake ta zuba ido yaga ta ina ze ganta saide har aka yini beganta ba,kasa hakura yayi da yamma yafita ya zauna waje cikin wata ƴar rumfa da akayi sa dan shan iska nan yace a shimfiɗa masa darduma ya kishin giɗa awajen tare da wasu abokan harkallan sa dasuzo duba shi.

Suna nan zaune Ahmad ya dawo daga wajen aikin sa saida ya daidaita parkin ɗin motan sa yafito yanufi inda suke cikin takunsa dake nuni da shiɗin cikekken Namijine tunda kan ya ƙarasa isa inda suke"Alh na Allah yace da abokan sana"change the topic cikin yin ƙasa da murya yayi maganan shiko Ahmad yajishi tsaf dan Allah yamasa baiwan jin magana koman nisan dake tsakanin sa da mutum ko kuma mutum yayi magana cikin yin ƙasa da murya.

"Assalamu alaikum
Yace dasu sanda ya isa garesu yana miƙa musu hannun sukai musabaha sannan ya kalli Alh Na Allah yace a jiki Alhamdullahi tunda gaka zaune awaje fata de Allah ya kiyaye gaba adinga kula dan sake faɗawa a irin wannan hali"haka hakane Alh na Allah ya amsa maganar tasa a rarrabe sai kuma ya kalli abokan nasa yace ɗan wajen Alh Badamasi ne Ahmad,riƙo hannun Ahmad ɗin ɗaya mutumin yayi yana cewa"Ikon Allah Alhaji kalli girman ɗan mutum ba wuya Ahmad kaine haka badan Alhaji yafaɗa mana ba dasai muwuce ka wuce ko a hanya muka haɗu.

Yafaɗa yana faɗaɗa fuska da murmushi sai kuma ɗaya mutum ya amshe yana cewa"eh hakane wallahi wane aiki kakeyi kai yanzu kode irin aikin Mahaifinka kakeyi dan kaganmu duka muna da hannu jari a companyn sa kuma bamuji daɗin abunda yafaru dashi ba,yakare maganan yana mai kai duban sa ga AlhNa Allah dayayi suman zaune dajin ɓaram ɓaramar da Abokin nasa yayi yasaki baki sai sake zance yake.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now