47

134 14 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 47

    Suna shiga cikin ɗakin sukaja suka tsaya ganin ba wani alaman wannan mata ta motsa,inna fure ce ta kalli boɗɗo cikin harshen fillanci ta kai dubanta ga boɗɗo tace"anƴa bakarya kika mana ba matan nan ta motsa kuwa?

Cike da yarintar ankirata da makaryaciya ta shiga dirza ƙafa tana mustsuke ido ta ƙwaɓe baki tasaki kuka kai da gani kasan kukan shagwaɓane cewa tayi"am inna aide naji tace ruwa ruwa inma karya nake kutashe ta ita zata faɗi,kanta modibo yashafa yace "yi shiru boɗɗon Abba ai nisan bakya karya inna inaga mubata ruwan taimakawa inna fure yayi suka ɗan ɗagota suka shiga bata wani ruwan jiƙon magani da Abba yanemo cikin daji ya jiƙa,sunyi mamakin yanda tasha ruwan dadama,inna fure kasa hakuri tayi fuska ƙumshe da annuri tace"da alama fa lafiya tafara sumuwa tunda tsawon wannan lokaci data ɗauka cikin wannan hali dakyar ruwa yake wucewa ta maƙoshinta amma duba yau kaga hamdullahi tasha dadama wannan ma wata nasara ce.

*****
Daddagewa tayi da datsa masa cizo a harshen sa ai kuwa besan sanda yature ta daga jikin sa ba idon nan nasa sunkada sunji jajur,share hawayenta tashiga kana tace"kwarto anfaɗa kwarton saika tsireni ta kwasa a guje tayi waje bangaje juna sukai da jamila dake laɓe tana dakon fitowarta ai kuwa batayi wata wata ba ta damƙota ji kake fass fass ta sharara mata ruka har sau biyu,ita ma Aisha cike da jarumta dan ita bataga dalili da za'a mareta haka ba,tunda bada saninta taxo ta bigeta ba.

Ramawa tayi tana nunata da yatsa tace"idan kina cin kasa kikiyayi ta shuri bada sani na bangajeki ba amma kiyi hakuri harta juya ta fara tafiya sai kuma ta dawo da baya tace bafa hakuri akan marin da narama nake baki ba a'a hakuri akan bangazan ki danayi ne.

Baki sake jamila ke binta da ido dan kusan suman  tsaye tayi ita kan ta bata taɓa kawowa a ranta wannan ƴar ficikar yarinyar zata iya ɗaga hannu ta rama marin da tamata ba,dan haka tanaji tana gani Aishan tabar wajen harta ɓacewa ganin ta bata iya yin komai akai ba.

Alhaji badamasi zaune suke da abokin sa Alhaji manzo nan Alh manzo ya ƙurɓi lemon mai sanyi saida ya ajiye cup din hannun sa kana yadubi abokin nasa dacewa"kaman naji kishin kishin wai an ɗaurawa Ahmad aure da wata bayan ƴar gidan Alh sunusi da kowa yake tsammani,wani irin zabura Alhaji badamasi yayi yace"mai nakeji kake cewa ne kode nine banjika da kyau ba.

"Karde kace dani bakasan abunda ke tafiya a gidan naka ba,to inde haka lalle da.....sai kuma yayi shiru take zufa yakaryoma Alh badamasi inda yatuna maganan su da Alh sunusi na karshe inda yace dashi nayarda ƴata zata tare gidan ka bisha wasu dadilai amma kasani auren ɗanka da ƴata ba saki babu kishiya  babu taƙura duka abunda takeso shi zatayi matukar ɗanka ya tsallaƙe daya daga cikin wannan sharuɗan jinin sa ya halatta dan zamu sadaukar da jinin sa wa dodon mu.

Yana kawowa nan da tunanin sa kawai ya miƙe zumbur yashiga safa da marwa yama rasa tacewa sai shi Alh manxo ne daya ƙara dacewa"yanzu me mafita kasan sharaɗin da Alh sunusi ya ginɗaya maka kuma a gaban dodo akai wannan yarjejeniyar nima  kaina da wannan labarin ya zomun na kaɗu sosai nasan tabbas ba'a saninka hakan yafaru ba.

Amma kajeka kabincika a hankali cikin hikima zaka tunkari ita hajiar dan tanada masani komai tunda nima abakin mai ɗakina natsinta.
   Da haka suka rabu da Alh manzon inda ko
sallaman kirkiri betsaya yi da abokin nasa ba yanufi motarsa driven sa na ganin sa ya nufosa da sauri yabuɗe masa murfin motan saida yashi ya xauna da kyau shima drivrn ya zajaya yashi yama motar key sannan cikin ladabi da biyayya yace"Alh ina muka nufa?

Muje gida ya amsa masa a gajarce
Koda isarsu gidan be tsaya jiran sai anbude masa motan ba yabude da kansa yanufi cikin fuskar nan tasa hade kaman hadarin gabas zuciya tamasa nauyi har wani huci yake,ko sallama be tsayayi ba,saboda rufewar ido bemaga waƴan da suke zaxzaune a falon ba yana shiga kawai kan Ammi yasauke idon sa.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now