46

165 18 4
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 46

      Ba tare daya dago daga abunda yakeyi ba yace"jeki ki dubomun Aisha cikin musu ɗinki,wani irin tuƙuƙin bakin ciki taji ya turnuketa tama rasa meke mata daɗi koba komai ai yabari yaji dame taxo amma sai wani shamƙamshi yake duk uban kuɗin data ɓata wajen yimasa kwalliya dan ganin ta burgesa amma a banza.

Saurin juyawa tayi ta fita tana jawo kufar da karfi yabada sautin garammm ɗan tsuka yayi ya cigaba da abunda yake.

Yau asabar anwayi gari da labarin ɓacewar wasu riƙaƙƙun ƴan ta'adda da hukumar ƴan sanda ke nema ruwa a jallo,wannan abune daya tsorata sauran ƴan click ɗinsu dama manyansu kai duk wani ɗan mafiya ya tashi da tsananin tsoro da fargabar yake da ɓacewar manyan yaransu har guda hudu LION da akafi sani da NO17 sai junior sai kuma kaska da bazuka ɓatansu ya girgiza manyansu dama ƙasa baki ɗaya dan ba wanda yasan taƙa maiman wanda ya ƙwamushe su,hukuman ƴan sanda tuni sukai zaman gaggawa dan acewar su wannan abun kunyane ace suna aiki ba dare ba rana amma ace sungaza kama waƴan nan mutanen saide kawai suji labari agari wai wani ya kamesu ba su ba,wannan abun kunyane gare sosai cikin ɓacin rai IG yamiƙe yana tada jijiyoyin wuya yana faɗa cikin tsananin bacin rai yace yabasu nan da awa 48 dan ganin sun kamo wanda yayi wannan aika aikan kokuma suda aka kaman wannan umurnina yafaɗa da kakkausan murya.
Duka amsa masa sukai da yes sir.

Duk da sunsan abune mai matukar wuya ace susamo waƴan nan mutanen cikin kwana biyu dan duk wanda yayi wannan abun ba karamin shiri yayi ba.

"Alhaji ya ina faɗamaka ga abunda boka yace kana ɓagarar da zance wallahi wannan bokan aikinsa kaman yankan wuƙa yake baya karya duk abunda yace ze faru to ba makawa saiya faru.

A fusace ya ɗaga mata hannu rai aɓace yafara magana"haba mariya sauraramun da zance bokan nan mana haka tun dazu kin isheni da magana ɗaya waima in tambayeki mana"ina jinka ta amsa masa a daƙile.

"Shin da izinin wa kika ɗauki ƙafa zuwa wajen bokan?
Tambaya daya mata a bazata kame kame tasoma yi dan bata da amsa guda dazata bayar dan kare kanta ita kanta sai yanzu ta tuna da katoɓarar da tayi dan tun tuni Alhaji sunusi ya haneta da bin malamai ko bokaye acewar sa idan kishiya take tsoro shi bashi bayi mata ƙari sannan yara wanda ta haifa masa sun isheshi rayuwar duniya shisa suke cin duniyarsu da tsinke duk abunda tanema yimata yake wani abun ma saide kawai taga yasayo mata.

"To daga yau kika sake wanke kafa kikaje wajen wani boka kiyi kuka da kanki idan kinyi wasama ita ƙawar taki mai baki shawara zuwan zanyi muku katanga tsakanin ku,fuuuu yawuce ciki cike da fushi abu ya game masa goma da ishirin.

Suhail duk ya tashi hankalin sa dana ƴan gidan su baki ɗaya da rashin samun sahibar tasa a waya kwana biyu da beyi ba,kira dubu zema khalid amsar ɗayace ba tazo aiki ba koyaje gidan su besame su ba,ganin sa cikin damuwa ya tashi hankulan ahalin sa baki ɗaya musamman ummin sa,yanxun ma zaune yake wayansa riƙe a hannun sa kaman wanda ze ganta taciki ɗagowa yayi yace"Ummi kibani izini inason zuwa Nigeria a yau ɗin nan dan son ganin meyasame ta nasan haka kawai bazata kashe wayarta ba inma wayar tata tasamu matsalane ai dole zanji daga khalid tunda kullu yaumin sai taje aiki,kafin ummin tayi magana suhaiham
dake zaune dan nesa dashi ta taso tazo gaban sa tazube gwiwa a ƙasa tace"yanzu akhi dama duk saboda mace ka shiga wannan halin damuwar dan Allah faɗamun dame tafini,kyau ko asali naɓata lokacina akanka nakori duk wasu samarina masu sona da aure nace sai kai irin sakaiya da zakamun kenan kawai sai ta daura kanta saman cinyarsa tafashe da kuka saida tayi mai isarta sannan ta ɗago tariƙe masa hannu tace dan Allah kasoni ka kaunaceni koda kwata kwatancin sonda nake makane wallahi idan  kagujeni koka juyamun baya mutuwa zanyi kawai sai tari ya tsarƙe mata tasomayi ba kakkautawa take duka sukai kaita kira suke suhaima suhaima cikin tsananin tashin hankali ummi take kira ɗaukota muje asibita amma tuni tatafi luuuuuu sai tarota yayi sumamiya cikin tashin hankali ya ɗauketa da gudu yayi waje da ita sakata mota yayi Ummi tashiga ta daura kanta saman cinyarta sai hospital.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now