61

214 22 1
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 61

   Jujjuya ledan data tamiƙa masa yafara sai can yace"hajia gaskiya aikinki mai saukine sannan da wuya abunda yasa nace haka nide nawa zubawa ne kawai amma sakashi yaci wani abun ko yasha wannan badaga ni bane dan haka shine wuyan da nace,dole sai annemi wanda ze ja hankalin sa yaci abincin ko kuma yasha juice ɗin,shin kina da wanda ze aiwatar miki da wannan ko babu idan babu ko kinga xubawan asarace.

Saurin ƙatseshi tayi ta hanyan ɗaga masa hannu tace"banason jin an anbaci asara nan"to hajia ga shawara kice da amaryar tayi iya yinta dan ganin ta bashi koda juice ne yasha"shawara mai kyau tace dashi harta juya zata tafi sai kuma ta juyo tace dashi ka kula wajen zubawan kar wani yagani"baki da matsala inde wannan ne kede kiyi ƙoƙarin dan ganin yasha ko yaci wani abun shine kawai daga haka sukai sallama da cewa sai yajita.

Tana barin wajen daddy ishaq ya ƙwashe da dariya yaron sa kamilu ya matso kusa dashi yana cewa"oga da alama waƴan nan mutanen basuda imani haryanzu idan bacin haka yaushe asiri yake tasiri aiko yayi naɗan wani lokacine"ai kamalu basu sani ba kuma bazasu san kuskure da suke tabƙawa ba harsai ranan da reshe ya juye da mujiya tukun zasu sani,ai yanzu idona nakan duk wani motsin su kafin a gama wannan bikin ko zan samu nasaran ƙusawa cikin masarautar su ko kuma sai yayi shiru....."karka damu oga in sha Allah saikayi galaba a kansu wannan karon Allah yana tare da mai gaskiya yafaɗa cike da bashi gwarin gwiwa"hakane ya amsa yana komawa ciki.

Hajiya mariyah gaskiya keɗin gwaskace shiga irin wannan ƙatsurgumin dajin wallahi tunda muka tafi bansamu nutsuwa ba harsai da naga munshigo gari kuma cikin gida sannan naji hankalina ya kwanta,dariya sosai hajiya mariya tayi tana kallon hajia shema tace"ai bari shema nima kaina dayace mu fita a hankali karmu taka musu yara suna wasa wallahi karfin hali kawai nayi amma da kin lura lokacin zakiji yanda cikina yake ƙuji wallahi dariya suka kece dashi a tare sannan hajiya mariya ta kwalawa mai aikin ta kira ta kawo musu abinci da abun sha,saida sukaci sukai nak sannan suka daura sabon hira dakuma yanda zasu ɓullowa basma tabawa Ahmad koda juice ne yasha kada asamu matsala dan sanin halin basma da shashancin kartasa muyi zuwan banza.

"Kaman kin shiga zuciyana kin gani abunda nake tunani kenan nima shema tunda boka yabani maganin hanyan da zanbi nazuba masa a abinci nake ta tunani to wannan an wuce wajen dan fitan da nayi da muka shigo ai naje nasami wanda zemun wannan aikin ne saide shima ce mun yayi nashi mai saukine wanda zesa ya danci wani abu ko shan waje abun shine kawai.

Ɗan shiru sukai kaman masu tunanin wani abun sai can hajia shema tace"yauwa gawani shawara ki kira ita basman yanzu,ba musu kuwa hajia mariya ta dauki waya ta kira basma bugu daya biyu sannan aka ɗaga tunma kafin tayi magana tace"kisameni a ɗakina yanzu"to mummy kin dawone?"eh na dawo yi sauri kizo karki batan lokaci muna tare da mummynki shema kuma tafiya zatayi yanzu"tom mummy gani nan zuwa daga haka ta katse wayan tana kallon salaha tace"ina zuwa yanzu mummy nakira na daga haka tasa kai tafita daga dakin tabar ƙawayenta da mai makeup dasuka gayyato.

*********
Wow kinga yanda ƙunshin nan yamiki kyau kuwa?gaskiya na dade banga wanda gyara ya amshi jikinta ba farat ɗaya irin ki,takare faɗin haka fuska ƙunshe da murmushi.

Murmushin ita Aisha ta maida mata tace"kai hajia karki saka kaina ya kumbura naringa jina a sama,dariya tayi tana riƙe haɓa tace oh ƴar nan dan ma kinsamu na yaba to bani ba bari wanda yakawokin yazo dan nasan shima kansa sai yayaba yakuma karamun da tuƙwici dan wannan gyaran babbar harkace dukda yace keɗin ƙawarsace amma ba komai nasan ze yaba kuma dan Allah ko raran aurenki karki mance da nan kizo ko gayyatana kiyi har gida zanje namiki gyara na musamman na amare tsawon sati biyu zamuyi wallahi sai kinga yanda jikinki ze dawo tamkar balarabiya ai ingaya miki munan bama wasa wajen inganta aiyukanmu kayan mu masu ingancine dan daga sudan muke oder nasanma dole yallaɓe yayaba irin kyaun da kikayi"hajia kenan kita wani yayaba aiko be yababa ni nasan aikinki yayi tunda naji wasu ƴan canje canje ajikina ba karya.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now