53

148 15 0
                                    

O💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 53

  "To aiga irin tanan ana baka kana roƙa kai zaka iya batawa da kowa akansa dan farin cikin sa amma shikuma baze iya batawa dako ɗiyar da ya haifaba saboda farin cikinta na sama da kowa awajen sa,sai kakira Ahmad ɗin kaji ta bakin sa amma inde a haka zaku tafi bana tunanin wannan aure da kukeson kullawa zeyi tasiri dan shi Ahmad mutumne mai kafiya da tsayuwa kan magana ɗaya shikuma Alhaji sunusi mutumne daya fifita bukatarsa saman komai a duniya kai kuma bazaka iya ƙetare maganan shi ba kaga kuwa Ahmad dinne ze sha bakar wahala dan wannan yarinya bana tunanin ko ruwan zafi ta iya girkawa.

Ganin tagama maganan tana shirin miƙewa"koma ki zauna ina kuma zaki ikilima ai sai kitsaya ki saurareni tunda nima danake babba sama da ke natsaya na saurari ta bakinki,kawai de zance dake inde kisan da bakin ki ko dana ƴar uwaki Ahmad yasa Ahmad yin haka wallahi kuyi gaggawan cemasa ya janye daga kudirinsa yakuma dawo gida in kuma yayi wasa wallahi insa yau dinnan adaura masa aure da basma kowama ya huta.

Ƴar dariya Anty hajia tayi tace"yayah amma kanada abun dariya yo idan aure zaka daurawa Ahmad sai kazo ka nemi fada mana yo mume namu ciki,bakaga muda mukasan zafinsa dakuma sanin abunda ze faranta masa ai sai ji kawai kayi mundaura masa aure da wacce tafi dacewa da rayuwarsa wacce kai da kanka sai kazo kana alfahari da zamowarta surukarka.

"Oh ta haka kula ɓulo to bari kiji wallahi wallahi dande kun saka malam cikine badan haka ba da tuni nasaka ya rattaɓa mata saki ai ni ku yanzu wannan auren ban ɗaukesa aure ba auren wucin gadi kinsan abunda ake nufi da na wucin gadi to haka na daukesa lokaci ƙanƙani nake jira"Antyn yara aka kira daga bayansu tare suka juya jin muryar Ammi yasa Alh badamasi yin kicin kicin da fuska itama haɗe fuskarta tayi ba alamun wasa tace zoki wuce ki tafi gida mayi waya anjima.

HAJIA MARIYA
Ganin kukan na basma bana karewa bane tashiga rarrashinta harta samu ta shawo kanta tayi shiru ta faɗa mata damuwarta,murmushi tayi ta kamo hannun ta tariƙe tace"basma kefa ba yarinya bace karama haryanzu da komai sai daddynki yashige miki gaba sannan zaki samu.

Keko ƴar kissarnan ta ƴan matan zamani baki iya ba kice komai sai da izza zaki mallakeshi kisani wani abun karfin izza data mulki kuɗinki shi zesa ki mallakesa ba, wani abun saida ƙaskan da kai sannan ne ze kaiki ga samun abunda kikeso.

Yanzu duba kigani da kinje masa da lallami da tausassan kalma da yanzu kinsami biyan bukata amma kinje kinyi masa wannan haukan naki taya ze saurara miki shin baki taɓa jin shikansa daddyn naki yana faɗi a harka ta kasuwanci babu sani ba sabo ba,yanzu gashi kinge kinsaka daddynki ciki ƙila yace koda karfin kuɗi saiya samo miki wannan riga saboda farin cikin ki amma shi Ahmad ɗin naki kinɓata masa.....shiru tayi tana sauraron mummyn tata a can karkashin ranta kuwa tunani take yaushe mummynta tazama haka take magana cikin sanyi.

Ganin kaman tana tunani yasa mummynta dan tabata kamanko tasan abunda take magana aranta tace"kinga bar wahalar da kanki sai kinsan komai kibar komai yanda kika gansa yanzu de tashi kishaga kisamu kiyi wanka ki kira Ahmad ɗin a waya ƙila yasauko daga fushin da yayi ki kalallamesa karkuma ki dauko masa zance rigan mude samu yasauko da fushin tukunna musan abunyi da haka tasamu ta korata ɗaki ita kuma ta zauna zaman jiran Alhajin nata.

Aisha koda tashiga ciki wanka tasamu tayi hankali kwance,tafito bedroom dinta daure da towel saida ta tsane danshin ruwan jikinta sannan ta zauna zaman shafa jikinta da lotion masu kyau da daɗin kamshi tana gama shafa man ta jawo turaruka ta feshe jikinta dashi light makeup tayi sai kawai taji aranta ranason saka wannan rigan kai sai ta jawo abarta tasa tashiga juyi a gaban mirrow ita kaɗai sa sakin murmushi take kawai sai dauko wayanta da kasheta ta ajiye tun kwanaki takunna saida ta gama searching sannan tashiga camera tasoma haska kanta da hotuna saida tayi mai isarta sannan ta tsagaita abunda bata taɓa yiba daura hoto a media shine yau tayi na musamman amma a IG dan nan sukafi ɗaura tallan kayansu idan sunyi sabbin styles imoji tasa daidai kan fuskarta sannan tayi rubutu kaman haka dayaja hankulan mutane musamman matasa ƴan uwanta masu sana'ar dinki.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now