87

149 18 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTERS FORUM* ✨

      ✨ *G.W.F* ✨

CHAPTER 87

"Take it easy Oga za musan yanda zamuyi mu nemo su batare da sun bamu matsala ba.yakare maganan cikin kwantar da murya.

Cike da fushi ya kalle shi jikin sa duk tsuma yake saboda tsananin tashin hankali dayake ciki dan shi kaɗai yasan halin da yake ciki na tashin hankali dakuma asara dayake gani tana neman kunno masa kai cikin al'amuran sa.

"Wai meke shirin faruwa danine?komai nawa yana neman lalacewa kai ina bazeyu ba,banfa tsaɓa dokan da Boka ya jindaya mun koda sau ɗaya ba,amma me nake shirin gani haka?yasake faɗa da karfi yana dunƙule hannun sa ɗaya yakaima  ɗaya hannun nasa naushi,Ya..ya..ya.yashiga faɗi yanason kiran sunan Allah amma yayi harshen sa yamasa nauyi yakasa kiran  kawai saiya dafe kansa dake neman rabewa gida biyu yakira sunan Idon mikiya"Na'am Oga ya amsa yana rissinawa dan yaga yau Ogan nasa kaman baya cikin hayyacin sa.

"Inaso duk yanda zakayi kayi kai idan takama ko kisane ayi muddin zaku samu kuɓutar dasu Garzali ku dawo mun su nan.kallon sa Idon mikiya yayi yace"ran Oga yadaɗe idan kuma su suka shirya hakan da kansu dan su gudu fa?ya faɗa yana tsare sa da Ido.

Shiru Alhaji Sunusi yayi dan shi beyi kawo wannan tunanin ransa ba,kwata kwata wannan tunanin bezo masa ba,dan haka kawai yace idan su kuka kama da alhakin wannan aika aikan tabbas jininsu ya halasata gareni.

Alhaji na Allah tunda Mami tafita ta barsa dan yayi wanka,yana gama wayan da yayi ya ajiye wayan saman gado kenan fuskar Aisha ta faɗo masa kaman majigii yake kallon ta tarr .

taya hakan xeyu?Yaro daya ɗauke shi kaman Uba Mahaifi ace ƴar manuniyar tsafin su yanuna masa matar sa,kai ina ade sake duba wannan lamarin yafaɗa cikin ransa,dan shi tunɗazu dayayi tozali da yarinyar yaji tsigar jikin sa duka ya mimmiƙe ashe da walaƙin.

Dan haka meetin din gaggawa ya buiata ta hanyan yin magana ta wani madubin sihiri dake ɗakin duk wani ɗan ƙungiya dole ya hallara a wajen wanda yake da nisa ko tafiya ta kamashi zuwa wata ƙasar kuma zeyi amfanine da madubin sa ayi meetin ɗin dashi dan ze iya ganin duka abunda akeyi ta madubin sa.

A daddafe yashirya a fito suka ci abinci bayan sun gama yazo falo ya zauna nan ya jawo wata ƙatuwar a kwati daya zo da ita yashiga bawa kowa tsarabar sa harda Aisha da Ahmad saida ya ciro musu cikin kayan da yasiyowa Sajid Aisha kuma cikin wanda yasiyoma Fauza tayi ta masifa tana ta kumbure kumburen fuska da kyarde ta hakura,ta kwashi sauran kayan tayi ɗakin ta dashi itama baby safna ɗaukan nata tsarabar tayi da ƙatuwar teddy dinta mai kyaun gaske tayi ɗakin ta dashi tana cewa gobe zata nunawa Anty Sajida da Anty Aisha,bayan duka sun bar falon ya rage daga Mami sai shi hankalin sa yana kan Tv da ake labaran ƙasa yace "kamata yayi kije kikai musu kayan nan sai kuma ki taso Yarinyar gaba tazo nan din ta kwana cikin.masu aiki ko?

"Narke masa tayi kaman wata ƙaramar yarinya tace"bara nakira Ahmad din ta waya ta haɗo kayan tazo,ta kare maganan tana ɗaukan waya zata kira Ahmad katseta yayi dacewa"haba hajia ai komai yinsa ake da lissafi me yasa ke sam baki dashine?eh madadin  kitashi kije da kanki sai ki zauna kina kiran wata aba wai waya,kuma kinfi kowa sanin waye Ahmad wajen kafi da taurin kai ƙila idan yaga cikin idon ki zefi barin ta.

"Kaga kuma banyi wannan tunanin ba,niko nasan waye Ahmad mutumin da kunama tasare shi amma ko motsi beyi ba sai zufa daya muka gani yana tsassafo masane Hajia ma'arufa ta ankara da yanayin sa dakuma canji da tagani tattare dashi fa muka shiga dubawa muka ganin shi damƙe da kunamar a hannun sa ashe wai kunamarce take neman ta harɓi Uwar tashi shine shi kwamma shi da ita,wannan magana danake faɗama tunfa yana yaro matashi,wallahi Alhaji tunda nake ban taɓa ganin yaro dayake son Iyayen sa kaman shi ba.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now