62

200 21 1
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 62

  Masha Allahu walaƙuwata ubangiji yayi halitta anan besan sanda ya furta hakan a fili ba,yana nan tsaye de har suka zo Aisha ta gaida khalid ya amsa yana zolayarta da cewa"kode gasan kyau zaki bamu sani ba ƙanwas murmushi kawai ta sakar masa tana jan hannun Anty malika dake tsaye saida suka dan gilmashi sannan khalid dake tsaye yana kallon sa yaɗan bigi saman motar da karfi nan Ahmad yayi firgigit yadawo daga duniyar tunani daya tafi sake kallon hanyan babban shagon yayi hajiya hanas din yayi murmushi hajia hanas dake tsaye a gaban sa ta sakar masa dole ya maida mata da murmushi yaƙe ganin yanda yake dan kalle kalle yasata cewa"gasu can sun wuce.

Wayancewa yayi yana cewa"oh na gansu bani acct dinki,ba musu ta karanto masa yasaka nan take sai ga alart zaro ido hajia hanas tayi cike da jin daɗi irin wannan kyautan hakan yasake tabbar mata dacewa lalle aikinta yayi kyau kuma wanda akai domin sa yayaba,dama ance yaba kyauta tukuwici gashi kuwa tagani godiya tashiga yi masa har tana haɗawa da khalid cewan yata yata godiya wajen Alhaji sannan ta juya baya tanasake jaddada masa duk sanda madam takeda bukatar gyaran jiki lalle ko wankin gashi dama ƙitso ko waya kawai yayi ba matsala ko gidane zaje aimata godiya yayi mata ta koma cikin shagon ta cike da murna irin wannan kyauta da tasamu.

Shiko Ahmad ganin yanda khalid ya tsastsare sa da ido yana ƴar dariya ƙasa ƙasa yasake haɗe fuska shi ala dole bayason wargi yace"me kawani tsareni da ido kaman zaka haɗiyeni?

khalid besan sanda wata irin dariya da karfi ya kubce masa ba ganin raina masa hankali Ahmad kesonyi kaman bashine yanzu yagama kallon yarinya dayake kiran Auren wucin gadi yayi da ita ba.

"To malam me nawani haɗa rai ai sai kaje kakira ta mutafi kasan tun tuni su faisal na can mu kaɗai suke jira amma mutum kawani sake baki kana kallon gwailan yariyan da banaji ko ƙirgen dangi ta gama kaida za kawo maka classic lady me nawa westin time kan wannan abar yakare magana yana ɗauke kansa daga kallon inda Aisha da malika ke tsaye jikin motar malika kuma yayi hakan ne kawai dan son kunno da abokin nasa ai kuwa ya kunno,dan wani irin tuƙuƙin bakin cikine ya turniƙe masa zuciya besan sanda yayi kwafa yana ce masa to me zan gani anan ɗin karkaga dan nakawo ta nan anyi mata ƙunshi kadauka wani abunne wannan din hakkine akaina banason ana taron baki yazama itace kaɗai batayi ba,yana kare fadin haka ya yafito malika da hannu shikuma fuuu yakoma cikin mota duk takaici yagama isar sa yama rasa abunda ke masa daɗi khalid ma ya kalle ta haka ina ga wasu kenan haka ake kallonta ji kawai yayi kaman yafasa ma tafiyan da ita wajen yace da malika kawai su koma gida,amma kuma idan ta koma shirin sa ze rushe haka ya danne zuciyar sa.

Malika na isowa yace"jeki kirawota kinsan koma amma kinason ɓatamun rai"yi hakuri bro wallahi tun ɗazu nake fama da ita amma ta kafe bazata wajen wani party da wannan shigar haka ba saide a nema mata hijabi.

Besan sanda yaja wani gajeran tsuka mtsss yana cewa"matsalata da irin waƴannan yaran kenan rashin wayewa to wama ze kalleta a wajen idan munje ana ta manyan mata wake ta gwaila irin dallah malama kizo karki batan lokaci,yanda yayi magana har saida yabasu dariya amma duka suka waske basuyi ba,sai ma khalid ne yace"bara na taimaka maka da wannan yanufi bakin motar malika yasami Aisha tsaye yace"ƙanwas kefa muke jira tuntuni kuma kinzo kin tsaya anan,marairaice fuska tayi tace"wallahi yaya khalid banajin zuwa wajen partyn ne haka"ina ina kanwas saide fa yau ɗaya kiyi hakuri yah faisal ma yace yana jiranki a can gakuma kawarki laila ita tana bakin hanya tana jiran muje madauke ta dan haka kiyi hakuri keɗin kibi motan Ahmad kuje tare nikuma da malika zamu biya ta inda laila ke jiranmu muɗauke ta"amma yah khalid i zamu iya zuwa tare mu dauketa ko?"naa ba zauyu muje dukkan mu mubar ba kede muje kawai kutafi muma gamunan tafe.

Haka Aisha ta hakura zatabi motan Ahmad amma badan saboda tanaso ba dande kawai karta kafe khalid yagani kaman taƙi jin maganar sa ne,har bakin motan ya rakota saida yabude mata gidan gaba tashiga ta zauna khalid harda gyara mata riga saboda tsokala ai kuwa ya tsokalo dan yana ɗagowa yasamu guzurin mugun kallo daga oga Ahmad dake tsaye murmushi yasakar masa dacewa a kular mana da ƙanwa banda tuƙin ganganci dan naga kaman ka haura sama"dallah malam ware kukesa kananun yara suna raina mutane surinƙa ganin kansu daya dakai dakayi magana,dariya khalid yayi malika natayasa duk da tana ɓoye dariyar tata kar yayan nata yagani amma abun ya gagara dan saida dariyar ta fito fili,daƙyar ta danne dariyar tana cewa"yaya in banda abunka ai koda ƙwana daya ka girmi mutum ai ka girme sane balle kaida kaba da shekaru shima yah khalid ɗin yafaɗi hakane kawai dan ya tsokaleka kuma kai kanka kasani har abada ba raini tsakanin mu dakai wallahi ko ita Aishan ma banajin zatayi tunda ba halinta bane,wayan Ahmad ne tayi ringin wannan shine kiran da faisal yamasa na biyar kenan tunda sukazo daukar su Aisha ɗaga wayan yayi yana cewa to malam sauri ba wajen zuwa gamu nan yanzun nan na daukota kasan sha'anin mata komai ƙanƙantar mace wajen wanka kadai sai taɓata a ƙalla minti talati wajen shafa mai ma haka sannan wajen kwalliya wannaan itace uwa uba dan sai taɓata awa guda sannan......"yaushe kazama haka Ahmad faisal ne ya katse shi dafadin hakan murmushin gefen baki Ahmad yayi yana maikafe Aisha dake zaune a mota da ido duk da kallon gefen ido yake binta dashi sai kawai yakashe wayan yana maida abun sa cikin aljuhu shima yashiga motan ya zauna saida yamata key yabata wuta sannan ya cillata saman kwalta dama tuni khalid sun tafi da motar malika tunda yasa Aisha a motar Ahmad ya anshi key daga hannun malikan bayan yagama tsokalan Ahmad yatafi.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now