84

187 21 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTERS FORUM* ✨

     ✨G.W.F✨

CHAPTER 84

Tana mikewa daga inda ta duƙa Mami na bude kofar ɗakin a ruɗe take kallon ta,ita ma kallon nata tayi ganin ta kaman a ruɗe yasata tasake kallon ta tace"wai ke lafiya duk kinbi kin ruɗe kaman wacce aka kama tana aikata mummunan abu?

Aisha ki nutsu karki bada kanki ƙila Allah yanason ya warware wani ƙulli ne yakawo ki  nan ɗin ki nutsu ki iya takunki karki bari a zargeki idan kika bari ta gano wani abun lalle kin kufsa.

Tana yin wannan tunanin ta miƙe tana gyara tsayuwarta ta ɗaga kanta sama tare da aro jarumta tayafawa kanta tace"eh nagama ne ki duba kigani koda wani abun da zanyi miki?

Kallon ta Mami tayi mai cike da tuhuma saida ta mata kallon kusan daƙiƙa goma tana nazarin ta sannan ta ɗauke kanta daga kallon ta nata tana kuma hana zuciyarta zargin ta tace"anƴa kina da gaskiya inma wani abun kikayi zan gani ne dan nan ɗakin tako ina akwai cctv camera,kirjintane taji ya bada sautin daamm amma saboda karta ba budewa hanyan zargi a kanta cikin nutsuwa dayin kasa da kanta tace"inde wannan ne Mami baki da matsala dani dan ni abunda kika sakani kawai nayi.

"Kina iya tafiya tace da ita tana maida duban ta ga ɗakin yasha gyara dan kaf ma'aikatan da suke masu gyara ba taɓa yima ɗakin gyara irin na yau ba.

Raɓawa tayi zata wuce ta gefen ta ta tsinkayi muryarta mai cike da izzar nan nacewa da ita"ki wuce can kitchen kitaya su aiki dan nan ba gidan hutu kika zo ba karkiyi tsammanin Ahmad mallakin kine ki sakankance zan barki da shine zuwa na ɗan wani lokacin,ki kaddara zaman ki dashi na wucin gadine Fauza itace ma mallakiyar shi ba ke ba.

sake yin ƙasa tayi da kanta batare da tace da ita komai ba,ta wuce zuwa can kitchen ɗin da tace tana samu tafita daga falon mai gidan wani numfashi ta sauke mai karfi cikin ranta kuwa mamaki take mai yakawo waƴan nan takardu mai ɗauke da sunan Mahaifin ta nan.

Me haɗin mai gidan da mahaifin ta?

Wace alaqa ce ke tsakanin su?

Dan da gani waƴan nan takardu duk da kallon tsoro tayi musu kaman na wasu kaddarorin sane da aka canza aka sabuntasu ya ilahil alamina ka kawo mun ɗauke.

Ga tambayoyi nan fal a ranta saide ba wanda zata faɗawa ko tambaya tasamu amsa daidai da tambayar tata a nan ɗin.

Tsuƙa tayi daidai tana shiga kitchen ɗin wai ma wani tsautsayine yasana nabiyo wannan mutumin.

Ai ba cikin hayyacin ki kika biyoshi ba wata zuciya ta bata amsa.

Ahmad kuwa yana fita a gida airport ya tafi saida ya yanki tiket ɗin tafiya sannan yakira su ƴan term dinna sa ta waya ba  tare daya faɗa musu ainihin inda zasuje ba,kawai ce musu yayi susa mesa a airport nan da minti talatin Mansur kasan banson deley"yes sir yace yana kashe wayan yakira Bk da mahmud sai kasim su dinma koda suka tambaye shi ina zasuje"ni ma bansan inda zamu ba,yade kirani a waya yace musame shi a airport nan da 30mt kawai,rufe computer dake gaban shi yayi yana miƙewa tsaye yazari car key dinsa dake saman desk yakai duban sa kan abokan nashi yace"guy's muje ko?

Bk ne ya amsa da cewa eh Mansur ya kai kallo sa kan sauran abokan tafiyan nasu yana cewa to me muke jira ai gwara muyi sauri dan kada mu tsaɓa lokaci kunfi kowa sanin sabon Oga bayason jira ko african time,kuma fa hakane suka amsa su duka a tare suna miƙewa suka fita ba wanda yasan ga inda zasu,dan ko Oga kwata kwata basu faɗawa ba balle sauran yaku bayi.

Isarsu airport keda wuya aka soma kiran matafiya ticket yamikawa kowa nasa sannan yace da Mansur"ka karɓi wayan hannu su ka haɗa danaka duka kazuba anan.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now