60

206 10 0
                                    

💕 *AURE WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 60

Zaro idonta tayi kaman zasu faɗo ƙasa tasoma wutsul wutsul da kafanta ba bakin magana saboda rufe mata bakinta da yayi da tafin hannun sa ɗaya sai"um um um kawai ta iya cewa.

Falo yanufa da ita a hakan daga ita sai ƴar riga mara nauyi da tasa na shan iska"me zan gani haka ni ikilima yau sauke mun ƴa Anty hajia ke magana daidai shigowan sa falon ɗauke da ita kaman wata ƴar tsana.

Kusan duka waƴanda suke zaune a falon miƙewa tsaye sukai idan kacire yah faisal da kallo ɗaya yamasa yacigaba da aikin da yake a systerm din da ke saman cikinyan sa fuska ƙunshe da murmushi.

"A'a Anty hajia dan Allah karki tsaidani taurin kai takeson yimun idan bata bini a hankali ba wallahi fitan da zanyi da ita ta tafi kenan wai kaman ni zan bata umurni amma yarinyar nan saboda taurin kai ko motsawa batayi daga inda take zaune ba,almost 30mnt nabata dan ta ƙimtsa amma tayi kunnen uwar shegu da maganana"to naji yanzu de sauketa yi hakuri ta fada tana nufosa dole yasa yadireta badan yaso ba,sake tamke fuska yayi yana kallon wani direction ɗin yace"hijabi kawai zata ɗauka tazo mutafi kokuma...."a'a bazayi haka ba ta dakatar dashi dafaɗin haka yanzu de dan barmun ita tayi koda breakfast ne.

"Ai taƙoshi kuma anty hajia idan ba abunki ba ina kika taɓa ganin ango bayar amaryar sa da yunwa ai tattaleta zanyi ai gwara ni na zauna da yunwa da in barta dashi ki yarda dani yakare maganan cike da zolaya.

Sannan ya ɗan kalli faisal da khalid dake tsaye ƙiƙam kaman dogari yace bros anjima around 8 zaku rakani wajen taron wancan yarinyar,baki sake suka bisa da kallo"wace yarinya?

Khalid yayi karfin halin tambayan sa duk da yafahinci wa yake nufi amma yaga tunda suka fara shagalin su ba wanda ya hallarta"daddy yakira yanzu yake tamun faɗa dan nace bazani ba yasake faɗin haka da damuwa kwance saman fuskan sa.

Ke malika ki haɗo mun da kayan da zata canza kuma na gayyace ku dasu umma salma gaba ɗayanku kuje,murmushi faisal yayi ya ajiye aikin da yake gefe sannan yace"kai akeson gani ba wasu tarin yara akeson gani ba har kana wani gayyato su auta kaide kawai zamu maka rakiya dan fidda kai kunya gani ga khalid sai nawwar zan kira dr sapwan a waya anjima inaga mun wadatar ko?kai kawai ya gyada masa.

Amma zancen wayannan yaran barsu a gefe sannan ita Aisha kabarta su tafi da malika tunda....saurin katsesa yayi da fadin nine zan kaita ai taƙi tafiya dasu malikan tun tuni yana gama mafadin haka yaja hannunta tana turjewa tana me yafita da ita,saida yasata mota ta zauna ya kullo ƙafar sannan shima yaxaga yashiga ta ɓangaren driver yaja suka fita daga gidan dan duk yanda Anty hajia taso sutafi da malika tare ƙi yayi daga karshema sai ce mata yayi wai anti hajia tsoron me kike?nagade matatace ina da hakkin keɓewa da ita da sauri anty hajia tashiga tattaɓa kunnenta da hannu tana cewa"kaide baka da kunya sai ku tafi amma ka maidomun da ƴa da wuri dan bazan lamunci...."haba anty hajia ki barsu su tafi kina ɓata musu lokaci cewa malika dake zaune tana daddana waya wani irin harara Aisha ta zabga mata ganin kaman tana sake zugashi.

Tunda motan yafita daga cikin gidan ya hau saman titi kawai sai taji hankalinta ya tashi tashiga rera masa kuka duk yanda yaso basarwa kasayin hakan yayi dan jin kukan nata yake harkasan ransa,samun gefen kwalta yayi ya faka motan ya juya ya kalleta fuskar nan tasa tamƙe kaman hadarin gabas yace"idan baki rufemun bakin kindena wannan ɗan iskan kukan bako to wallahi tafiya da zanyi dake kin tare kenan har sai randa zamanki na wucin gadin ya kare sannan zan maidoki,mukut ta haɗiyi wani abu mai kauri tashiga kunkuni yasanta da tsiwa dakuma rashin tsoro maidawa mutum martani inde abu beyimata ba,tada motan sa yayi yasoma tafiya sai ya tsinkayi muryanta cikin kuka tana cewa"ai wannan zaluncine auren rashin gata dan kawai anga iyayena basa raye har kana wani ikirari da cewa auren wucin gadi zakai dani dan kawai anga bani da gata saboda rashin sanin darajan mace,jin yanda ta taƙarƙare sai zuba take yasashi dakatar da ita ta hanya cemata"ba gwara ni ba ko banza kina kasarki ta gado kuma ai zaman namu naɗan wani lokacine da zaran nasamu abunda nake nema kinga sai nasallameki kikoma ga wanda kikeso kafin sannan kinyi girman da zaki iya rayuwa koma a inane,amma da yanxu na bari mai jan kunnen nan ya aureki kinga nafarko barin ƙasar zeyi dake sannan abu na biyu ba lalle ƴan uwansa su amsheki matsayin surukuwa ba saboda bambancin launin fata,gani nayima taimakonki nayi tunda banbijire wa Ammina ba na amince da aurenki na amsa ai godemun yakamata kiyi.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now