57

175 17 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 57

NAGODE DA ADDUO'IN KU GARENI MASU KIRANA TA WAYA KAI TSAYE DA MASU TURA SAKON KARTAKWANA DAKUMA MASU YIMUN MGN TA WHTAPP ALHAMDULLAHI NAJI SAUKI ALLAH YABAR KAUNA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA

   Suna gama wayan ta sauke jiki a sanyaye take sanar dasu abunda ke faruwa da mijin yayar tata kowa dake wajen sai da jikinsa yayi sanyi kuma sun kaɗu dajin wai cid aka jedashi wannan yana nufi da cewa case ɗin ba karami case baneba tunda harda su cid aciki"Anty hajia ko zaki kira yah faisal ki sanar dashi abunda yake faruwa cewar Aisha"nima abunda nake son cewa kenan kika rigani inji malika.

Koda Anty hajiya takira wayan faisal cemata yayi yanzu haka suna cid office shida Ahmad amma bawani feedback tunda aka shiga dashi ciki kuma sunnemi ganawa da manya amma babasu wannan daman ba ajiyar xuciya ta sauke kana tace"karka bar ɗan uwanka shi kaɗai katsaya dashi dan ganinka tare dashi ze bashi kwarin gwiwa,amsa mata yayi da In shaa Allah Anty hajia bazan taɓa barin sa shi kaɗai ba duk yanda ake ciki zan kasance dashi,daga haka yakashe wayan.

Yana ɗan kallon Ahmad dayake waya da commissioner ƴan sanda dayake mutumin daddyn sane amma sai ce masa yayi"Ahmad kayi hakuri sannan kuyi ta addu'a ba abunda zan iya yimaku dan case ɗin na Alhaji babban case ne akwai kuma lauje cikin naɗin daga haka ya kashe wayansa yana mai bawa Ahmad din hakuri.

Shiru Ahmad yayi idanun nan nasa sun kaɗa sunyi jajur jijiyoyin kansa sun tashi rudu rudu saboda ɓacin rai,bakin nan nasa yabushe kai kace yashekara besha ruwa ba,case din Alhaji akwai lauje cikin naɗin shine abunda yake ta maimaitawa waye?
Waye wayake son ganin yaɓatawa mahaifinsa suna tawannan hanyan waya zaɓi ɓatasu a idon duniya ta wannan lalle maishi koma wanene yayi babban kuskure.

Dafashi faisal yayi dan ganin yanda yake kai komo yana maganganu yace"lafiya?
Girgiza masa kai yayi sannan ya labarta masa yanda sukai da commissioner shiru faisal yayi sai can ya dago yana kallon Ahmad yace"kai me kafahinta anan?"babu saide inason fahintane dan wallahi nagano koma wanene yakeson jafa daddyna cikin wannan mawuyacin halin saina kasheshi da hannuna yakare magana a fusace.

Murmushi faisal yayi yadaura da cemasa dadina dakai saurin fushi amma katsaya kayi tunani a tsanake zero sai shegen zuciyar banza data wofi yanzu kai baka tunanin da saka hannun wasu ko wani shin baka zargin wani cikin wannan abun?

Shiru sukai duka kaman masu tunano wani abu sai can Ahmad ya dago yana kallon faisal ɗin yace"gaskiya bana zargin idan ma zan zargi wani to Alh sunusi ne amma fa ko shiɗinma bana tsammanin zai ɓatawa daddyna suna ko dan saboda abotansu.

"Hmmm bro kenan irin su Alh sunusi zasu iyayin komai saboda biyan buƙatar kansu yanzu de abu ɗaya nakeson kaimun dan son samun bakin zaren ni kuma zanyi aiki da ƙwarewata dan ganin mun kama duk wani mai hannu cikin wannan case din amma da sharadi"wace irin sharaɗi fadi koma wacece zanyi dan ganin anyi released daddyna kuma an wankeshi a idon duniya.

Gyaɗa kai faisal yayi cike da gamsuwa yace"yanzu de ɗauki wayanka kakira shi Alh sunusi kace ka amince da auren basma dama tsarinsu na tarewarka gidan sa,kallon baka da hankali ahmad yamasa eh ta nan kaɗai zamu samu kama masu lefin a hannu da shi Alh sunusi shike sarrafa cocaine a company ta Al hakk bincikemun yanuna shike amfani da mazuban capsule dakuma tambarin Al hakk ɗin waje guda suka ware suna wannan aikin a binciken da mukai saide bamu da ƙwakƙwaran hujja dazamu gabatar koda mun kamashi.

Cike da gamsuwa ya gyaɗa kansa cemasa zakayi yanzu ga halin da daddayn ka ke ciki kana neman alfarman a ɗan ɗage auren zuwa lokacin da zaa saki daddynka idan zargina akansa daidaine to dazaran yaji haka zaka ganshi ya dawo nan kuma ze tsaya tsayin daka dan ganin yafito da daddy yau din nan tunda yasan manya sosai.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now