69

171 18 1
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 69

    Saurin duƙawa ƙasa Aisha tayi ya yinda xuciyar Basma yashiga dukan tara tara dan yafi karfin akira shi da uku uku dan tariga da ta saddakar ƙwalbar Aisha zata ɗauko tatona mata asiri saide ga mamakin ta sai ganin Aisha tayi duƙe gabanta tana mai bata hakuri ɓoyayyen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta maida dubanta kan Aisha dake duƙe a gabanta cike da ƙaskanci take kallon Aishan nan ta tuna da maganasu da boka.

Kina nan zata zo tabaki hakuri daga nan kiwuce kai tsaye wajen angon naki dan ai watar da aikin da muka baki yanzu haka yana zaune a office din sa yana tunanin wata yarinya da ban bake ba.
"Kan bala boka wacce asararrarce takeson shiga gonata?"shine bamu sani ba dan bama ganin abunda cikin zuciyar mutum shikuma wannan zuciyar sa arufe take ruf,har wani irin huci take naɓacin rai tasake cewa"ita kuma yarinyar da nazo amun aiki akanta fa?da wani mahaukacin dariya boka ya kece wanda saida dajin ya'amsa  amon dariyar nasa daya wage wagegen bakin sa dayake fidda wani irin ɗoyin wari saida tsagaita dayin dariyar ya kalle ta yace"itama yanzu haka mun tura aljani ɗan tsaiko kuma a namu ɓan garen zamu turnzura miki ita yarinyar a duk inda take zata biyoki ta baki hakuri nan ke kuma zakiyi amfani da daman wajen juyata yanda kike so kirama abunda tamiki saide ki kiyaye abu ɗaya shine duk sanda zakiyi amfani da maganin mu ba kiran sunan Allah dan duk wanda yaxo wajenmu ɓatatcene wanda yariga yakwashe kayan sa gaban ma'aiki sannan kiyi ƙoƙarin gano mai ke tsakanin ta da shi mijin da zai auraki idan kika gano sai kizo ayi musu farraƙu ta yanda zamu raba tsakanin su rabuwa ta har abada.

Basma tare suka je office ɗin Ahmad da salaha sunko taki sa'a yana ciki,tun daga bakin ƙofar shiga office ɗin ta ciro wani ɗan ƙaramin ƙwalba acikin jakarta ta shiga shafa wani abu mai kama da turare a fuska sau uku kaman yanda bokan yace mata kuma shafarwa da zatayi ba duka face din bane a'a cross zata zana dan haka cikin sauri tayi sannan suka shiga ciki.

Cikin son nuna isa da son nuna ita watace tana yatsine face da bintse baki tace"zan hakura amma da sharaɗi,da sauri Aisha ta amsa da"wani irin sharaɗi?dazaki zauna dani a gidan mu har tsawon wata biyu bayan aurena zaki zamemun ƴar aiki idan kin yarda da hakan to kuwa tabbas zan tafe miki zan kuma yin miki kyauta mafi daraja"zan duba yuwuwar hakan gareni,cewar Aisha tana fadin haka tajuya zata fita batare da takalli ko inda Ahmad ɗin ke tsaye yana ta kallon ta a mamakance ikon Allah waime kedamun yarinyar nan ne yafiɗi haka a ransa yafi aƙirga.

Alhaji badamasi komawarsa gida kenan daga dubiyar Anty hajia zuciyar sa sai tafarfasa yake ga miki da sa'insa dasukai da Ammi duk haushinsu yakeji yana nan zaune a falo maigadi yayi sallama yashigo ya duƙa ya gaida dashi amsawa yayi yana kafesa da ido yace"Alhaji dama wasune sukazo suna son magana da kai,dan shiru yayi sai kuma yace"cene musu sushigo,mikewa maigadin yayi yama mutanen iso har bakin kofan shiga falon sannan yajuya bakin aikin sa,da sallama suka shiga amsa musu sallaman Alh badamasi yayi yana cewa"bismillah ganan waje ku zauna.

Bamusu suka zauna bayan sun gaisa ne yane yake kallon su cike da rashin sani ɗaya daga cikin su biyun yace"Alhaji baka ganemu ba ko?'eh wallahi kallon da nake muku kenan kaman naso ganeku kaman kuma ban taɓa ganin kuba,"eh kwarai tayu kasanmun miƙa masa wani farar takarda dake linke yayi yace"daga kotu muke wannan sammacine kallon su Alh badamasi yake a razane yanda yarazanan nan da a tsaye yake da tabbas daya fadi kasa sa'ansa guda a zaune yake,take wani irin zufa ya karyo masa,sabida tsaban rudewa da yayi ko sunan Allah ne yakasa ambata hannu yakai ya dauki ruwa dake a jiye cikin juk dake saman wani ɗan karamin table yakafa bakin sa a juk ɗin saida yasha kusan rabi sannan ya maida juk din a jiye gaban rigan sa duka yajiƙe da ruwa,kana ganinsa kasan duka a ruɗe yake ganin yanda yaruɗe ɗayan daga cikin su biyun yace"yi hakuri Alhaji bafa komai bane idan kana da gaskiyanka ko ina aka kaika gaskiyanka shin ze ƙwaceka kaide kawai abunda zance dakai karka ɓoye komai abunda kasani kuma karka zama mai magana biyu duk tambaya da zamaka kasa nutsuwa a ranka kafin ka amsa tambaya da zamaka wannan gudumawa nane daga haka sukai masa sallama suka tafi duk magana da mutumin yake masa ba abunda daya fahinta abun yake iya ganewa illa kalman sammaci saboda tsaban tsoro da ruɗewa ko takardan kasa budewa yayi yagani balle yasan ko akan me ake tuhumasa.

Da sauri Ahmad yamara mata baya ganin tamaƙe bata ko kalle saba balle yasa ran zata masa magana saima wani abu datake kaman drama wa basma shi abun natama daure masa kai yayi"ina tashiga kwana biyu ta barsu da zullumin wani hali take ciki suna yawon nemanta tun fitowar rana idan sun fita sai fadiwarta suke dawowa gida tunda ta ɓatan nan yau kwana biyu ko ruwa bayajin yasha ya tsargemasa ciki baccin sama ragaggene ga anty hajia na kwance ba lafiya amm.....tunanin sa ya katsane ganin ta nufi bakin get gadan gadan ba tare da ttama kula kowa ba.

"Hajia mariyah kishirya na kaiki wajen malamin gangare neman taimako nasan kuma zeyin dan kinsan aikin sa kaman yanka wuka yake,hmmm hakane hajia bilki shiyasa nake yinki dan baki taɓa bani shawaran banji daɗin sa ba,yanzu zamu ko?"eh idan akwai dumus a hannunki ai muje kawai kinsa ance abari yahuce shike kawo rabon wani gwara de kawai muje yanzu dan a wuce wajen.

Hajia shema tace"tom nide balki zan koma gida kinsan yau nike da Alhji kwara naje dawuri"gaskiya kan ki kasa ki tsare kodan saboda wannan munafukar kishiya taki"ai kede bari ina ganin barukanci kala kala wajen wannan figigiyar matan"kice har yanzu kina fama?"ai saima abunda yaƙaru mariyah kwanaki fa harni Alh yakalli tsaban idona yake cewa wai in saida masa da kwanana zaije gunta dan tafini daɗi,zaro idanunsu sukai dukkan su suna haɗa baki wajen cewa"me
"Eh"kuma kika sayar din?lalle balki ashe bakisan wace shema ba kawai cemasa nayi idan maɗacice ni haka zayi idan yaso ranar girkin ta taje yasha zuma amma bazan sayar ma ƴar iskar nan kwanana ba.

Dariya suka kwashe a tare suna shewa tare da tafawa kai kace yarane yan sweet sixteen saida suka shirya zasu fita sannan hajia mariya takira Alh sunusu a waya yana dauka tace zasu fita dasu hajia balki zata karbo sako sai kin dawo kawai yace yakashe wayan sa.

Aisha na gaf da zata fita bakin get Ahmad ya cimmata yana zuwa yasa hannu yariko hannunta ɗaya"kacikani tace dashi batare da juya ta kalle sa ba.

"Eashow yakira ta cikin sanyin murya bata amsa masaba shima be damu da ta amsan ba,kinko san halin da muka shiga da bamu ganki ba?"musu shiga de suka shiga waƴanda suka damu da ɓatata amma bakai dake zaune kuna tsara yanda bikinku ze kasance ba"what eashow kina da hankali kuwa?kinsan abunda kike cewa kuwa?kinsan matsayinki wajena aiko dan igiyar aurena dake kanki dole na damu a fusace Aisha ta juya tana kallon sa tace"Aure aure hmmm ai na wucin gadine naɗan wani lokaci da zaran kayi aurenka da wacce kake so zaɓinka ba xaɓin kowa ba ni kuma saika sauwake mun dan nasamu na aure wanda nakeso yake sona wani irin fizgota yayi bata ankara ba sai jinta tayi ta faɗa ƙirgin sa daidai basma sun fito tana dariya Aisha itako Aisha fashewa masa da kuka tayi basma ko batasan sanda jakar hannunta yatsuɓuce yafaɗi kasa ba......




ALLAH YASA MUDACE.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now