81

159 18 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

STORY AND WRITEN
    ZAHRA ALI ABDULLAHI

✨GORGEOUS WRITTERS FORUM✨

    ✨G.W.F✨

CHAPTER 81

  "Oga wai me wannan yake nufine da mu?
Girgiza kansa yayi yana haɗawa da murmushi saida yakai zaune daga tsaye da yake sannan yace"shiɗin Jarumine sannan Jajirtacce baya taɓa juya baya akan abun harin sa,ire iren sa muke nema dan sune waƴan da zasu kawo karshen su GAGARA BADAU.hhhhhhh

Sake baki Mutumin yayi yana kallon Ogan nasu dake dariya yace"Oga kana nufin karshen GAGARA BADAU cuwa cuwa harƙalla?
Ya tambaya da mamaki"kwarai Mansur yanzu ne lokacin da GAGARA BADAU zasu san muna da jajirtattun ma aikata ba lusarai ba,sannan karshen su yazo dan ze sasu guduwa akan titi ne.

Mansur yayi dariya yace"Oga kace muyi shirin sakasu guduwa ya faɗa yana rage murya"yes Mansur daga randa GAGARA BADAU yayi tozali da A-B sai yayi acawe a wando duk da su biyun ba wanda yasan ɗan uwansa shine abun harin sa.

"Oga kana nufin kace Ahmad besan waye GAGARA BADAU ba?"kwarai be san shi ba,haka shima Gagara badau ɗin basu san junan su ba,ba wanda yasan ɗan uwan sa.

"Amma Oga waye shi wannan ɗin?

kuma wace al'aqa ke tsakanin GAGARA BADAU dashi A-B ɗin?

"Hmm ya sauke ajiyar zuciya ya danyi juyi saman kujeran da yake zaune sannan yace"daga randa ya karɓi aiki a nan ma'aikatan ya dawo mana da martabar mu,bashi da tsoro tun fil'azal har yayi aiki damu,na tsawun shakara biyar ya samu mana nasarori da dama yaɗaga martaban aikin mu kafin barinsa aiki NAPTIP ɗin.

Mutum ne shi wanda bashi da tsoro ko kaɗan baya tsoron ko wace irin barazanar ƴan jagaliya,shine mutum na farko daya taɓa nunawa Alh Rabe hannu yakuma jashi a titi ya makashi kotu da tarin hujoji yanzu haka yana Gidan Mazan yana girban abunda ta shuka.

Bansan dalilin komawarsa aiki damu yanzu ba,saide naji labarin an maka Mahaifinsa kotu bisa zargin sa bisa lefi uku 1kisa
2 fyaɗe dakuma
3fataucin miyagun ƙwayoyi.
Ina da ya ƙinin ko yanzu zuwa yayi dan samun hujja yake nema dan kare Mahaifinsa a kotu yashi komawa aikin da yabari na tsawun shekara biyar na tabbata yanason amfani da wannan daman dan wajen ganin ya kare Mahaifin sa daga zarge zargen da ake masa sannan ya gurfana masu lefin gaban kotu.

Kuma zuwan nan nashi cikin mu ze mana amfani dan kawo karshen waƴan nan azzaluman masu fuskoki biyu cikin al'umma.

"Oga wani irin fuskoki garesu?
"Hmmm Mansur ka cika tambaya to suɗin ba ko wanne irin mutane bane face Dattawa ne su masu faɗa aji jagororine su masu jagoran al'umma amma fa a baɗinin su wallahi idan aka budema su ko Kare  baze shinshine abubuwa da  suke aikatawa.

"Oga yasake kiran sunan cike da kwarin gwiwa dan yanaji aransa yasamu Uban gida da zeyi dashi  tare.

Ɗaga masa hannu yayi yana cewa"Mansur No more question duk da hanashi magana da Ogan nasu yasoyi saide ya magantu da cewa"inason za mowa ɗaya daga cikin tawagarsa,a shirye nake dan rasa rayuwata ga kare ƙasata da al'ummata yafaɗa yana ƙamewa a gaban Ogan nasu.

Kallon sa Sir Olufemi Oba yayi yana faɗaɗa fuskarsa yace"Allah yayi jagora daga haka yaja file ɗinda Ahmad ya aje masa yasoma dubawa, Mansur ɗinma fita yayi daga office din yana nufan nashi office din yana jin wani irin farin ciki a ransa,dan gani yake yau ne karon farko da zeyi aikin da aka ɗauke shi dan shi yakuma yi alkawarin taimakawa Ahmad din da abubuwan da shima yasani gami da abunda yake son yin aiki kai.

******
Aisha suna zaune suna kallon hotona kaman daga sama Fauza ta faɗo musu falon ba sallama balle neman izini tana shiga ta dallarawa Aisha wani mugun harara tajan dogon tsaki tace"Allah wadaran naka ya lalace yanzu Sajida lalacewar taki har takaiki bin miji daga AUREN WUCIN GADI sai ki liƙewa Yayah kamar kaska saboda rashin dajara.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now