83

187 18 2
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTERD FORUM* ✨

    ✨G.W.F✨

CHAPTER 83

  Zaro idon tayi kaman zasu faɗo ƙasa tangal rangal tayi kaman zata faɗi tayi baya tafita daga falon ba tare da sun ganta ba,tana fita yasake ta yana komawa inda ya tashi ya zauna cike da bada umurni yace"oya tashi ki wuce kici abincin nan kona miki ɗure.

  Tasan ba wasa yake da ita ba ze iya mata ɗuren kaman yanda yace ɗin dan haka salim alim gwara tazo ci ɗin kaman yanda yace taci,miƙewa tsaye tayi saida ta ɗauki ledan kayan furuit da drink daya shigo dasu takai kitchen ta sakasu a freeze sannan ta dawo ta dauki ledar take away din tabude a hankali jalof ɗin macaroni ce daya sha kayan lambu hade da hanta da aka yanka gutsul gutsul sai ƙunshin nama a fege  tun kan tabude ledar taga abunda yake ciki ƴawun bakin ta yatsinke amma saboda karta bada kanta a gunsa cike da yanga ta bude tana yatsine fuska saida taje ta wanko hannunta kafin tazo ta zauna zaman cin abinci bata wani ci dayawa ba,amma taci naman da ɗan dama dan tamata daɗi sosai taci ta daura da freesh milk mai ɗan sanyi sannan ta mike ta tattare gun ta shiga tayi brush sannan tayi alwala ta fito tayi sallan ta anan cikin falo tana nan zaune tana addu'anta kaman yanda ta saba har ta gama ta gade kaman bashi da niyar dashi yashiga ɗaki ya kwanta.

Dan koo jiyan ma a bisa lalura ta kwana dashi ɗaki ɗaya amma bawai dan ranta yaso mata hakan bane,gyaran murya tayi ya ɗago da dubansa kanta ba tare da yabar abunda yake yi ba.

"Kwanciya nake son yi"and so?
Tura ɗan mitsitsin bakin ta tayi cike da shagwaɓan da itama batasan tayi ba tace"waje zaka bani kuma banason kwanciya cikin haske ta ƙarasa faɗin hakan tana murguɗa baki ganin ya ɗauke kansa daga kallon ta abunda bata saniba shine duk wani motsin ta akan idon sa take dan yana kallon ta a fakaice.

"Kina iya shiga ɗaki ki kwanta"ni fa bazan kwana da kai ɗaki ɗaya ba,tasake ce masa"saide yau kiyi kwanan zaune dan bazan bar aikina saboda ke ba.

"Ai wannan muguntane mutum kawai yazo ya zauna daki ɗaya da mutum bayan yasan rashin halascin yin hakan wannan ai shiga hakkin mutum ne ni gaskiya bazan kwana a wannan ɗakin ba saide kawai ka koma can ni kuma na kwanta a nan din,ta dage sai masifa take amma da zaran ta ga kaman ze ɗago kansa saita fuske.

Ta ishe shi da surutu dan har takai baya iyayin aikin da yake saboda yanda surutun nata ke hawa masa kai miƙewa yayi tsaye ya ajiye systerm ɗin gefe ya nufota ai kuwa da gudu tayi hanyan ɗakin ba shiri tana shiga ta kullo ƙufan girgiza kansa yayi yana komawa da zaman sa inda ya tashi yace"da alama yare ɗaya kawai take fahinta ita sake girgiza kansa yayi yana gajeran murmushi yana tuno moment ɗin su na ɗazo.

Mami tana komawa site ɗinta a falon ta taja ta tsaya tana tuna irin wahala data sha dakuma kuɗi data kashe akafin tasamu Ahmad din yasake waiwayar inda suke amma saide gani take kaman wankin hula yana neman kaita ga yin dare.

anƴa idan ta tsaya kallo burukan dukkan su ze cika kuwa?"kai ina yanzu duk wahala dana sha dan ganin auren sa da wancan Basman beyi ba sai ga wata ita kuma wai Aisha duk da har yanzu bata gama sanin wace alaqa ne ke tsakanin sa da ita ba amma da alama akwai kamshin gaskiya a maganar da Sajid yafaɗa mata ɗazu da safe dan tasan Ahmad ciki da bai inde ba canza halinsa yayi daga baya ba,da dekan tasan harkar ƴan matan basu a gaban sa belle sukai ga sun burgeshi duk yanda yan matan ke bibiyarsa amma shi baya kulasu.

Irin yanda taga yana riƙe da yarinyar yanzu dole akwai wata alaqa tsakanin su,idan ita din matar sace fa?ta tambayi kanta saurin kawar da wannan tambaya tayi tana kai ina hakan baze yu ba.

Tace tana zagaye falon dan neman mafita,can tatuna da ƙawarta Hajiya Taslima tayi saurin zama tana ɗaukan wayan ta takira ta ringin ɗaya ana biyu ta ɗauka tana cewa"ke ba ajinki ko ganin ki saita ɓaci.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now