90

213 18 2
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨

  ✨ *G.W.F* ✨

CHAPTER 90

Ja baya kaɗan yayi jin abunda tace ɗin,kallonta yake ta kasan idon dan shi kadai yasan abunda yakeji gami da ita,idan ta kalle shi jin wani abu yake na tsirgar masa jinin jikin sa.

Jin yake kaman ya haɗiye ta su zama abu ɗaya"ni kafita mun a ɗaki banason ganin ka kusa dani kuma sai na rama mugunta da kamun ko shari'a ta kwatan mun hakki na.

Sosai yanzun kan yake kallon ta ko kiftawa babu dan jin abunda tace ɗin,nufota yayi taja da baya haka sukai ta tafiya harta kai kuryar bangon ɗaki"kide rama din zefi ba sai kinkaini ga shari'a ba dan nasan ko munje ba iya faɗa musu abunda yahaɗamu zakiyi ba,ya faɗa cikin yin ƙasa da murya kaman mai raɗa.

Da karfi ta rintse idonta ta ciki jin zafin abunda yace da ita"eh naji kafita mun daga ɗaki tunda kariga kasami abunda kakewa yanzu kuma me kazo yi guna,ko zuwa kayi ka gani idan ban mutu ba ka ƙarasa ni,ka cuceni ka cuci rayuwa ta bayan kasan ba so tsakani da Allah kakemun ba,ba kuma Auren dindindin mukai ba kaman yanda kafaɗa mun a gaban kowa da kowa tunda kasan Auren wucin gadi kai dani to me naka na rabani da budurcina da kai?

"keep quite Aeshow yafaɗa cikin hargowa kaman zekai mata bugu.

Fashe masa kai da kuka tana cewa"tunda kasan ba sona kake ba dole kace nayi shiru, karabani da abunda na jima inama Mijin da zan Aure tanadi na dauki tsawon shekara goma sha tara ina tattalin sa sai gashi cikin minti goma sha tara karabani da shi.

kuma ka wanice karnayi magana karabani da masoyina na gaskiya wayyo ni Anna ina kike kizo kiga abunda.
dan kaga bani da kowa ina zaune Gidan ƴan uwanka shine kamun haka?eh

Tafaɗa  hawaye wani na bin wani bisa kyakkyawar fuskanta karshe kuka tasake fashe masa dashi tana ƙanƙame jikin ta,yanda tayi masa maganan take yaji jikin sa ya masa sanyi so yake ya rikota ya fadamata bada niya yamata hakan ba amma ina taƙi ko bude idon belle yayi tsammanin zata kulashi karshema daya dage wajen bata hakuri a tsawace tace"dan Allah malam karabu dani ko dole saina kulaka.

Cak yaja ya tsaya jin yanda take faɗa masa magana son ranta kuma a tsawance cikin fitan hayyaci"Ahmad ko zaka ɗan jira a falo ne?
    Anty Haraja da tunda Aisha tasoma magana take tsaye daga bakin ƙofa dan taxone ta bata magani tasha kafin ta kwanta dan ita batasan da zuwan Ahmad din ba ma.

"Amma Sis... jinjina masa kai tayi bata bari yayi magana ba,bayan fitan Ahmad waje riƙo hannun ta tayi ta jata zuwa bakin gado ta zaunar da ita ruwa mai sanyi ta miƙa mata cike da kofin glass karɓa tayi ta shanye tas ta ajiye kofin tashiga sauke ajiyar zuciya saida ta dan nutsu sannan Anty hajaa ta kalle ta tace"Ƙanwata banji daɗin yanda kikawa Ahmad magana ba,ko ba komai shiɗin sama yake dake balle kuma Aure ya haɗa ku kina zaune a ƙarƙashin ikon sa,yana kuma da hakki a kanki kaman yanda kema kike da hakki a kansa.

Banji daɗin yanda kikayi ta faɗa masa maganganu son ranki haka ba,kina ɗaga masa murya kinsan hukunci mace da take daga murya wa mijin kuwa?

Aisha ina hankalin ki me amfanin ilimin ki inde ba zakiyi amfani da abunda kika sanin ba,ko a lahira hukuncin wanda yasani ya take sanin hukuncin sa na daban ne.

Share hawayen ta da yaƙi tsayawa tayi sau babu adadi cikin rawar murya tace" Anty bakisan abunda yamun bane daya zo..."idan ma nasani Aisha sanin nawa bazeyi amfani ba,tunda mijinki ne shi kumama me aciki dan yazo dubaki  lefine yin haka ai sai wanda yadamu da kai yake bibiyarka Aisha nasan Ahmad gaba da baya idan ba daga bayane ya canza hali ba shi mutum ne da baya shiga tsabgan mata,ko sanda yake Makaranta matan suke bibiyar sa yake guje musu,harkuma yau din nan bana tsammanin yana kulasun,keɗin ma da halak din sace.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now