35

161 16 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Chapter 35

Ɗaukan ta yayi be direta ko ina ba sai a tsakiyar office ɗin sa yashiga kallon ta daga sama zuwa ƙasa dakyar ya hadiye wani abu daya tokare masa a maƙoshin sa,
Cike da taƙaicin ɗaukarta dayayi kafin yayi magana tariga shi cike dajin haushin sa a tsiwace tace"wai me hadina da kaine daxaka wani kinkimo ni haka saikace
wanda ya dauki matar sa?

Wani abu yaji yana yayo tun daga saman kansa zuwa babban yatsan kafarsa dakyar ya iya daidaita nutsuwar sa fizgo maganar yayi yace"wani irin shigane wannan da kikayi?

Mamakine yacika Aisha a fakaice takalli kanta sai kuma ta maida kanta gefe ba tare data tanka mishi ba,ganin tamasa banza yasake jeho mata da wata tambaya data sata ɗago kanta ba tare data shirya ba,zuba masa idanunta tayi sai ta murguɗa masa baki tana dauke kanta daga kallon sa.

Takowa yayi gareta cikin takun nan nasa na ƙasaita baya baya tasoma yi yana biye da ita saida tajin gina da bango takowa yayi daf da ita tokare bangon yayi da hannuwansa duka biyu ritse idanunta tayi da karfi ganin yanda yatsaya daf da ita har suna iya jin hucin numfashin junan su,

zubama baby face ɗinta ido yayi yana kare mata kallo wani abu yaji yana taso masa tundaga babban yatsan kafan shi har zuwa tsakar kansa.

Wani abu yakeji mai kaman mayen karfe yana jansa zuwa gareta besan sanda yakai hannun sa ɗaya ya dago haɓarta ba,sai jin saukan tattausan leɓenta tayi saman nata.

Waro manyan idanun ta tayi bata sauke ko ina ba sai saman fuskan sa da idanun sa suke kulle,wasu zafafan hawaye na zallah takaici da tsanar sane suka shiga zubo mata daga ƙwarmin idon ta.

Ɗumin hawayenta dasuka zubo masa saman fuskan sa shiya ankarar da shi kuka take saurin saketa yayi yana ja da baya,ganin ya saketa yasata duka awajen tasaki wani kuka maicin rai kaman ranta zebar gangan jikita tanayi tana goge bakita da gyalen dake kanta tana tofar da ƴawu.

Saida ya daidaita kansa sannan ya iya buɗe bakin sa yace,matukar kika sake irin wannan kwalliya kikazo to wannan shine hukunci da zanyi miki,sai na tsotse jan bakin tass...Ɗagowa tayi a zafafe ta banƙa masa harara kaman idonta ze faɗo kasa ta murguɗa masa baki tace"ɗan iska kawai kace kawai iskanci kake neman yi mun.

Wani irin zabura yayi jin abunda tace ɗin ƙwasa tayi da gudu tayi waje kaman zata kife,komawa yayi ya zaune saman kugera haka kawai ya tsinci kansa da sakin murmushi da besan dalilin sa ba,dacewa yarinya bar ganin kun tsira zamu haɗune dake.

Saida tayi nisa da office ɗin nasa taje can ƙarkashin wani bishiyar maina sannan taji wani irin kuka mai karfi yataso mata,saida tayi mai isarta sannan ta tashi jiki baƙwari tanufi hanyan fita dan tafiya gida.

Tana ƙokarin fita wata baƙar mota ta shigo wajen haka kawai zuciyarta ta bata tabi sa komawa tayi da baya ta laɓe bayan wani mota tana kallo wani mutumi yafito daga cikin motar bayan ya faka yanufi ciki wajen direbobi dake lodin kaya suna kaiwa gari gari bayan ɗan shuɗewar minti shida zuwa bakwai sai gashi da wani daya daga cikin direbin sun iso wajen motar tasa a tare shiga ciki sukai sai gashi wannan direban ya fito riƙe da wata baƙar jaka rike a hannun sa sai washe baki yake yana dafe da aljunun sa da alama kudi aka bashi yasa sallama sukai yashiga ciki dan komawa inda yafito shikuma wacan mutumin yaja motar sa yafita da uban gudu.

Wallahi tunda take bata taɓa taƙaicin rashin riƙe waya ba sai yau"yama zama dole nafara riƙe waya a hannuna tace dafata taji anyi da sauri ta juyo cikin tsoro.

Wannan direban ne ashe tunda suka zo da wacan mai motan yalura da ita a wajen shiyasa yace sushiga cikin mota shine yanzu ma yazago yazo"me kikeyi anan?

Ya jeho mata da tambaya,fuskarsa ba rahma yake kare mata kallo ta tsorata da irin yanda yake binta da kallon dukda ta tsorata da irin kallo daya binta dashi amma bata bari tsoron yayi tasiri a ranta ba ta aro jarumta tace"gudowa nayi ta bashi amsa tana barin wajen.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now