80

169 25 2
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

STORY ND WRITTEN
    ZAHRA ALI ABDULLAHI

____________________
✨ *GORGEOUS WRITTERS FORUM* ✨

    ✨G.W.F✨

*GORGEOUS,INTELLIGENT,AND EXPERT WRITERS,WE THE BEST AMONG THE REST.*
__________________

CHAPTER 80

  A corridor ya cimmata tare da mummyn ta hajia mariya da ita ma kaman wacce aka mitsina tafito tana kallon mummyn nata ta faɗa jikin ta ta fashe mata da kuka mai ban tausayi cikin kukan take cewa"mummy kema kin yarda da narasa Ahmad kenan ki faɗawa daddy shine wanda ya ƙwaitamun da auren sa tun bansan shi ba shine wanda ya koyamun yanda zan so shi yakuma alkawarta mun da samun sa matsayin mijin aure,amma ya kasa cikamun alƙawarin,bayan ni ba abunda yanemi nayi masa wanda banyi masa ba da karfina da harda jikina dan kawai nacika masa burin sa nason mallakan abun da zuciyar sa ta ƙwaɗaitu dashi to ni mai yasa ba ze cikan wannan alƙawarin ba.

Bayan ni ba abun da yataɓa sani wanda ban aikata masa ba,daddy ka rubuta ka ajiye idan nasa kowa ze rasa.

"A'a Basma karki sake cewa kin rasa ni nine nan wanda ze nema maki abunda ranki keso koda a ƙarƙashin ƙasa yake,sai kuma ya sassauta murya yace koda zan rasa tawa rayuwar dake ki rayuwa yana kaiwa karshe ya fita waje cikin sauri shi kaɗai yasan abunda yakeji a ransa.

"Yau naga ikon Allah ni Tani ta Malam Tanko Gwaggo da take tsaye tun fitowar Hajia Mariya tana sauraron duka abunda suke magana ta cigaba da tafa hannu tace wai Mariya me kike ɓoye manane ni?

Eh ko kina da wasu waƴan da suka fimu ne?
Ina Usmanu?tunda muka zo nake ta baza ido in ganshi amma bashi ba labarin sa,sake tsuke fuska tayi irin ba wasan nan da Gwaggo Tani irin Matan nan ne masu zafi da masifar tsiya da kuma yawan mita idan kayi lefi sai ta kusan yini tana maimata magana dan haka kowa shakkarta yake.

Yayace gun Mahaifin su koda Iyayen nasu suka amsa kiran Allah dukkan su dan gini ne ya rushe da su cikin damuna ana tsaƙa da ruwa ita ta karɓi rikon su basu taɓa kukan maraicin Iyayen nasu ba,ta tsaya musu tsayin daka basu taɓa neman wani abu sun rasa ba.

Haka suka rayu cikin rufin asiri basu taba neman wani abu wanda takasa yi musu shi ba,ta aurad da Hajjo ga wani attajirin mai kuɗin sannan kuma ta aurad da ita Mariya wa Alh Sunusi tun lokacin yana ɗan buga bugan sa daga baya kuma ya haɗu da wani uban gida ɗan jarida yana masa driver sannan suka zo suka fara harkar kasuwanci da uban gidan kafin shima ya amsa kiran Ubangiji Allah.rasa me zata cewa Gwaggo Tani sai kawai ita ma ta fashe da kuka saboda susa mata inda yake mata ƙaiƙayi da Gwaggon tayi wato Usman dan tunda yasaka kafa yabar gidan da sunan fita waje karatu bata sake jin muryan ko mai kama dashi ba.

*****
Aisha na shiga falon ta ga file ɗin a inda yace mata ya ajiye ta dauka har zata fita ta tuna da koran ta da Hajia da ƴarta sukai sai kawai ta koma ta dauki hajibi da tayi salla dashi tasaka tafito yana nan tsaye a inda ta barshi saide yanzu Hajiyar nan da taji ya kira da suna Mami tsaye take sun saka shi gaba da ɗiyar nan tata suna magana duk bata ji mai suke faɗa masa ba,haka kawai taji ta tsane su batason sake zama kusa dasu duk da be fito ya faɗa mata wace alaqa ne ke tsakanin sa da sudin ba.

Tun kafin ta ƙasara isowa   inda suke ya kafeta da ido yana kallon yanayin takunta cikin tsari kaman da gaiya take takawan,zagawa yayi ta bayan su ya isa gareta yana kai hannu ya karɓi file ɗin tare da saƙale hannun ta a nasa hannun ba tare daya kalli fuskar ta ba yashiga ta kowa a hankali dole ta bisa tunda itama din tanason barin gidan dan batasan idan tabari ya tafi dame za su zo mata ba,gashi ba sanin gari tayi ba balle tace zata gudu ta komawar ta inda tafito.

Suna gaf da giftasu Mami ta kalle hannun su dake sarƙafe dana juna tana yatsune fuska tace"kaji mun wani sabon tashanci anan yanzu Ahmad ko kunyar ido na ba kayi zaka riƙe hannun ta haka,ai ko mutuwa tana kunyar ido a kan wannan abar kake koƙarin wulakanta ƴar uwarka itadin wacece a wajen ka?

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now