66

154 13 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 66

      "_Kiyi hakuri Aisha babu abunda zamu iya yi kiyi tamasa addu'a da zaran yayi bacci ya farka ze dawo normal kaman ba abunda yataɓa samun sa.

An dalilin zuwansa wannan wajen sabida ke mukaje yaga hotunan ki a media yana ta yawo mutane da dama sun ɗaura a shafukan sadarwarsu yazama abun muhawara yanda kuka halarci wajen taron ƴar gidan Alh sunusi Oga yaji tsoron kar su Alh sunusi suyi miki wani abun na cutarwa saboda fushi dayaga ƴar tayi awajen saboda ɓata mata taro da kukayi shikuma a duniyarsa ba abunda yakeso yake kuma gudun fushinsa sama da ƴan nan tasa wannan saya muka garzaya zuwa wajen dan baki kariya kuma mukai katari da wanƴan mutane sunyi garkuwa dake.

Share hawayen daya wanke mata fuska tayi tana kallon Goga dake mata bayani ta bude bakinta dakyar tace"dama damuwa tana jawo taɓuwar ƙwaƙwalwa?"eh idan tayi yawa sannan ya haɗu da ƙunci yakan jawo hakan saide shidin ba damuwarce kaɗai tajawo masa wannan hali dayake ciki ba,harda asiri da akai masa dan son a haukatashi,"asiri kuma?''eh asiri wannan karon lukman ne yayi magana labarine mai tsawo Aisha abun mai mahimmanci garemu yanzu shine daƙile duk wata hanya da Alh sunusi zebi dan kawo karshen zaluncin sa,sannan target dinsa yanzu shine Alh badamasi yana amfani dashine dan ganin yakwace masa dukiya da komai nasa yaxo hannun sa.
Wannan ƙuduri nasa yasa yabawa ɗan Alh badamasi auren ƴarsa daya tilo dayake matukar so,sannan yayi hakan da biyune dan shi a nashi tsarin inso samune da anyi auren ango yatare a gidan sa naƴan kwanaki zebi duk wata hanya dan ganin yaraba aurensa da ƴarsa bayan saide kudurin sa akan shi angon ne haryanzu bamusan abunda yake shiryawa ba.

Shiru Aisha tayi tana sauraron duka abunda suke cewa ganin magariba tayi duka alwala sukai sukai sallah jam'i anan sai lukman da sauran sukai masu sallama dacewa zasuyi waya,akabar Goga da Goge da wasu tsirara kana ganin su kaga yan daba na haƙiƙa bayan ta idar da sallah tana nan zaune tana ta tunanin shin wayama mahaifinta asiri to dan mema zamasa asirin shida ko can be tara komai ba,bayan aikin sa daya saudaukar da rayuwar sa da lokacin sa kacokan ga aikin sa wajen bankaɗo da sirrikan da ba'aso a sani yanda Anna ta zauna koda yaushe cewa take Aisha kizama mai gaskiya da rikon amana a rayuwari kaman mahaifinki idan kikayi riko da wayan nan abun biyu sannan ki kara da hakuri zaki zama abun koyi kuma gaskiyarki ze kaiki ga nasara arayuwa.

"Aisha Aisha kiran sunan ta da akaine tunanin ta yakatse dago da jajayen idanun ta tayi tazu su akan sa"ko kina bukatan wani abune akawo miki,kai ta girgiza masa alaman a'a.

Su Ahmad kuwa barin hotel din sukai tunda dattijon nan yace masu motocin sunyi nan kudu ku duba kugani ko za dace,nan ɗaya daga cikin abokan aikin Faisal ya amshi tukin motan Ahmad ganin yanda Ahmad din yakoma so weak jiki duk asake.

Saida sukai tafiyan minti talatin mai kyau sannan suka tadda mota tashiga karkashin daf,sauka sukai da sauri bayan sun parka motocin su dukkan su zuciyoyin su na wani irin bugawa na tsoron abunda zasu tadda a can din,saide koda suka karasa wajen da dan sassarfansu sun iske drivern daf din sai yaro motan sa saikuma bakaninki ID dinsa faisal yaciro yanuna musa sannan yashiga tambayar su me yafaru a wajen.

Driver yace"ranka yadaɗe motar muce tasamu matsala tun da safe,to koda muka kira bakaniki ɗazun ganin to akwai karfen da sai an canza shine ya aiki yaron sa yaje yasayo mu kuma muka zazzauna anan zaman jiran daworsa  muna ɗan taɓa hira muna sauraron radio kaman a shirin film mukaga mota tayo kanmu a guje shine muma muka ranta a nakare dan tsiratar da rayuwarmu daga can mukaga wata mota data biyosu taja tatsaya"wasu kattine majiya karfi suka firfito daga cikin motan suka yo wajen wannan mota suna zuwa suka bude suka fito da samari biyu bayan wannan motan cewar bakanikin babban motan dayake da farko drivern ne yayi magana"shin acikin motan da akwai mace cikin su?Ahmad ya tambaya"eh naga anfito da wata kaman ma bata numfashi suka nufi daya motan da ita dawani babban mutum ke zaune a ciki"shi na cikin motan da akakai yarinyar yafito waje ne?ko zaka iya fada mana kamannin sa?faisal ya tambayi yaron motan"a'a gaskiya yallaɓa banga fuskansa ba dan be fito daga cikin motan ba kumama muna danisa tsakanin mu akwai tazara mai tsawo muna wancan ƙududdufi kaga bazama iya gane kamannin mutum ba"hakane to amma bayan tafiyan su ko aakwai wanda yaxo nan din"shiru sukai dan tabbas akwai saide gargadi da akai musu baze bari su faɗi ba"daya daga cikin abokan faisal dinne ya daka masu tsawa yana cewa"bako akema magana ba kunyi shiru ko kafin mu akwai wanda yaxo nan din?ciki ruɗewa yaron mutan daf din ya amsa da"eh yallaɓe saide sun gargademu driver da bakanikin nan sai muzurai suke suna masa alama karya fadi amma saide yayi kaman begani ba saima cigaba da magana da yayi wasu gungun ƴan sara sukane suka zo nan din saide sun tadda bakowa wajen shine suka ce ko jami'an tsaro sunzo karmu yarda muce sun zo nan din"ina sukabi?nan yayi musu nuni da ɗan yatsaya hannun faisal yamiƙa musu sukai musabaha yace"mun gode ƙwarai da hadin kai dakuka bamu zaku iya janye wannan motan gefe dan kuji daɗin gyara naku daga haka suka shiga motan su suka bar wajen.

Anty malika tayi kiran Faisal yafi aƙirga sai yanzu yasamu ya dauka ko sallama bata tsaya yimasa ba tace"yauwa yah faisal kunganta?"haryanzu bamu ganta ba nan yakwashe yanda sukayi da masu daf din nan yafaɗa mata"innalillahi wa'inna ilaihirraju'un tashiga faɗi Malika lafiya?sai kawai ta juya tafaɗa jikin Anty hajia tasaki kuka tana cewa Anty hajia wallahi Aishace sai Aishace kawai take maimai tawa"naji Aishace me?meyasa meta?mekuke ɓoyemun tun ɗazu shima ɗan uwan naki yaxo ya tambayeta inma wani abune yasameta ku fadamun mana malika amana uwarsu tabarmun su kar naxamu cikin masu kasa rike amana dan Allah kibar kukan nan ki sanar dani meke faruwa sai kawai itama tasa kuka ganin kukan nata yasa malika sassauta nata tashiga sanar da ita aikuwa bata ida sauraro ba tasume mata tana kiran ƴaƴan amana uwarsu tabarmu ya Allah kadubi maraicinta ka kuɓutar da ita daga hannun koma wanene tun ana iya jin muryarta harma tadena motsi gaba ɗaya iya tsorata malika ta tsorata da yanayin da mahaifiyar tasu ta shiga sai kiran sunan ta take tana jijjigata amma ko gizau batayi ba saurin daukan waya tayi takira faisal tana kuka ta sanar da shi abunda yake faruwa,ya amsa mata da gamunan zuwa kawai Ahmad yakira dayake ɗaya motan ya sanarwa da halin da ake ciki faɗa yashiga yi mai yasa aka bari tasani bayan kasan Anty hajia da Ammina basu iya ɗaukan abu da sauki ba ya salam yafaɗa yana dafe kansa dake sara masa yakashe wayan.

Hajia mariyah zaune take a katafaren falonta daya wadatu da kayan alatu ta daura kafa daya kan ɗaya sai girgiza kafan take ta kalli kawayenta hajia bilki da hajia shema tana yatsine fuska tace"wai wannan yarinya da wancan dan iskan yaron yazo da ita wajen party da ita ƴar wani matsiyacin yasamo?bintse baki hajia balki tayi tace"inade ganin kaman Aisha ce saide wannan kaman tafi Aisha fari da wayewa,wani irin zabura hajia mariyar yayi tace"wace Aisha kike nufi bade Aisha yarinya dake mana wanki ba.

Ita fa"a'a bilki karkisaka jinina ya hau"to wai ke mariyah idan kina tantamane ki kira basman ki tambaya ƙila ita bazata rasa sanin ta ba,cewar hajia shema.

Waya hajia mariya ta ɗauka takira basma tana dagawa tace"komai kikeyi kibari yanxu kisame ni a falo tana cewa haka takashe wayan minti biyu tsakani saiga basma da kawarta salaha suka shigo falon ko sallama basma batayi ba,sai salaha ce tayi sallama ta gaishe dasu hajia ita ko basma sai cika take tana batsewa tasamu waje ta zauna kallon ta hajia mariyah tayi cike da ɓacin rai ta kallata tace"ke dan ubanki wace yarinya Ahmad yaje da ita dazu?tura bakin ta tayi cike da sakalci tace"yo mummy ina zan santa bayan yace abokiyarsa ce da wani dan jarida ya tambaye shi"shin kin bashi wani abu ko ruwane yasha a wajen?tambayar da hajia shema tayi mata kenan"mummy shema ina zan bashi bayan yazo da wata ya batamun komai nawa nayi ta cika baki wajen kawayena yazo ya dizgani"la'ilaha illallahu yanxu basma duk abunda muka fadamiki rannan yatashi a banza kenan ke kinsan muƙudan kuɗaɗen da nakeshe wajen saman miki da maganin da muka kaɓo miki common ki bashi ruwa kodan wani lemu yasha kika kasayi gashi yanzu kinja mana asara yanzu gashi ai yasomo yarinya da batakai kiyi kishi da ita ba zata rainaki"kuttt amma mummy meyasa tun ranan baku bude komai kunfada mini ba,"ngonan basma hajia mariyah tafaɗa tana mata dakuwa cike daɓacin rai,yanzu ke yarinya ce da komai sai anbude maki shi zakiyi.

"Shin kinsan ko wacece yarinyar?hajia balki ce tajeho mata da tambayan"girgiza kanta tayi cike da jin haushin mummyn ta gani take kaman cin fuskane ta kirata sun sakata tsakiya da kawayenta suna yimata faɗa why not tabari daga ita sai ita"to kinga irin shashancin naki ko ko yarinyar baki iya kingane taba"kaman de wannan yarinyar da kika taɓa kira da mai wanki ranan da mukaje wajen......ai bata bari salaha tagama maganan ba tamiƙe a zabure tana lallayo ashar tana yaɓawa.




ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now