40

160 15 0
                                    

💕 *AURE WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 40

  Saida ya sassauta da dariyar dayake sannan ya dubesu ɗaya bayan ɗaya yace"kafin sannan na san kai Alh hamza kasani cewa koda giwa ta faɗi tafi karfin.....be barshi yakai karshen maganan ba yace"haba haba ya alhaj karkaji komai ba wata matsala kawai de mundan shiga ruɗune kasan sha'anin kuɗi ba abun wasa bane ba.


Alhaji ɗahiru ya amshe da cewa"kuma kaima kanka Alhaji sunusi kasan harka ta kuɗi kaman yanda bakason wasa dasu haka muma dan idan mutum yace ze shiga tsakanin mu da samun mu to wallahi yanzu ne zamuyi uwar watsi da shi.

"Aisha yakira sunan ta.

Ɗaga masa hannu tayi murya na rawa tace"kaini gida kawai ba lalle ne karamin kwakwalwata ta iya ɗaukan abunda kake cewa ba.

A karancin shekarun nan nawa ba lalle na fahinci mai kake cewa ba,da kace mahaifina yana yaraye gwara kace dani anga mahaifiyata wannan shine abunda zan iya yarda da shi.

"Amma Aisha kinsan bazan miki karya ba ko?
Yafaɗa yana tsareta da ido.

Saida ta share hawayen da ke kwaranƴa a idanunta sannan tace"aiko yanzu yaya faisal bance karya kayi nun ba,amma menene dalilin ka nacewa mahaifina na raye?

Tsawon wannan lokaci shekara goma fa ba kwana goma bace ba?

Abu ɗaya nasani shekara tara baya an tsinci motar sa ta ƙone hakan yana nufin be tsira da rayuwar sa,idan ko yana raye yaci ace tsawon wannan lokacin wani ya gansa koda hatsari yayi ya kamu da cutan mantau wata ƙila wani yagansa ko ayi cigiyar ƴan uwansa amma ina anyi haka?

Idan kuma bayani kake so na baka gami da abunda yashafi aikin ka ba wai sai kabi dani ta nan ba zan faɗa maka iya abunda nasani,zanyi hakan ne dan cikan burina dakuma ta iyayena amma zancen wata NATASHA kabarta nan daga haka taja bakin ta ta tsuƙe duk yanda Faisal yaso ta bashi haɗin kai suyi magana taƙi dole bawai dan yaso ba ya ƙyaleta dan bata daman tayi tunani.

Ahmad zaune yake a main falon gidan su yana tura wasu samfuran kaya wa customer ɗin sa,Ammin sa dake zaune gefe tana kallon tashar sunnan tv ta ɗan maida kallon ta kansa tace"kasan yaune kai lefen ka ko?

"Nasani ya amsa mata cikin halin ko in kula.

Kallon sa tayi da mamaki ganin bema nuna damuwar sa ko wani zumuɗin sa kan wanna. auren ba,cigaba tayi da maganan nata tasake cewa"wani tanadi kaiwa bikin naku dan naga Alhaji yaɗauki abun da mahimmanci sosai.

Sannan kuma dama ina tason muyi magana da kai gami da yarinyar da nace zan zaɓa maka to Alhamdulillahi an rigada an ɗaura auren ka da ita tuntuni da wani irin sauri ya ɗago da kansa yana kallon Ammin nasa dake magana saide duk kwafkwafinka baka isa kace ga yanayin da yashiga ba.

Tuni yaji ƴawun bakin sa ya ɗauke magana yake son yi amma yakasa furta koda kalla gudane.

Sai cigaba da magana da Ammi tayi bata damu da sai yace komai ba,Ahmad na tabbata zakayi alfahari da wannan auren,nan gaba dan yarinyace mai hankali da sanin yakamata na yaba da tarbiyarta da kuma hankalinta shi yakaini ga sha'awan aura maka ita.

Idan kasamu lokaci zaka iya zuwa gidan Antinku hajia tana can da zama tun bayan daura aurenka da ita zamanta ya koma can.

Kafin ta sake wani magana Alhaji badamasi ya banko ƙofar falon  ko sallamar kirki babu yashigo cikin falon yana aunawa Ahmad din harara shiko Ahmad ƙasa da kansa yayi dan yasan kwanan zancen"lafiya Alhaji?

Ammi tayi tambayarsa dan ganin yanda yake huci,da mugun kallo yabita dashi yana cewa"eh dole ki tambayeni ko lafiya tunda kin iya saka shi gaba ki zugashi.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now