51

211 21 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 51

  "Ransane yayi mugun ɓaci da abunda Ahmad ɗin yayi masa dama gashi cikin ɓacin rai yake yauɗin tunda yabaro wajen shugaba,laluɓen wayansa yasake yakira Alh badamasi dashima yake zaune zaman jiran jin shin Ahmad din zebi umurnin sa ya aiwatar da abunda ya umurce shi yayi koko bazeyi ba?

Kiran yashiga wayan sa saurin dagawa yayi tunma kafin Alh sunusi yayi magana yashiga bashi hakuri yana cewa"wannan takadarin yaron beje ko Alh amma kayi hakuri kabarni da shi anjima da kaina zan tasosa gaba nakawo shi har gidan naka amasa afuwa kasan sha'anin yaran zamani yarane ba duk abunda mutum keso sukeyi ba.

Yanda Alh badamasi ya marairaici murya da kaskan da kai kaman ɗalibi yama malaminsa lefi zai zanesa yana bada hakuri haka shima yayi abun gwanin tausayi gwanin ban haushi kai kace bashine Alh sunusin yake nema daga gareshi ba tsaban yanda ya asirce shi.

HAJ MARIYA
"Sauke numfashi tayi bayan ta gama sauraron ƙawartata tace"yanzude kawata duka ba wannan ba wace hanyace kike ganin zan samu natatsi Alh rabona cikin ruwan sanyi.

"Yanzude magana zaki masa zaki fara kasuwanci sarin kaya daga dubai china mukuma tsoffin yan kasuwa zamu samo miki da customers kinga daga haka sai kifara zaran rabonki idan yashigo da ƴaƴan banki cikin gida,ke ba ruwanki da nau'in kuɗi bata kasarnan bane kawai zara zakiyi"anƴa kawata kina ganin bazai zargeni ba,ta faɗa cike da tsoro.

Murmushi Haj balki ta sakar mata tace"kingani ko wannan tsoron naki bazai taɓa bakirinki kiyi abun arziki ba,jeki kawai duk sanda kika shiryawa neman nakanki sai kisake zuwa muyi zama na musamman idan takamama muje dake can ƙungiya inyaso ƙyaji ta bakin sauran manya mata idan kin shirya zama babbar mace wacce zadama dake to sai taware mata hannunta idan ko baki shiryama tafiyan nan shikenan sai kiyi ta zama kinashan Ac ki ci zaji kisha juice ki juye a masai wannan shine ribarki.

FAISAL
"Wai ya ake cikine haryanzu yau tsawon kwana uku da ɓatan ƴan ta addannan waƴan da hukuma ke nema ruwa a jallo amma ace waƴansu zasu samu nasanar sacesu abun kunyane garemu baki ɗaya mene amfanin mu?

"Sorry muna iya bakin ƙoƙarin mu dan ganin munsamo bakin zare"a hakan kake wani cewa kuna kokari ina ƙokarin take anan?faisal har tsawon wani lokaci ya daukeka dan ganin ka kamo ɗaya daga cikin su shin kayine?kamal kenan shike magana cike da fushi dan yaso abashi wannan case amma aka hanashi aka bawa faisal shisa yasaka yaranshi cikin tawagan faisal din batare dashi faisal ɗin yasani ba suke kawo masa dukkan wani mutsin faisal gefe guda kuma yahaɗa kai da ƴan ta'addan shike basu bayanai har suke samun zarran tsallake duk wani tarko da ake ɗana musu.

Murmushi mai ciwo faisal yayi ba tare da yakalli sashin da kamal din ketsaye ba yafara magana kaman haka"yallaɓe muda muke da bara gurbi cikin mu masu fitar da duk wani motsinmu suna saidawa ƴan ta'adda akan farashi mai sauki tayaya kake ganin zamuci nasara akansu har mukai ga kamesu bana zaton haka ko gaba dan cikin mu masu sanye da uniform waƴanda sukai rantsuwar kare rayuka da dukiyoyin al'umman ƙasa amma suke daƙile layukan wayoyin mu bamu isa muyi magana koda ta sirrine da iyayen mu ko abokan aikinmu ba face sai waƴan nan ƴan ta'addan sunji komai.

Kaima kanka kasan nasaran mu bazata samu ba inde a hakan zamuyi tafiyar harsai mun wanke dauɗan dake tattare damu,sannan maganan sace su LION a gaskiya ni banyarda sace su akai ba kawai anawa tunanin gani nake kaman sun ɓoye kansune saboda sunason wasa da hankulan ƴan sanda nide a nawa ganin kawai rabuwa zamuyi da su basai mun sha wahalan cewa sai mun nemo suba ko sai lalle munsan inda suke ko wayan da sukai wannan aikin ba,kawai mu maida hankulan mu kan wasu aiyukan daban masu mahimmanci.

Cike da gamsuwa da bayanan faisal din IG yajinjina kai shiko kamal kwafa yayi ganin ba wanda ya kula da zance sa shide haka kawai yaji yana zargin faisal akan bacewar su Lion ɗin tunda manyansu irin su Alh shehu da Alh sunusi sunnun lalle lalle yabinciko masa wake da hannu cikin kame musu yara kuma abun mamaki kosu ƴan rahoton nasa basusan da wannan zance ba to waye da alhakin wannan aikin.

Ahmad bayan yagama waya da basma kashe wayan nasa yayi baki ɗaya yakuma juya akalan tukin nasa zuwa wani gidansa dayake sauke baƙi gidane ɗan madaidaici kuma ginin gidan ya tsaru dan wani tafiya da yayi turkiya acan yasayi zanen gidan,horn yayi mai gadi ya bude masa kofa saida ya tsaya suka gaisa da maigadin sanna yanufi ciki ya parke motan direct falon yashiga yasamu komai tsaf bawani ƙura tunda akwai mai shara wato matar mai gadin ita ke wannan aiki kuma yake biyansu albashi ita da mijin nata.

Saman kugera yakwanta hutu yake buƙata na ɗan wani lokaci cire rigar jikin sa yayi yamiƙe madadin hutun da yake bukata gakuma kansa sai sara masayake kaman yarabe gida biyu,sai kawai yashiga tunani wai yama akai daddynsa baya tsayawa koda yaushe matukar abu ya danganci Alh sunusi yayi tunani ko yabi abun a hankali ne sai kaganshi duk yasusuce kaga kaman yayi lossin main dinsa,dan ko Amminsa bayajin daddyn nasa yana ɗagawa ƙafa inde abu yashafi wannan mutuminne.

Wai yaushe masukayi irin wannan sabo haka idan be manta ba shekaru biyar da suka wuce suka haɗu da shi da matarsa dakuma ƴarsa a airport sunje taro ƴartasu wato basma shima kuma Ammin sa da daddyn sai faisal khalid da autar Ammi wato saima dasukaje tarɓansa nan suka haɗu sanadiyan musayan jaka dasukai da  ita basman.

AISHA

yanda take tasakin murmushi ita kaɗai abun ma gwanin ban dariya Anty malika ce tafito daga cikin falo zata fita motartake kiciniyar budewa ganinta yasata dan tsayuwa tana tsura mata ido Anty hajia ma data biyo bayan malikan dan tare zasu fita kallon ta ta tsayayi ganin ma kaman bata gansu ba,zunguranta tayi tace"wai ke lafiyanki kuwa sai sakin murmushi kike ke ɗaya?

"Anty hajia inaga kode sun daidaita da broo ne irin wannan murmushi haka Anty malikace ta kare da faɗin haka bayan Anty hajiya tayi tambayarta.

Dan sosa kanta tayi tana tura baki tace"Anty hajia kinga Anty malika ko?"eh to nima de tambayan da nakeson yi miki kenan,lumshe idonta tayi tasake budewa tace Anty hajiya zanbiku inda zakuje"a'a ba inda zaki bimu sai kintambaya an barki tukunna.

"Wazan tamvaya kuma bayan gaki tafaɗa cikin rashin fahinta"Ahmad zaki tambaya tunda yanada igiyar sa uku a kanki Anty malika ta bata amsa da hakan.

Cinno bakinta tasakeyi tace inde sai na tambayi wancan ɗan uwan naki zanfita to na hakura mema akai akai AUREN WUCIN gadi da zabashi wannan mahimmanci ai idan kinji ana neman izini sai auren so da kauna ba auren haɗi haɗinma irin namu da maishi be wani daukeshi da mahimmanci ba.

Sai kuma ta juya wajen Anty hajiya tace"wato yau na fusata wani fusataccene tsuntsune shisa nake jina cikin wani irin farin ciki tawani ware hannunta tana tsalle sake baki sukai su dukkansu biyu suna kallonta garin tsala tsalanta rigan data ɗaura acikinta  yasince ya fadi ƙasa duƙawa tayi ta dauka tana warewa sai kuma komai ta tuna saita kwashe da dariya tana cewa wannan rigar aradu ƙwalelenki.......




ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now