44

145 14 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 44

  Sunjima Anty hajiya na bata labarin ban dariya harta sake sosai kaso hamsin cikin ɗari na damuwarta sai taji ya gushe,suna cikin hira sai ga sallamar Ammi daga falo tare suka miƙe suka isa gareta har kasa Aisha ta tsuguna ta gaidata amsamata tayi fuska sake tana kamota ta miƙarta ta zaunar da ita kusa gareta tana kara godewa Allah daya sa Aisha ta zama surukuwarta sannan tana addu'an Allah yasasanta tsakanin su yakuma dasa musu soyayyar junan su a zukatan su.

"Aisha Ammi takira sunanta cikin sanyi murya.

Na'am Ammi ta ansa mata kanta duƙe.

"Nazo da kaina ne domin baki hakuri bisa kuskure da muka aikata miki,karki ga kaman dan rashin gata mukai miki haka a'a munyi hakanne saboda munyaba da tarbiyyarki kamalarki sannan uwa uba nasabanki da yarda kuma da amincewar mahaifiyarki mukai wannan abun asalima itace ta jagorance mu wajen wani Baban Abba shiya wakilci dauri auranki.

Idan kinga munshiga rayuwarki ne kiyi hakuri Allah yana gani kuma shiya dasa mana kaunarki harmukai wannan tunani,idan ma so kike na duƙa a gabanki nabaki hakuri wallahi Aisha ashirye nake dayin hakan.

Nasan mun miki lefi dan Allah ɗiyata kidubi girman Allah kiyafe mana...Aisha jitayi duk jikinta yayi sanyi yanda Ammi take mata magiya jitayi duka ta muzanta mace kaman Ammi da girmanta da komai amma tasauke kai take bata hakuri ba tayi la'akari da ƙanƙantarta shekarunta ba,sunyi kalan tausayi kaman zasu saki kuka daga Ammin har Anty hajiya kallon fusko kinsu tayi ɗaya bayan daya sai ta sauke kanta tace"Ammi karkiji komai matsayinki na uwa dan kinyanke hukuncin kan ɗiyarki ai ba lefi bane kawai de naji babu daɗine da yaxo yake cewa dani sai kuma tayi shiru saboda nauyin Ammi da takeji yanzu.

Shafamata kai tasoma yi tana mai cewa"Allah yayi miki albarka ɗiyata ubangiji Allah ya bayyanar mana da Nafi aduk inda take yakare mana ita da lafiyarta"amin Anty hajia ta amsa daga nan suka shiga hiran su nan takejin satin sama auren sa da basma wani irin abu taji yadaki ƙirjinta zuciyata ta gwaɓeta da ina ruwanki da auren sa da har zakiji wani haushi keda aurenki dashi na wucin gadine to haushin me zakiji,miƙewa tayi tanufi ɗaki duka bin bayanta sukai da kallo tare suka sauke ajiyar zuciya kowanne cikinsu da abunda yake aiyanawa aransa.

Ahmad koda ya tafi company kasa sukuni yayi lokaci zuwa lokaci sai yaja tsuka da kallon tangamemen agogo dake maƙale a office ɗin nasa,a wannan halin khalid yashigo yasame shi yayi mamakin ganin sa a wannan lokacin dan besaba shiga company a wannan time ɗin ba shisa ko knockin beyi ba yashiga turus ya tsaya yana kare masa kallo"man lafiya na ganka a wannan yanayin?

"Me kagani?

Ganin raina masa hankali yakeson yi kawai sai yace"dama suhail ne yakira yace an dage wannan taron sai next 2weeks kai kawai yajinjina masa,sai kuma ya daura da cewa waƴancan kayan na suleiman Ghana gobene fa alkawarin mu kuma naga har yanzu Aisha bata shigo ba.

"So
"Nagade ita keda alhakin wann...katseshi yayi ta hanyan cewa"daga yanzu na canza tsarin tafiyan ba ita ba yin wasu aiyuka masu kaman daa,kallon kataɓune khalid yamasa kaman zeyi magana sai kuma yayi shiru yana dage kafaɗa yayi ficewar sa yana amsa kiran da suhail yamasa ya tambaya mai yasami mutuniyartasa baya samunta ta waya.

"Ai yau kwata kwata bata shigo ba nima tunani da nake yanzu ko llafiya amma kwantar da hankalinka zan bincika inji,a ɗaya ɓangaren suhail kaman zeyi kuka yake cewa khalid din dan Allah ina jiranka idan da wani abu ka taɓoni jinake kaman nayi tsuntsu na ganni a garin naku.

Dariyama abun yabama khalid dan haka saida yadara kana yace"kasan mu ƴan africa musamman nageri ƴan matan mu daban suke da sauran.
Shima suhail din dariya yayi yana cewa"gashi nagani karamar yarinya duk ta dagulamun lissafi nakasa samun sukuni idan banji muryarta ko munyi video call ba jinake manan rayuwata ce takusa barin gangan jikina"kai mr suhail dama ance ku labarawa kunfi kowa iya soyayya da iya tattalin mace.

wannan kan sosai yasaka suhail darawa yace"kai khalid ai bakasan matsalanku ku ƴan africa baku iya sauke kai ga mace bane alhali ko ta fannin halitta halittarmu ba ɗaya da nasu bane sannan kaga mu yanzu anan koda mune da gaskiya sanda mace ta hau 90 tayita faɗa tayi kuka to karshe zamu zauna mu sauke kanmu mubata hakuri da sayo mata ɗan fure ko wata ƴar sarƙa komade mainene abunda ze faranta mata raide hakade tare da kalamomi masu sanyaya zuciya da nuna mata zallah soyayya amma ku maxan africa baƙwayi masamman ma ku hausawa.

*********
Aisha kuwa koda tashiga ɗaki
duk yanda taso kawar da abun aranta kasawa tayi karshema fashewa tayi da kuka mai tsanani ita fa a ganinta duka rashin gatane yajamata haka,tana haka su khadija suka dawo daga makaranta suka isketa hankalin yaran yayi ƙololowar tashi da ganin halin da yayar tasu ke ciki,cikin kuka khadija ta rungumeta tana cewa"Anti aisha me akai miki daya yake saki kuka?

Gaskiya idan har zamanmu anan ɗin be kwanta miki a rai ba mu masu binki koda dokar daji murayu dake matukar hakan zesaki farin ciki.

Kallon fuskar ƙanwartata tayi sannan ta miƙawa mubaraq hannu yaro dama kaman jira yake yazo da dan gudun sa ya faɗa cinyarta yana sauke ajiyar zuciya,shirune yaɗan ɗauke su na ɗan wani lokaci kana Aisha ta dubi khadija tace"khadi nasan kina da hankali dakuma lura duk da ƙarancin shekarunki bani da kowa da zan faɗawa damuwa naji sassauci acikin zuciyata sai ku,nasan wani abun idan kin fahinta wanin ba lalle ki fahinta ba,khadi aure aka ɗaura mun kuma da alama ya kwan biyu bansani ba.

Wani irin zabura khadija tayi ta waro idanunta waje tana kallon yayar tata baki na rawa ta maimaita kalmar"Aure
"Eh aure kuma nan takwashe yanda sukai dasu Ammi ta faɗamata.

Saida ta gama sauraronta sannan tace"anty aisha dan Allah ki kwantar da hankalin ki mubi komai a hankali ganinki cikin damu yana taɓamun zuciya da hanani sukuni.

Nan tashiga kwantarwa da Antyn tata hankali da kalamai masu dadi nan shima mubaraq yashiga bata labarin makarantar su da yanda uncle malik yake sayamai kayan dadi yace"Anty harma wajen wasan yara kaini yake muhau lilo tare ya goyani Anty har wasan doki da ƴan ɓoye ɓoye munayi dashi jin yanda kannen nata ke ta fadin alherai ga ahalin gidan yasa xuciyarta dan sassautawa amma fa batajin zata sassautashi kan uban gayya tunda ya furta da bakinsa auren wucin gadi to lalle sai ya furta yajanye kalaman sa sai yazo ya duka gabanta dan neman yardan ta da soyayyarta.

Ya faisal kansa duk ya dauki ɗumi aiki yake tuƙuru amma bawani  haske cikin lamarin nasa wacce yake tsammanin wani haske ta wajenta itama tamasa mummunan fassara zaune yake yana rubutu a saman wani dan takarda inda ya rubuta LION da manyan harufa yakasa gane kan abun yaja tsuka yafi akirga Aisha ce ta doso wajen ganin takarda iska ya dauka tayi sauri kamowa tana ajiye masa gaban sa dacewa"Ya faisal da alama hutu kake bukata dubi yanda iska yayi filla filla da takardun dake gabanka amma kagaza yin komai ta ajiye masa saman dan karamin tablr dake gabansa tayi shigewar ta cikin garden.

Bude idon sa dake lumshe yayi ya sauke su saman table din da nufin tattara komatsan sa yashiga ciki ya huta kaman yanda tace din,kwayan idon sa yasauka saman paper data ajiye masa LION taya juya upside down yabashi abunda yake nema tsawon kwanaki wato NOI7 besan sanda wani irin ƙayataccen murmushi ya suɓuce masa saman fuskar sa ba....tare da furta kalmar Alhamdullahi acikin ransa.

Alkalami 🖊️yafi
Takobi⚔️

ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now